Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

wuya wurin Allah Maryam da Nabilah suka zana jarrabawar wucewa babbar sakandire (SS.1), wato placement, suka fara shirin tahowa hutu. Sai dai kamin lokacin Maryama ke daukar na daya, Nabilah na biyu, ko Nabilah na daya Maryam na biyu. Kamin kuma su zana jarrabawar nan ba haka Uncle ya barta ba, sai da ya tabbatar ya tusa mata karatu cikin kwanyar kanta ta yadda faduwa, sai wani babban ikon Allah. Zuwa lokacin Maryama ta kara girma, matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha biyar. Zama da Nabilah ya sa Mairo tasan me ake kira 'gyara' na diya mace. Ta yi sharr ta yi 'fresh' jazur da ita. Kirjinta ya soma cika dagwas haka kirarta ta soma fitowa na alamun budurci. Gashin kanta ya mike baki sidik na Fulanin usuli sabida samun gyara. Duk wani abu da tasan zata yi amfani da shi a kantin makaranta ta ke saye ta tafi da shi gida, wasu abubuwan kuma daga Nabilah ta ke samu duk da ko yaushe cogewa ta ke da karbar abin hannun Nabilah, amma naci da mitar Nabilah ke sawa ta amsa wani zubin ko ta ki ko ta so, don ba zata barta ta zauna lafiya ba da korafi da mitar ba ta dauke ta ‘yar uwa yadda ta dauke ta ba. Suka kare jarrabawa ta dawo gida inda ta tarar da tashin hankalin da ba ta taba haduwa da shi ba a rayuwarta. Malam Beddi ya fadi a gona rabin jikinsa ya mutu (paralysed), sai dai a kwantas a tayar. Mairo ta yi ta kuka kamar ranta zai fita, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a rayuwarta. Daga kwancen da yake Malam Bedi, ya miko hannun shi mai lafiyar ya kamo hannunta yana dan girgizawa alamun lallashi. Mairo ta soma damuwa kwarai da rashin zuwan Habibu, tana tunanin da yana nan, da tuni ya kai Babansu asibiti, shekaru biyar curr ba aike ba sako, anya kuwa Yaya Habibu bai manta da su ba? Daga ranar ta ajiye komi ta shiga taya Innarta jinyar Baban. Ita ce ke ba shi abinci safe, rana da kuma dare. Ita ke yi masa alwala ta fuskantar da shi alkibla, yayin da Innar ke kula da tsaftar jikinsa da dahuwar abinci. Maganar makaranta Mairo ta ajiye ta a gefe, ba ta jin tana da ranar komawa har sai Allah Ya baiwa Baba sauki. Duk da shelar da ake ta yi a rediyo na cewa, a koma. A karshen watan Allah ya jefo Alhaji Abbas ya tarar da halin da dan uwansa ke ciki, ya yi ta yi wa Hure fada kamar ya doke ta ya ce, mai yasa ko da kanta ba zata je ta fada masa ba? Da dan uwansa ya mutu cikin wannan halin da ba zai yafe mata ba. Ya debo su duka a motarsa suka taho asibitin Murtala a Kano, aka ba su gado. Nan aka ci gaba da bai wa Malam Bedi kulawa ta masu lalura irin tasa 'Physiothearaphy'. Har zuwa watanni biyu, babu wani canji ko hannunsa ba ya iya motsawa. Mairo cikin asibitin ta zama 'yar gari ba inda ba ta shiga. Rannan Malam Bedi ya bude baki ya yi magana, ita da Hure suka matsa sosai cikin tsananin murna, suka kasa kunne don jin abin da zai fada. Babu abin da ya ke ambato sai, "Habibu... ku kirawo min Habibu". Dukkansu babu abin cewa, dai-dai lokacin da Ladidi daya daga cikin 'ya'yan Alhaji Abbas ta shigo dauke da kwanukan abincinsu. Tana yatsina ta ajewa Innar kwanukan babu ina wuni, balle ya mai jiki. Ta juya zata fita, wannan al'adar 'ya'yan Alhaji Abbas ce ga su Hure, tun zuwansu asibitin don ba su ga dalilin da Alhajinsu zai damu da wadannan shirgin kauyen ba akan wannan gawa-ta-ki-ramin Bedin, shi a wahale su a wahale. Kullum dare da rana ana aikensu kawo abinci, tun daga Yakasai suke takowa a kasa har zuwa asibitin. Yanzu kam yaran har buyarwa iyayensu suke idan lokacin kwashe abincin ya yi a neme su sama da kasa a rasa, wani lokacin sai shi Alhajin ne ke kawowa da kansa. Har ta kai bakin kofa sannan ta juyo ta ce "Ke Mairo, tare muke da wani mutum wai yana nemanki, Baba ne ya hado ni da shi na nuna masa ku". Ta ce "Yana ina?" Ladidi ta ce "Ga shi can a kofar shigowa ward din nan". Ta kada kai ta fita abinta. Mairo ta sanya gyale ta fito tana dube-dube, sai ji ta yi cikin taushin murya mai cike da damuwa an ce "Sannunki Maryam, kin kyauta". Ta daga idanunta a hankali ta dube shi cikin mamaki, Uncle Junaidu ne, rungume da hannayenshi a kirji, kafarshi ta dama jingine da bango, ya yi rama ainun cikin riga da wando na yadin siliki. Suka zubawa juna ido na 'yan dakikai, kamin ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba, suna diga kan tafin kafarta. Uncle ya kula, ya ce "Ni ne ya kamata na yi kuka ba ke ba. Ni da kika bari cikin zullumi da yawon nemanki kusufa-kusufa. Idan har yanzu ba ki yi hankalin da za ki damu da damuwar masu kaunarki akan ki ba, sai yaushe ne Mariama? Watanni uku Baba ba lafiya ba ki neme ni kin sanar da ni ba, ba ki sanar da hukumar makaranta uzurinki ba. Na raina wayonki Mariama, kin bata min sosai, amma hakan da kika yi ya taimaka min wurin gano matsayin da kika ba ni a zuciyarki. Na gane ba ni da wani muhimmanci, ni kadai na…...." Muryarshi ta sarke sabida takaici, ya wuceta ya shiga ciki yana raba ido a cikin ward din, har ya hango Inna Hure tana yi wa Malam firfita. Da sauri ya karasa ya rungume dattijon hawaye na fita mishi tararara! Bedi ya mika hannunshi mai lafiyar yana shafar kanshi, ya ce, "Habibu...." Ya zube a gabanshi ya kamo hannunshi ya rike tamau cikin nasa kai ka ce mahaifinsa ne. Ya ce "Baba ba Habibu ba ne, Junaidu ne, Baba Allah Ya ba ka lafiya". Jikinshi na mazari da karkarwa ya ce, "Junaidun-Mairo?" Ya ce "Shi ne Baba". Ya kama hannunshi da nashi hannun mai karkarwa ya ce "Ina Mairo?" Mairo da ke rakube a gefe tana rasgar kuka maras dalili, ta karaso ta ce "Ga ni Baba". Ya ce "Miko min hannunki". Cike da fargabar abin da Baban ke shirin yi, ta daura hannunta na dama akan nashi. Ya zare nashi, nata ya sauka akan na Junaidu, ya kama su duka biyun ya dunkule ya ce "Na ba ka amanar Mairo, ka rike min ita amana kar ka bari a raba ta da mahaifiyarta. Idan Habibu ya dawo ka damka masa ita, shi kadai na yarda ya rike min Mairo sai uwarta, kai kuwa dama amanata da kai…. ita ce karatunta……." Ya zare hannunshi ya yi shiru. Jikinsa ya mace murus, daga shi har Mairo an rasa wanda zaiyi jarumtakar fara dauke hannunsa. Ita kuwa Hure tana gefe akan tabarma tana ta sharar hawaye, ya yi ta maza ya zare hannunsa cikin karfin hali ya ce "Baba Allah zai ba ka lafiya. Da yardar Allah kai zaka ci gaba da rikon Maironka, har ka daura mata AURE". Haka suka kasance har dare, jikin Malam ya

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21