Chapter 15
Chapter 15
yanzu na hakura ba zan cuce ka ba.” Na cika da mamaki na ce mata, “yaushe kika yi nufin cutar da ni alhali kuwa ga shi muna soyayya?” Ta ce, “ba za ka gane komai ba saboda yarintarka da karancin tunaninka, ba ka san kaidi da makircin mata ba. Da a ce tana nan a raye na tabbata da za ta kare ka daga fadawa hadari bisa dalilin makircin mata. Yanzu na hore ka da kada ka sake kula wata mace, kada ka yi mata magana ballantana ka sadu da ita ko aurenta. Yarinya ce ko tsohuwa. Ka ji na fada maka, ka kiyayi kan ka, ka kiyayi rayuwarka domin ka zama ba ka da mai kiyaye ka. Wadda ke fassara maka isharun nan ta riga ta mutu. Ni ina kaunar ka, bana son na ga ka fada wata masifa da ba za ka iya fita ba. Saurayi ya ce da Tajul Muluk matar nan ta ci gaba da nuna mini girman hasarar da ya same ni saboda mutuwar ‘yar uwar nan tawa. Bayan ta k’are yi mini bayani sai ta tuma tana kururuwa, da birgima a k’asa tana marin kanta tana cewa, “wallahi ban san da zaman wannan yarinya ba, da na ba da tawa gudummawa. Allah ya ji k’anta, ta kasance mai girman ladabi da biyayya, kai wannan yarinya da zurfin ciki take, ta rufe sirrin cutarta, amma ba ta ci riba ba, da ta cimma burinta, da ba ka shiga wannan hanya ba.” Da ta k’are kukanta sai ta ce da ni tana son abu guda a wurina, watau tana son in kai ta wurin da kabarin ‘yar uwar nan tawa yake ta yi ziyara, na amsa mata cewan kashegari zan kai ta wurin. Bayan mun k’are hayaniyarmu muka kwanta barci, amma bayan ko wace sa'a matar nan takan juya ta numfasa ta ce, "da ka gaya mini tun da sauran wuri da ba haka ba." Maganar ‘yar uwar nan tawa a bakin wannan mata ya dame ni, na rasa yadda zan yi in fitar da zuciyarta ga wannan zance na kasa, sai na tambaye ta cewar ta gaya mini ma'anar kalmomin nan guda biyu da aka bar wasiyyarsu a wurin uwata, amma sai ta kyale ni ba ta ko dube ni ba. Na yi ta tambayarta amma a banza ba ta gaya mini ba. Kashegari da muka farka daga barci sai na ga ta dauko wata jaka da dinari a ciki, ta ce na tashi na kai ta wurin da kabarin ‘yar uwata yake. Na tashi na shiga gaba, muna tafiya, tana ba da sadaka a kan hanya, har muka isa, koyaushe ta ba da sadaka, sai ta ce ta bayar saboda ‘yar uwar nan tawa. Yayin da muka isa na nuna mata kabarin sai na ga ta yanke jiki ta fadi, tana mirgina, tana kururuwa, sa'annan na ga ta fito da mabugi da karfe ta zauna kusa da kabarin ta rubuta wad’annan baitoci: Na wuce kaburbura da dama cikin tausayi, Amma wannan ya fi matuk’ar girgiza ni Na tambayi mazaunin cikinsa da ladabi, Aka ce min ta mutu da ciwon son zamani Na roki Allah na cika da so cikin raina Aljannar Firdausi ki zauna babu gunaguni Su kuwa masu cutar da ma’abota son su, Za su ga k’ask’anci komai tsawon zamani Ina ma wata ran kabari zan zo ziyara, Na yi maka kuka na zubar da hawayen jini Bayan ta k’are rubuta wannan baiti kan kabarin nan sai ta sake fashewa da kuka, ta yi salati, sa'annan ta tashi muka koma cikin gonar da muke zaune, muka zauna muna hira sai na ga ta yi shiru. Ta d’aga kanta sama ta dube ni ta ce, "na had’a ka da Allah wanda ya halicce mu, kada ka yarda ka dauke mini k’afa ko da da rana d’aya." Na amsa mata cewa, “na yarda da haka.” muka ci gaba da zamanmu tare da ita, koyaushe tana nuna mini karimci da kyautatawa, wani lokacin takan tab’o ni da maganar kalmomin nan da ‘yar uwata ta bar wasiyyarsu, idan ta tambaye ni sai na yi murmushi sa'annan in biya mata su in tambaye ta ma'anarsu, amma sai ta k’i fad’a mini. Haka muka zauna muna ci tare, muna sha tare, muna kuma holewarmu kamar yadda muke so har zuwa wani lokaci mai tsawo har bak’in cikin mutuwar ‘yar uwata ya rabu da ni, hankalina ya zauna, na murje har na yi k’iba na yi kaurin wuya, na yi taib’a abin gwanin ban sha'awa, da ban al'ajibi, kullum ina sa tufafi mai kyau na yi shigar da nake so. Rannan sai na shiga d’akin wanka na yi wanka na komo cikind’akina na zauna a nan na sami wata moda an cika ta da wata zuma mai kauri da na shak’i k’anshinta gwanin dad’i. Na yi k’arfin hali na dauki zumar nan na sha, sai maye ya kama ni, lokacin sallar lisha ya yi na tashi zan yi salla na ji ba zan iya ba sai na koma na kwanta, ina nan har lokacin da zan tafi wurin matar nan ya yi, na tashi zan tafi wurinta ina had’a hanya. Ban san yadda aka yi ba na gan ni a cikin wani lungu da ban taba shigarsa ba. Ina tafiya cikin lungun nan na hadu da wata tsohuwa tana tafiya, tana rik’e da wata fitila da kuma takarda a hannunta, an nad’e ta. Saurayi Azizu ya ce da Tajul Muluk, lokacin da na ke tafiya na hadu da tsohuwar nan sai na gan ta tana kuka idanunta sun yi sharaf da hawaye, tana cewa, kaiconka samari shin ba ka ganin jama’a na maka maraba? Ni na dade a wurinta, ina kallon su, ina kuma sauraren muryarta mai sanyi mai dadi, ina ma a ce zan iya cire wadannan kayan wuyan in ba ka kyauta, ai kuwa da zuciya ta karaya a cikin sa'a guda." Da ta gan ni sai ta matso kusa da ni ta ce in karanta mata takardar nan da ke hannunta. Ta miko mini takardar ta kawo fitila kusa da ni, na bude takarda sai na ga ba a rubuta kome ba a ciki sai gaisuwa da tambayar lafiyar masoyi, na mika mata. Sa'annan tsofuwar nan ta yi mini bishara da cewan bakin cikina zai yaye kamar yadda nata ya gushe. Yayin da ta juya ta tafi sai na tsuguna zan yi fitsari. sai ga tsohuwar nan ta dawo wurina cikin hanzari, ta kama hannuna ta ce in biyo ta mu je wani katon gida da ke kusa da wurin. Na nuna mata ba ni da bukatar zuwa gidan, amma sai ta dage har na yarda na bi ta, muka je na tsaya bakin kofar gidan, ta ce mini in shiga na ki, na tambaye ta inda ta sami wannan takarda, ta ce mini wai wani d’anta ne da ya yi tafiya kamar shekara goma bai dawo gida ba, shi ne ya aiko mata da takardar, ta ce mini wai yana da wata ‘yar uwa a cikin wannan gidan, wadda tun lokacin da ya tafi take kuka dare da rana. Kuma ta dage a kan cewar sai an kawo mata wanda ya karanta wannan takarda ta gan shi da idonta sannan za ta yarda da abin da
Table of Contents