Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

duka wannan kayan nata ne. Abinci kuma daga mahaifiyarsu ne sai ta rasa irin godiyar da zata yi wa Uncle din nata. Bayan tafiyarsu ta kinkimi kayanta daya bayan daya ta nufi hostel. Cikin ledojin ba komi ba ne sai biskit na kwali kala-kala da crackers na shan shayi irin wadanda ta ke ganin su Kausar na ci, dayar kuwa alawoyi ne, cakulet kala-kala masu dan karen tsada da katon na irin taliyar da ta ga dalibai suna jikawa (indomie), sai katon na lemon gwangwani (Rani). Baki ta bude cikin matsanancin firgici, ba ta taba tsammanin wai ita Mairo zata taba cin irin wadannan abincin ba a rayuwarta. Cikin kulolin kuwa bayan abinci akwai soyayyun kaji wadanda suka soyu rakau yadda za su jima ba su lalace ba, cin-cin mai nama (meat pie), cake da sandwitch masu yawa sosai. Kenan godiya ga Uncle Junaid wadda ba ta karewa. Mutanenta suka shigo, wani abin mamaki kulolinsu duk iri daya ne da nata, sai kala da ta banbanta. Suka yi kasake! Cikin mamaki ganin irin garar da ke gaban Mairo wadda ko a mafarkinsu ba su zata ba. Abin da suka dauka shi ne, ramar da ta ke kwadawa mai tsamin tsiya da kanzo su za a karo mata. To sai ga sabani ga tunaninsu, ina ruwan Allah Mai azurta bawa. Mairo dai jeren kayanta ta ke a loka, ba ta kula su ba. Nabilah ta kasa shiru ta ce, "Kausar yau billager ta shigo gari". Kausar ta ce "Ke ina jin 'charity' ne daga (MSS), ba ki san ta shiga MSS ba? Kungiyar 'yan a bamu saboda Allah?" Ita yaran sai suka koma ba ta dariya sabida yadda suka sa mata ido babu gaira babu dalili, ko mai ya yi masu zafi da ita? Allahu A'alam. Bayan bisiting da sati biyu, rannan Mairo ta fito domin yin fitsari da daddare a lokacin Kausar ma ta fito ta tsugunna a bakin rariyar hostel tana goge bakinta domin ta kwanta. Mairo na daga bandaki ta hangi wani mulmulallen abu mai sheki da tsayi na sanda ya nufi Kausar. Ta ware idanunta gabadaya sai ta gane katon maciji ne wanda ake rade-radin akwai a makarantar. Ta yar da butarta ta sheko da gudu dai-dai sanda macijin ya fasa kai, ta angije Kausar tun karfinta ta wulwula ta fada kwatami da baka, abin tsautsayi, sai kulbar (macijiyar) nan ta huce fushinta a kafar Mairo, wato ta sare ta. Kausar ta mike cike da bala'i a lokacin idanunta suka gane mata abin da ke faruwa, dai-dai lokacin kulbar ta sulale tana komawa inda ta fito, ga kuma Mairon da ta angije ta kwance a kasa ba yadda ta ke. Ta daura hannuwa aka ta rafsa ihu, wanda ya ratsa gaba dayan hostel din, student da metron suka fito. Kausar ta ce “macijiya ce ta sare ta.” Ai jin haka captain ta suri Mairo, sauran yara suka bi ta yuuu! Har da su Kausar sai gidan principal ana buga mata kofa. Ta fito a gigice ita ma nan take ta bugawa school doctor waya, nan da nan sai ga ta, aka wuce da Mairo asibitin makaranta, Doctor ta dukufa ga son ceto ranta. Kausar da Nabilah suka kasa komawa hostel ko babu komai akwai tausayin rai a zukatansu, balle ita Kausar da tasan hakikanin yadda abinda ya faru. Nadamar abubuwan da ta ringa yi wa Maryam Bedi, suka shige ta. Ta ji tausayin Maryam matuka, ta kuma tambayi kanta, shin ko wace irin zuciya ce da ita? Irin su Maryam ne masu rama sharran da hairan, babu shakkah ta yi nadama. Nabilah ta yi mamakin damuwar Kausar akan Maryam ta yi yawa, ta kasa ko magana. Ta ce "Kausar kowa ya koma hostel sai mu, ni fa tsoro nake ji". A salube Kausar ta sa kafa cikin dan karamin asibitin ta samu benci ta zauna, ba ta da niyyar tashi. Nabilah ta biyota cikin mamaki, ta ce "Wai me ya faru ne? Ba zaki zo mu tafi ba?" Ta ce "Je ki abinki Nabilah. Amma ni a nan zan kwana". Nabilah ta kama baki, dai-dai lokacin da Mummy Dukku wato principal ta fito zata koma gidanta. Ta hango su Nabilah ta ce, "Ku kuma me kuke a nan ba ku koma hostel ba?" Kausar sai ta sa kuka. Ta matso ta dafa kanta domin ta santa farin sani sabida mahaifinta, ta ce "kawarku ce ince ko?" Nabilah ta yi saurin cewa "A'ah, dakinmu ne kawai daya". Mummy ta lura da kukan da Kausar ta ke sosai ta ce, "Ke kuwa tausayinki ya yi yawa Kausar, alhamdu lillahi dafin bai shiga cikinta ba, kuma Doctor ta zuke shi. Insha Allah zuwa safiya za ta warware, tashi ku tafi dare ya yi sosai". Sai da suka je daki ne Kausar ta ke gayawa Nabilah hakikanin yadda akai maciji ya sari Maryam. Ta ce "Yanzu ni tashin hankalina shi ne, idan ta mutu ban nemi gafararta ba ina zan sa kaina?" Jikin Nabilah ma ya yi sanyi, ta ce, "Allah Sarki, irin su ne ake cewa masu halin 'yan aljannah". Suka yi jugum-jugum har wayewar gari ba su runtsa ba, nadama ta ishe su, sai kuma kaunar Maryam farat daya ta bi zuciyoyinsu. Washegari Uncle ya zo kiran suna kamar yadda ya saba, cike da mamakin rashin ganin Maryama a class don kullum ya shigo idanuwanshi akan wurin zamanta yake. Duk da haka bai fasa kiran sunan ba, har ya zo No. 40, shiru ba ta amsa ba. Ya dago manyan idanunsa ya zubawa Kausar cike da zargi kamar ita ce ta boye Maryaman. Ya ce "dakin ku daya, tana ina ban ganta ba?" Kirjinsa har wani harbawa yake da sauri-da-sauri. Fargabarsa kada ace da shi iyayenta sun cire ta daga makarantar sabida su Kausar. Bakin-cikinsa shi ne yau ace Maryama ta bar makarantar nan. Tashin hankalinsa shine ko sunan kauyensu bai sani ba, alhalin yanzu yadda yake kaunar Ilham haka yake kaunar Maryama. Idan zai iya rabuwa da ita, to hakika zai iya rabuwa da Ilham. Cikin in-ina Kausar ta ce "Maciji ne ya sare ta, tana kwance a maternity..." Tun kamin ta kai karshe Uncle ya fita. Ya doshi maternity cikin matsanancin tashin hankali, ko gani ba ya yi sosai. Ya banka kofar da kafarsa babu neman izini. A kwance ta ke, idanunta a rufe, rana daya kacal ta zabge, ta yi wani irin fari fat kamar babu jini a jikinta, sannan ta kumbura kamar an hura balam-balam. Nurse din da ke kokarin daura mata 'drip' ta juyo a razane ta dube shi, bai kula ta ba ya karisa gaban gadon da Maryam ke kwance ya tsaya kurum yana kallonta. Kamar an ce da ita bude idonki, ko kuma alamar tsayuwar mutum ta ji a kanta oho, ta bude fararen idanunta a hankali wadanda suka kumbura suka yi mata nauyin budewa, a hankali ta ce "Uncle…….." Sai hawaye suka zubo ta gefen idonta. Ya yi saurin kama hannun damanta, ya ce "Sannu Maryama, sannu kin ji. Allah Ya ba ki sauki". Ya juya ga nurse din ya ce "Edcuse me madam Serah, na yi miki shisshigi cikin aikin ki. Maryam na daga cikin dalibai na masu muhimmanci a gare ni. Ki yi hakuri". Ta yi murmushi ta ce

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21