Chapter 13
Chapter 13
a duniya ba ne suka janyo masa wannan tsufan ba, a'a, wahalar rayuwa ce kawai ta noma, girbi, da sussuka irin ta kowanne manomin kauye. Tausayin Mairo ya kamata, ta tabbata ita 'yar talaka ce futuk, amma she is contented with what she habe (a gamshe ta ke da abin da ta ke da shi, ba ta taba kwadayin abin hannun wani ba). Mairo ba ta taba tambayar Nabilah ita 'yar waye ko daga ina ta fito ba. Wannan ya sa Nabilah tambayar kanta, shin Maryam wace iri ce? A zahiri miskila ce, abin da tasa a gabanta shi ne kawai ya dame ta. Ta mike ta tadda su tana gayas da Malam Bedi cikin tsananin girmamawa. Mairo ta ce "Baba Nabilah sunanta, ajinmu daya, dakinmu daya. Da har da Kausar amma ita ta rasu". Fuskarshi ta nuna bai ji dadi ba, ya ce, "Sannunki Nabilah, Allah Ya jikan Kausar". Idanunta ya ciko da hawaye, ta juya tana sharewa ta ce, "Amin". Babu irin neman da ba ta yi wa Uncle ba, don su gaisa da Babanta, amma ba ta ganshi ba. A haka cikin rashin jin dadi ta yi sallama da Nabila rike da 'yar jakar kayanta ta buhu (Ghana Must Go) suka fita. Sun sha wuya matuka irin ta motocin haya kamin Allah Ya kawo su gida. Ganin irin wuyar da Babanta ya sha ya sa ta alkawarta wa ranta daga wannan hutun zata hutar da shi kai ta makaranta da dawo da ita, tunda ta gane hanya zata dinga tafiya da kanta. Tunda yaro ya shigo da jakar Mairo Hure ta biyo bayansa da saurinta. A soro suka yi kacibus, da Mairon nata. Suka rungume juna kamin Hure ta soma hawaye ta ce "Ashe wannan ranar zata zo Mairo, ranar da zan kara ganinki?" Mairo kuwa baki ya ki rufuwa a haka suka karasa cikin gidan kamar wadanda suka shekara ba su ga juna ba. Inda duk Inna ta mika hannu sai ta zarowa Mairo abin sawa a baka, ta ci ta yi nak! Ta ci girkin Innarta da ta yi kewa, ba kadan ba. Duk da cewa abin da ta ke ci a makaranta ya fi na gidansu amfani a jikin dan Adam. Hure ta kasa boye mamakinta, ta ce "Shin mai kike ci a makarantar nan ne Mairo? Kinga kuwa yadda kika zama buleliya, kika yi fari sai sheki kike?" Mairo ta sa dariya, ta ce, "Ba abin da bana ci Inna. Tun daga kan kwai, dankali, agada, doya, madara, nama da kifi ba abin da ba a bamu. Har 'ya'yan itace (fruits) ba dole in zama buleliya ba?" A ranar dai Mairo da iyayenta kwanan zaune suka yi, tana ba su labarin rayuwarta a makaranta. Sai dai fa duk rabin hirarta, "Uncle Junaidu" wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wurin sama mata farin ciki da walwala a cikin dalibai 'yan uwanta. Malam Bedi ya ce, "To Allah Ya saka mishi da alkhairi". Sai dai a cikin labarinta ba ta kawo labarin saran sa macijiya ta yi mata ba, don ta tabbata idan suka ji, kidimewa za su yi su ce ba zata koma ba. Hutun Mairo gwanin ban sha'awa a gidansu, gabadaya yanayin rayuwarta ya canza, ba ta barin Innarta da aiki ko ya ya, sai ta karba ta yi. Haka ta ke bin babanta gona tana taya shi shuka da ban ruwa. Abokinta Rabe da ya ji ta zo hutu daga makarantar kwanan da aka kai ta, sai ya aiko yaro rannan da yamma wai Mairo ta zo su je su hau tsamiya. Malam na jin sanda ta maida dan aiken ya tambayo mata Rabe, shin yanzu ta yi masa kama da 'ya'yan birrai ne da zai ce ta zo ta hau bishiya? Sai ya yi murmushi yana kara shi wa Habibu albarka a zuciyarsa. Rannan sun dawo gona ke nan ita da Babanta, ta zuba ruwa a buta tana alwala a gindin rijiya sai ta ji rurin mota. Kamin ta kare alwallar sai jin sallamar Nabilah ta yi a tsakar gidansu. Da ta yi wurgi da butar cikin rijiya ta kwaso da gudu ta cacume Nabilah suna ta tsallen murna. Inna ta fito da sabuwar tabarma ta shimfida mata a shararriyar rumfar hutawar su tana, "Lale da Nabilah, muna murna da zuwan Nabilah". Shi ma malam ya fito daga turakarsa yana na shi marhabin da bakuwar Mairo domin dai labarin Nabilah kamar na Uncle ne a cikin kansu. Nan da nan ya fita ya shigo mata da damammiyar sabuwar fura da nono kindirmo gami da gasasshen nama. Nabilah karamcin iyayen Maryam ya burge ta, rayuwarsu kuma ta ba ta sha'awa. Ta raba komai biyu ta kaiwa direbanta wanda ya kawo ta. Ta dawo tana ci suna hirar bayan saduwa har goshin magriba, sannan suka yi haramar tafiya. Nabilah ta ba ta mamaki kwarai yadda ta iya ta sarkafo kai cikin surkukin kauyen su, ko da wasa ba ta kawo zata iya cika alkawarin da ta dauka ba. Ta yi zaton dai ta karbi adireshin ne kawai. Direbanta ya sauke musu kwandon dankalin Turawa da doya cikin (boot) wanda Nabilar ta kawo musu a matsayin tsaraba. Hutu ya dauko karewa, Mairo ta soma shiri cikin nutsuwa. Tarkacen da ta tafi da su da farko, yanzu duk ta rage, sai wanda zai amfane ta kadai. Ta ce da Innar ta daina tara wannan uban kanzon da ta ke tara mata, ana ba su lafiyayyen abinci sau uku a rana. Ta tsefe kanta ta wanke tas da shampoo ta je aka yarfa mata sabon kitso yiri-yiri. Ana saura kwana biyu su koma makaranta. Ta yi wankan yammanta ta sanya sabuwar atamfarta 'jaba' ta zauna a rumfar tsakar gidansu tana gyaran kumbarta. Wani yaro mai zakin muryar tsiya ya kwada sallama ya kara da cewa, "Wai ana kiran Mairo a waje", Sai ta ji abin banbarakwai ta dago kai tana hararar yaron. Dai-dai lokacin da Inna ta fito daga bayan gida rike da buta zata yi alwala a gindin rijiya, ta ce da yaron "Wane ne mai kiran Mairo?" Yaron ya ce "Wani mutum ne dogo, fari ne kamar Balarabe, kayanshi masu kyau ne, ban taba ganin mutum mai kyawunshi ba. Ga dukkan alamu daga birni ya ke". Mairo ta saki kunne tana mamakin surutun Ilu dan makotansu. Ita kuwa waye wannan? Ina za ta tsaya tana yi wa mutum irin wannan kallon kowane ne shi, balle har ta iya yin sharhi a kansa? Kanta ya daure, haka kawai ta ji tana son ganin wannan mutumin mai kiran nata. Inna ta ce "Mairo kuwa, wa ta sani a birni? Ga shi ka ce namiji ne balle ince ko diyan baffanta ne, je ka ce ba zata zo ba, haka kawai mutanen birnin nan ba abin yarda ba ne". Ilu ya juya da gudu don isar da sako, Mairo ta mike ta jawo hijabinta a jikin kyaure tana cewa "Bari na je Inna, kika sani ko sako ne daga Yaya Habibu?" Inna Hure ta ce, "Ai kuwa, maza je ki jiyo mana". Ta fita tana dariyar Inna, ganin yadda ta rikice daga ambaton Habibu. Tsaye yake jikin bishiyar maina, wadda ke gaba kadan da gidansu, sanye da kufta da wando na farin yadin boyel mai salki,
Table of Contents