Chapter 16
Chapter 16
ke ciki. Tsohuwa ta shiga rarrashina tana ba ni magana, dad’in baki, har dai na saki jiki da ita, na bi ta, muka shiga cikin gidan. Na tsaya a bakin k’ofa, sai ta ce, "haba dana, shin ba ka ji Manzon Allah (mai tsira da aminci) ya fad’i cewa, "wanda ya gusar wa Musulmi da bakin cikinsa daya. Allah zai gusar masa da nasa sau saba'in da biyu, a ranar Alkiyama ba? Ko kuwa kana gudun ganin wannan yarinya ce, idan haka ne na yi maka alkawarin zan saka labule a tsakaninku, har yadda ba za ku had’a ido da juna ba. Ka sani dai kai dana ne, ba ni kuma da nufin kullin sharri zuwa gare ka kada ka yarda ka gwale ni a cikin wannan al'amari." Tsohuwa ta hura min wuta kan sai na shiga gidan nan, daga bisani na ce mata ta shiga gaba na bi ta. Muka kama hanya muka shiga tana gaba ina biye har muka isa bakin wata k’ofa, wadda aka yi wa ado mai ban sha'awar gaske. Kyauren k’ofar an yi shi da k’arfen tagulla ja ne, an daje shi da jauhari. Da muka isa wannan wurin, sai na tsaya a nan, na ce da ita ba zan shige nan ba. Bayan ta ba ni magana na ki ji, sai na ji ta fasa kururuwa, tana kiran wadansu sunaye da ban tab’a jin irin su ba a cikin wani harshe da ban tab’a jin sa ba. Jim kadan sai ga wata kyakkyawar yarinya ta lek’o tana murmushi. Da zuwan ta sai na ji ta yi mini magana a cikin murya mai dad’in gaske, maganar kuma mai cike da fasaha da ma'ana, sa'annan na ji ta ce, "Umma, wannan shi ne wanda ya zo karanta mini takardar dan uwana ? "Tsohuwa ta ce da ita, "na’am shi ne, amma na sha fama a kan sa kafin mu zo da shi." Yarinya ta fito da takarda ta mik’o mini, na mik’a hannuna zan karb’a sai ta rik’e ni, ta fizgo ni, har kaina ya shige cikin labulen da ke tsakanimmu, kafin in ankara sai na ji tsohuwa ta cuso kanta tana tura ni ciki, na turje, sai suka yi ta turi kafin lokaci kad’an sai ga ni na fada tsakiyar gida. Ashe wannan k’yauren da na rik’e yana tafiya da ni ne ni ban sani ba. Yarinya ta ja ni ta kai cikin wani makeken daki ta zaunar da ni, tsohuwa kuma ta shigo ta kama k’ofar dakinta saurayi Azizu ya cigaba da ba wa Tajul Muluk labarinsa, na waiwaya na ga kaina a cikin gida, tsohuwa ta yi hanzari da gaggawa kamar walkiya, ba ta yi wani abu ba face ta kulle k’ofar. Yarinya ta gan ni daga mashigar zaure ta taso zuwa gare ni ta rungume ni a kirjinta sannan ta matsa cikina da hannunta tana bugawa da kyau har sai da na kusa fita hayyacina. Ta rike ni da hannunta ba ni da ikon kubcewa, muka cigaba da tafiya tsohuwa tana gabanmu rike da sham’a har muka je zaure na bakwai sannan muka isa wani fili mai rairayi da yawa, wanda ya isa masu sukuwar dawaki su yi tsere a cikinsa. Incomplete This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels
Table of Contents