Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ga alamar kina da niyyar fita ba?" Ta sadda kai cikin kankanuwar murya ta ce "Ina tunanin yadda zan yi aikin da ka bayar ne". Ya yi murmushi ya ce "Aiki ne kuwa mai sauki, amma ga wanda ya gane tambayar. Wacce tambaya kika dauka a ciki?" Ta sunkuya tana kara nazarinsu, ta ce "Ina ganin ta daya za ta fi mun saukin amsawa, tunda daga karkara na ke, 'Yadda ake bikin sallah a karkararmu". Ya yi murmushi, ya ce "Ni kuwa sai na ga tambaya ta biyu zata fi dacewa da ke 'Ranata ta farko a sakandire', za ki kawo 'points' sosai wanda zai taimaka ki yi 'scoring' maki mai yawa. Kinga sauyin abubuwa da dama, a zuwanki babbar makaranta. Haka ne ko ba haka ne ba?" Ta yi murmushi, wanda ya lotsa kumatunta hagu da dama. Akwai wani asirtaccen kyau a tare da Mariama, wanda rashin gyara da rashin gogewa ya boye shi. Yarinya ce kamar diyar Larabawa, sai dai fatarta a dafe ta ke, kamar an shafa mata shuni, wanda kai tsaye ya banbantata da sauran yaran makarantar. Ta ce "Haka ne Uncle. Na gane cewa, ashe mu ba mutane ba ne, ababen kyama ne ga wasu jinsin al'ummah. Abin dariya ga wadanda Allah Ya yiwa falalar rayuwa. Ban san cewa ni 'yar talaka ba ce sai yanzu, tunda kuwa ban taba neman abin da zan ci na rasa ba, sai na dauka iyakarta ke nan. Ashe akwai masu shi fiye da ni, amma idan da ace ni ce a matsayin mai shi din, ba haka zan yi wa mara shi ba!". Mamakin kalaman karamar yarinya kamar wannan ya kama shi. Sai dai ya kula magana ta ke tun daga karkashin zuciyarta, ba wai tunaninta ba ne. Ya ce "Mariama!" Ta dago ta dube shi, amma ba ta amsa ba. Ya ce "Ina son ki sa wa ranki cewa, ba duka mutanen da kika tarar halinsu daya ne ba. Kowa da kika gani a duniya da irin halayyarsa. Wani yasan darajar kansa, yasan ta mutane, wani bai san darajar kansa ba, bai san ta mutane ba. Wani yasan darajar kansa bai san ta mutane ba.To wannan ba cikakken mutum ba ne, kuma shi ne wanda Allah Ubangiji Ya yi alkawarin dankafar da shi a duniya da lahira sabida girman kansa. Da zarar ka yi tunani ko ya ya cewa, kai wani ne, to kai ba kowa ba ne a wurin Ubangiji. Sabida haka a yadda kika dau kan naki a ba kowa ba, ci gaba da hakan. Amma kada ki yarda da cewa, sai wun fi ki ne. Ido biyu gare su, kunne biyu, kafafu biyu, hannaye biyu, ke ma su gare ki. To akan me za ki yi tunanin sun fi ki? Wanda ya fi ki kawai shi ne wanda ya fi ki tsoron Allah!”. Jikinta ya yi sanyi, ranta ya yi fari. Tana dubanshi da kyawawan idanunta, ta ce "Uncle kana nufin ni ba abun kyama ba ce?" Ya girgiza kai "Ko daya Maryama. Da za ki daure ki fidda su a gabanki ki yi karatu sosai ki dinga gyara kanki, sai kin fi su kyan gani. Ko a yanzu haka kin fi su, gyara suka fi ki. Ba kawa kika zo nema ba, ilimi kika zo nema, irin wanda suka zo nema. To akan me za ki damu da su? Ai abu daya za ki damu da shi, shi ne ki dage ki ga cewa ba su fi ki kokari ba". Ta yi murmushi ta ce "Uncle kana da kirki, sai na ke jinka kamar Yaya Habibu. Shi ma haka yake yi min irin maganganunka. Da zai zo ya ganni a makarantar nan, ban san irin farin cikin da zai yi ba". Ya ce "Yaya Habibu yana ina yanzun? Ni kuwa inje in gaya masa, ga ki a babbar makaranta". Ta washe baki ta ce "Ayyah, yana da nisa, yana karatu ne a kasar waje, amma komi nake yi sai in yi ta ganin kamar yana kallona, sabida shi ne ya dage, ya sani a makaranta". Ya ce "Ni kuwa gani na dage da yardar Allah sai kin yi karatun da Yaya Habibu zai dawo ya yi alfahari da ke, amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanki Maryama, wanda ba komi ba ne da ya wuce perserbearance (jajircewa) da ba da himma". Ta sake yin murmushi har kumatunta suka lotsa, ta ce "Na gode Uncle, kuma na yi maka alkawarin I'll persebere". Ya yi mata tafi guda daya ya ce "Good Maryama, ina neman alfarmar ki rike ni a matsayin Yaya Habibu",. Wani farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce "Kenan ka yarda na rinka kiranka da Uncle Habibu?" Murmushi ya yi, "A'ah, UNCLE JUNAIDU. Sunana Junaidu Galadanchi". Ta ce "Galadanchi?" Ya ce "Eh, kin santa ne?" Ta ce "A'a, ban taba ji ba ne. Garinku ne Galadanchi ko sunan Babanka ne?" Da alama Maryama matambayiya ce, kuma matambayi ba ya bata. Hazakar yaro na da alaka da yawan tambayarsa (curiosity). Ya ce "Galadanchi karamar unguwa ce a cikin birnin Kano. Sai dai tarihinta mai girma ne ga Kanawa. Duk wani Ba-Kano ya san Galadanchi, sannan mu 'ya'yan cikinta muna alfahari da ita da kasancewarmu 'ya'yanta. A Galadanchi ne aka fara samun Dr. a ilimi a jihar Kano. Haka idan kika bi tarihin manyan 'yan bokon Kano, da mayan malaman Jami’ar Bayero, wadanda suka fito da jihar Kano a tsakanin jihohi 'yan uwanta, to duk 'yan Galadanchi ne. sannan gasu da kyau, ga Alkur’ani da Tajwidi a cikin kansu". Ta ce "Ina fatan wata rana, in ziyarci Galadanchi". Murmushi ya yi "Insha Allahu za ki je Galadanci Maryama. Yanzu dai jeki ci abinci kamar sauran dalibai, idan kun fito 'pref' da yamma sai ki rubuta aikin gobe ki kawo mani". Ba musu ta mike ta nufi kofar fita. Bai daina kallonta ba har sai da ta kule ya daina ganinta. Shi kam bai san dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba. Haka dan zaman da suka yi a yanzu ya kara sanya mishi jin son taimakonta. Mairo da ta fito 'pref' ta yagi takarda kamar da wasa, ta soma rubuta 'essay' dinta mai taken 'My first day in secondary school'. Da jagwalgwalallen turancinta mara 'tenses' har haduwarta da Uncle a aji ta rubuta, inda ta ce, ba ta taba haduwa da mutum mai kirkinsa ba. A karshe ta ce “shin ko mutum nawa ne masu jin kai irin UNCLE JUNAIDU? Ta ce, Uncle Junaidu ya sa mata burin son zama malamar makaranta, wanda a da ba ra'ayinta ke nan ba. Ta sake bin jagwalgwalonta ta yi dan gyaran da zata iya, ta sanya a tsakiyar littattafanta. Washegari da karfin gwiwarta ta shiga aji, to amma Uncle bai tambayi 'assignment' din shi ba sai da period dinsa ta shiga. Yana bi daya bayan daya yana marking har ya zo kan na Maryama Bedi. A zahiri duka 'yan ajin sun fi ta iya Turanci, da kula da 'tenses' sabida su sun sami kyakkyawan tushe daga makarantu masu tsada. To amma idea da ke cikin rubutun Maryam fasaha ce tsagwaronta. Ta yi rubutunta kamar da gasket, tana magana kamar akan idonsa abin ya faru. Ya kirata yana nuna mata kura-kuranta, tare

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21