Chapter 5
Chapter 5
Mairo ne, shi yasa kowa ya sa mata ido. Amma insha Allah zai tsaya a kanta kamar yadda zai tsayawa 'yar cikinsa. Habibu ya yi godiya mai tarin yawa, ya nemi taimakonshi a kan ya taimaka ya bayar a dinka mata uniform, ya kirgo kudi ya ba shi har na littattafai da jakar makaranta. Sannan ya nufi islamiyyar yaran Gurin-Gawa, nan ma ya ba da sunanta. Sun tabbatar mishi ba komai ai irin su Mairon ake son a gyara. Hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya ga Mairo ranar litinin cikin kayan makaranta da jakarta a rataye ta tafi makaranta. Duk da Inna Hure na kumbure da shi, bai damu ba, tunda ya cika kudurin da ya dade yana damun zuciyarsa. Don haka koda ya je yi mata sallama zai komo Kano ta yi masa kunnen uwar shegu. Hure ta ga tijarar Malam Bedi irin wadda ba ta taba gani ba, ba ta kuma taba tsammanin ya iya ba, domin cewa ya yi idan Mairo ba zata je makaranta safe da yamma ba, to dukkaninsu su zo su fice masa a gida, su tafi duk duniyar da za su. Ba ta yi magana ba, amma a cikin ranta tasan wannan aikin Habibu ne, don yadda Malam din ke jin maganar Habibu ko ubansa sai haka. Abin da ta ce da shi kawai shi ne, "Saboda ka tabbata tsohon bakauye ka zauna dan ka ya fi karfin ka". Ya ce "Eh, koma mai zaki ce ki ce, amma Mairo da uwarta ba su zama min cikin gida muddin Mairo ba zata nemo ilimi ba. Me ye marabarta da dabba? Babu! Dabba ce aka sani da hawa bishiya da cin abincinta daga 'ya'yan itace, amma ba dan mutum ba". Habibu ya karkace kai ya yi ta ba Innarshi hakuri, ya ce "Inna ku yarda da ni, ba ni da nufin cutarku, sai dai ma na yi kokarin ganin duk abin da zai zamto cuta a gare ku na yake shi iya karfina. Ina nufin Maironki da alheri ne, bayan wannan ba wani abu. Ke da kanki wata rana za ki gane gata na yiwa rayuwar Maryam. Don Allah Inna ki sauko ki yafe min, kisa min albarka!". Zuciyarta ta yi sanyi lakwas, ta ce "Ai shi ke nan, nasan iyakar gaskiyar ke nan, laifina shi ne, ina son Mairo da yawa". Ya yi murmushi ya ce "Hakan ma ba laifi ba ne. Sai dai ki yi kokari kada son da kike mata ya sa ki kasa lankwasata. Ni ma ina son Mairon ki, son da bana yi wa kowa a duniya, amma idan har da gaske ina sonta, dole in inganta mata rayuwa da gishirin zamani, wanda idan babu shi miya duk dadinta lami ce. Wannan gishirin kuwa ba komi ba ne, face wannan ilimin dana ke so Mairo tayi. Shi ne zai haskaka mata ragowar bangarorin rayuwarta, tasan kanta, tasan inda ta sa gaba. Amma a yanzu wallahi Mairo ba ta da maraba da 'ya'yan birrai". Dariya Inna ta yi, ta ce "To Allah Ya taimake mu ta kimtsu". Ya ce, "Amin--amin, ko ke fa Innata? Ni ma karatun zan tafi..." Ya warware mata zare da abawa. Ga mamakinsa sai ya ga damuwa karara ta bayyana a kyakkyawar fuskarta, ita da a kullum, ta ke nuna ba ta damu da shi ba. Ya shiga kwantar mata da hankali cikin tausasan kalami, yana nuna mata shekaru shida kamar yau ne, idan da rai da lafiya. Da kyar ya samu ta sa ma abin albarka. Da wannan Habibu ya koma Kano ya ci gaba da shirye-shiryensa, da taimakon Baffansa. Cikin watanni uku kacal komi ya kammala, ya zo wa iyayenshi sallama. Ya ji dadin yadda ya ga Mairo cikin wankanta fes! Ba ta kuma yi masa wannan damuken oyoyon ba, an fara nutsuwa ke nan. Ya yi murmushi, ya ce, "Mairon Inna 'yan makaranta, ya ya dai?" Ta yi murmushi ta kawar da kai ba ta ce komi ba. Ya kamo hannayenta ya ce "Ba ki ga yadda kika soma sauyawa ba? Ina fatan duk runtsi za ki dage da zuwa makaranta? Zan tafi karatu Mairo, sai Allah Ya dawo da ni kimanin shekaru shidda a nan gaba. Ki kula da Innarki, ki dinga tayata aiki, ba wasan 'yar bebi ba kin ji Mairo nah?" Ta shiga damuwa sosai, nan da nan sai ga hawaye rau-rau a idanunta. Ta ce "Yanzu Yaya Habibu shekaru shidda zan yi ban ganka ba? Ina zaka je? Mai yasa ba zaka ci gaba da zama gidan Baba Abbas ba kana zuwa makarantar a can?" Ya ce "Kamar yau ne Mairo za ki ga na je na dawo, idan dai da rai da lafiya. Ki kula da kanki, ki dinga wanka kullum, ki dinga yanke akaifarki ta kafa da hannu duk sati. Ki kuma dinga wanke gashin kanki shi ma duk sati, kin ji?" Ta ce, "Na ji Yaya Habibu, Allah Ya dawo da kai lafiya". Ya ji dadi sosai, bai zaci Mairo tana da dan hankali ba ko yaya ne, har ta yi wa mutum addu'a. Ya sa hannu a aljihunsa ya ciro naira ashirin ya bata, ta yi ta murna ta je tana nunawa Innarta. Haka Habibu ya tafi cike da tunanin Mairo. Yana addu'a, Allah Ya sa ta dore da hakan. Watau turbar da ya sanyata. Washegari ya tashi zuwa Malaysia, inda ya samu gurbi a Unibersity of Malaya. Ya sha wuya matuka kamin ya samu ya mance da tunanin gida. Da taimakon abokinshi Amiru wanda shi ma dan Kano ne ya samu ya soma fuskantar karatun, amma babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai tuna Mairo ba. *** BAYAN TAFIYAR HABIBU M alam Bedi tsaye yake akan kafafunshi kan karatun Mairo don cika alkawarin da ya daukarwa Habibu. Da taimakon Allah Mairo ta saba da zuwa makaranta, kuma lokuttan makarantar sai ya shafe lokacin da ta ke samu ta hau bishiya ko ta yi wasan 'yar tsana. Idan ta dawo makaranta karfe daya na rana wanka zata yi ta ci abinci, ta yi sallah. Karfe biyu cikin ajinsu na islamiyya ya ke mata. Ba kuma za su taso ba sai goshin magriba, don haka ranakun alhamis da juma'a da yamma kadai ta ke samun hutu. A cikinsu kuma tana tare da Innarta suna ayyukan gida wadanda ta alkawarta wa Yaya Habibu taimakawa Innar. Rannan Mairo na surfen masara Inna Hure tana bakacewa, Mairo ta aje tabaryar ta ce "Oh Inna, Yaya Habibu yau watanninsa bakwai ke nan, yana can a cikin Turawa". Inna ta ce "Wa ya ce miki a Turai yake? Kasar Larabawa ne". Mairo ta yi murmushi, ta ce "A'ah Inna, rannan na tambayi malaminmu na makarantar book, a ina Malaysia ta ke? Ya ce min Asia ne, can wajejen India da Pakistan". Inna ta kama baki ta ce "Ke Mairo, yaushe kika iya Turanci haka?" Mairo ta ce "Ba Turanci na yi miki ba Inna, sunan kasashe na fada miki". Wani dadi ya kama Inna Hure, ba tasan sanda ta ce "Kai Allah Ka sakawa Habibu da alheri” MARYAM BEDI, ta ci gaba da karatunta cike da himma da kwazo. Takan sanya wa ranta cewa, kawai Habibu na kallonta, yana jin dadin kwazonta. Yana kara mata karfin gwiwa. Ba
Table of Contents