Chapter 14
Chapter 14
dai mutuwa ce magani.” Da ta ji abin da baitin wak’ar ya k’unsa sai ta fad’i kan gado a some, jim kadan sai ta farfad’o ta sake ba ni wani baiti guda, ta ce, Mun ji mun yarda, mutuwar ce za mu yi, Mun nemi aminci da saduwa da wanda muke so. Bayan da dare ya yi sai na tashi na kamo hanyar gona kamar yadda na saba, na sami yarinya tana zaune tana jira na a cikin gonar, muka zauna muka ci abinci, muka sha abin sha, sa'annan muka shiga yin masha'a har barci ya kwashe mu, ba mu farka ba sai bayan da gari ya waye tangaram. Na taso zan komo gida sai na rera mata baitin wak’ar da ‘yar uwan nan tawa ta ba ni, yayin da ita kuma ta ji wannan baitin wak’ar sai ta fashe da kuka. Ta yi kururuwa, ta kid’ima, ta firgita, ta cefirgita, ta ce wallahi mai wannan wak’a ta riga mutu, ta sake fashewa da kuka ta ce, "masoyina, yaya kusancinka da wannan mai wak’ar yake ?" Na ce mata, ‘yar baffana ce. Ta ce, “k’arya kake, wallahi da ‘yar baffanka ce da kai ma babu shakka ka so ta kamar yadda ita ma take son ka, kai ne ka kashe ta, Allah kuwa ya kashe ka kamar yadda ka kashe ta. Wallahi da ka gaya mini kana da ‘yar uwa wadda ke mutuwar son ka, da ban yarda ka yi kusa da ni ba! Na ce mata ai ‘yar uwata, ce kuma ita ce ke fassara mini dukkan isharorin da kike yi mini, da yadda zan yi da ke duka, ba domin ita ba kuwa, da ban sami saduwa da ke ba. Ita ce ta shirya mini yadda zan yi na sadu da ke, sa'annan ta ce da ni, ‘yar uwan nan taka kuwa har ta riga ta san ni ? Na ce mata, "na’am, ta sanki mana. Bayan ta numfasa sai ta ce, "Allah ya tab’ar da k’uruciyarka kamar yadda ka tab’ar da tata k’urciyar!" Bayan ta yi mini wannan mummunar addu'a, sai ta buga min tsawa ta ce da ni, “maza je ka ka kula da ita!”Na kama hanya ina tafiya hankalina ba ya tare da ni, har na kai gida. Yayin da na isa gida sai na sami gida ya cika da kururuwa da hargowa. Na shiga na tambayi abin da ya faru a gidan aka ce mini Azizatu ce ta mutu, an tsinci gawar ta a bayan kyaure. Na fad’a cikin gida a firgice, uwata ta dube ni ta ce, "yau ka cimma burinka, alhakin wannan yarinya duk ya hau kanka, Allah ba zai yafe maka alhakin wannan yarinya ba, sai ya saka mata a kan ka.”Allah ba zai yafe maka alhakin wannan yarinya ba, sai ya saka mata a kanka.” Ubana ya zo da sauran jama’a aka had’a ta, muka dauki gawar yarinya, muka je muka rufe. Sa'annan muka dawo gida muna karb’ar gaisuwa ga mutanen da suka zo yi mana ta'aziyya har kwana uku. Bayan nan sai uwata ta zo ta ce min, “fada min abin da ka aikata mata ya sa ta ciwon zuciya. Ka sani ya d’ana na tambaye ta ya fi a k’irga amma ta k’i fada min dalilin ciwonta. Yanzu dai Allah na kallon ka kuma ya san abin da ka aikata mata ta mutu.” Na ce wa uwata, “Ni dai ban mata komai ba.” Ta girgiza kai cikin takaici ta ce, “Allah zai mata sakayya a kanka, kodayake ba ta fada min komai ba, ta kiyaye sirrinta a wajenta har ta mutu, amma na tabbata ciwon son ka ne ya kashe ta. A lokacin da mutuwar ta karato mata ina wurinta ta bude idanunta ta ce min, “ya matar kawuna, ina rokon Allah kada ya kama d’an uwana da laifi a kaina saboda abin da ya yi min. Yanzu Allah zai tafiyar da ni daga wannan duniyar wadda ke cike da kunci zuwa inda zan huta wa raina.” Na ce mata, “ya ‘yata, Allah ya kiyaye ki kuma ya kiyaye kuruciyarki.” Na cigaba da tambayar ta dalilin rashin lafiyarta ta ki fada min sai murmushin karfin hali kurum take yi. Ta ce min, ‘ki fada wa d’anki cewar ya kiyaye wad’annan kalmomi cewa ‘cika alk’awari na da dad’i, warwarewa kuwa mugun abu ne.’ wannan shi ne zai zamana cewa ina kula da shi. Kuma zai nuna na damu da shi a lokacin da nake raye da kuma bayan mutuwa ta.” Sannan kuma ta ba ni wasu abubuwa ta ce kada na ba ka sai lokacin ka zo min kana kuka saboda bak’in cikin mutuwarta. Abin da ta ba ni yana nan hannuna ba zan ba ka yanzu ba sai na lura ka shiga taitayinka sannan na ba ka.” Na ce wa uwata, “ba ni abin na gani.” Ta yi mirsisi ta hana ni. Na zauna ina mai cike da bak’in ciki saboda mutuwar ‘yar uwata, kodayake ban damu sosai ba duk tunanina ya tafi wurin abar k’aunata wadda dare da rana na kasa samun sukuni saboda abin da nake samu a wurinta. Na zauna a k’agauce ina jiran dare ya yi, da dare ya yin na tafi gonar nan da muke had’uwa, yayin da ta gan ni ta zabura ta taso ta tarye ni, ta kama ni ta rungume, sa'an nan ta zaunar da ni ta tambaye ni labarin ‘yar uwata na ce mata ai ta mutu. Hankalinta ya tashi, ranta ya b’aci matuk’a, sai ta ce mu je mu yi mata addu'a, muka je wani wuri muka zauna muka yi zikiri da addu'a sa'annan muka shiga sha'animmu na holewa da nishadinmu. Bayan nan ta tambaye ni yaushe ne ta rasu? Na ce mata, “jiya kwana hud’u yau ne na biyar.” Ana karanta wannan labarai ne zaurukanmu na sirri wanda iya masu rijista kadaike samun daman shiga Domin yin rijista kuna iya tura kudinku 200 kacal ta sakon waya kota hanyar transfer'dauke da sunaka na Facebook izuwa 0803276754708 HIKAYAR AZIZA DA AZIZU MAISO DA WANDA AKESO Da ta ji haka sai ta fashe da kuka ta yi kururuwa ta ce, “ba na fad’a maka kai ka halaka ta ba? Da ka bari na san da ita kafin ta mutu da babu shakka na sakanta mata abin da ta aikata mini na alheri. Ta kyautata mini ta sada ni da kai, domin na tabbata ba domin ita ba da ba za mu taba haduwa ba balle mu biya buk’atar mu. Ni kam ina jiye maka aukuwar wani mugun abu gare ka, sakamakon abin da ka aikata mata.” Na ce “ai ta yafe min kafin ta mutu.” Na habarta mata abin da uwata ta fada min. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Allah ya jikanta, wadanne kalmomi ‘yar uwarka ta bayar da sallahun a fad’a maka?” Na amsa na ce, “kafin rasuwarta ta ce a fada min cewa, ‘cika alk’awari na da dad’i, warwarewa kuwa mugun abu ne’. Yayin da matar nan ta ji haka sai ta yi kururuwa, ta yi kuka ta ce, “Allah ya gafarta mata. Wannan kalmomi na nufin ta bar min kai. Kuma ta nemi na kyale ka daga sharrin abin da na yi nufin yi maka. A gaskiya da na yi nufin cutar da kai amma
Table of Contents