Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ki dadi. Bayan sallar isha'i Junaidu ya tafi gida da alkawarin gobe da sassafe zai zo ya nema masu (transfer) zuwa asibitin Aminu Kano. Da asubahin ranar Hure ta tashi ta ciko ruwa a buta ta dauko roba ta zo da niyyar yi wa Bedin alwala. Allahu Akbar ashe Allah Ya amshi abinSa cikin dare. Ta ja mayafi ta rufe masa ido ta yi alwala tana hawaye ta tada kabbarar sallah. Mairo ta tashi daga kan tabarmar da ta ke kwance ita ma ta yo alwalarta ta tada sallah. Da ta idar ta juya tana gayas da Inna, a nan ta lura Innar lazimi ta ke tana kuka. Sai ta ja gefe ita ma ta soma kukan da ba tasan dalilinsa ba. Gari ya yi dan shaaa! Haka, Misalin karfe shidda da rabi na safe, Junaidu ya iso biye da shi, Ilham ce rike da filas din ruwan zafi da filas din abinci. Shi kuma niki-niki da ledoji ya rusuna yana gayas da Inna, tare da tambayarta lafiyar mai jiki. Ta daure ta ce "Ka taimaka ka je gidan nan na Yakasai, inda idan aka rakoka nan, ka fadawa maigidan ya zo ya dauki gawar dan uwansa a yi masa suttura". A firgice Junaidu da Mairo suka dago, kamin dukkansu su karasa ga gadon Malam Bedi. Mairo ta sa hannu ta yane zanin da Inna ta rufe shi da shi. Ta tabbatarwa kanta Innar ba wasa ta ke ba, sai ta sulale a kasa ita ma babu alamun numfashi a tare da ita. *** *** U ncle Junaidu ya yi mata halarcin da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. Tare da shi aka yi ta zaman makoki har tsayin kwanaki bakwai, mahaifiyarshi da kannenshi duka ya kawo su sun yi wa Inna Hure gaisuwa. Ranar da aka yi sadakar bakwai ya tura aka kira masa Mairo azure, ya kara yi mata ta'aziyya, ya kara da nasihu masu sanyaya rai da karfafa gwiwa. Ya ce ta daure sati mai zuwa ta dawo makaranta har zangon ya yi nisa ba tareda ita ba. Ta rantse masa zata dawo amma tana tausayin Innarta, yadda zata barta cikin kewa. Ya ce "Wata rana aure zaki yi Maryama, ke da Inna sai gani da yawo, ita kanta tasan hakan. Don haka ki taimake ni in rike nauyin da marigayi ya aza mani akan karatunki". Bayan tafiyarsa Mairo da Innarta idan ka gansu gwanin ban tausayi. Tunanin Mairo shi ne, wa zai dinga nomawa Innarta abin da zata ci? Idan wanda ke cikin rumbunsu ya kare? Allah maji kan bawa, washegari sai ga Alhaji Abbas niki-niki da kayan abinci ya kawo musu. Ya kuma ce, wannan nauyin ya dauke shi insha Allahu. Sai a nan hankalin Mairo ya dan kwanta duk da Innar ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba. Shi ma Alhajin ya yi mata zancen makaranta ta ce, insha Allah karshen wannan satin zata koma. Hakan kuwa aka yi, ranar litinin ta yi shiri ta koma makaranta. Nabilah ta yi mata ta'aziyyar babanta wanda ta ji a bakin Uncle Junaidu. Rayuwar Mairo ta sauya kwarai, ta zama babu walwala, akwai shakuwa da kauna mai tsanani tsakaninta da mahaifinta, don haka ta ke jin kanta tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai ta samu kanta da son yin abin da zai debe mata kewa, don haka ta fara tunanin yin RUBUTU. Tana yi tana gutsirewa ta ajiye, idan ta ji bai yi mata ba. Kamar da wasa, ta fara rubutun labarai cikin harshen Turanci a kalla guda biyar tana yagawa. Lokacin da ta shiga aji biyar na babbar sakandire aka ba ta kallabin 'AMIRA' sabida hidimarta ga masallaci da kungiyar dalibai musulmai da Uncle Junaid ya sa ta. Haka nan ita ce ja gaba a club din Uncle, watau English club. Kowa yasan Uncle Junaid a Minjibir, yasan shi tare da Maryam Bedi. Mairo ce mai rubutawa club din DRAMA Uncle ya yi gyara a gabatar da ita. Wannan wata hikima ce da Allah Ya yi mata wadda ke bai wa kowa mamaki. Sai dai iyaka kwakkwafinka da sa ido, haka nan so kulla karya da sharri, ba zaka ce akwai soyayya tsakanin Junaid da Mairo ba, sai mutunta juna. A wannan hutun na zangonsu na biyun karshe a sakandire da Mairo ta zo gida. Ta tarar da ciwon kafar Inna ya yi tsanani. Ko bayan gida ba ta iya takawa sai dai ta ajiye (foo) a kusa da ita. Don haka Mairo ta kara kadewa ta rame, ta kuma soma tunanin jingine makaranta domin Innarta, tun tana tunanin Habibu har ta watsar ta hakura da shi, shi da ya ce shekaru shidda kacal zai yi. Ta tabbata inda duk Habibu ya ke tunda ya iya ya yi shekaru takwas bai neme su ba, to babu shakka ya manta da su, ya samu sabuwar rayuwa a gaba. Ba zata taba amincewa da cewa wani mugun al'amari ne ya faru da shi ba, tunda kuwa lafiya ita ke buya, amma ba rashinta ba. Cikin watan January ne sanyi ya yi tsanani, hazo ya mamaye sararin samaniya, wanda duk ya yi kuskuren fita babu shakka gashin ido dana girarsa fari fat za su koma. Mairo ta dawo daga wani chemist inda ta amsowa Inna maganin mura tana tafe yafe da mayafin gyauton atamfa, ta dunkule hannuwanta wuri guda.Tana ta sauri domin ta daura dafa-dukar taliya akan wuta, wadda zata bai wa Innar, kasancewar ba komi ta ke iya ci ba, sai abu mai laushi, kuma mai dan ruwa-ruwa, duka Mairo na kokari a kai. Ta kada ta raya da Innar ta kai ta asibiti, amma Innar ta ki, ta ce, ciwon kafa ba a kanta tsoffi suka fara shi ba. Ta doso zauren gidansu ke nan ta hange shi, tsaye a kofar gidansu. Sanye yake da farar shirt (Armani) da dogon bakin wandon jeans ya daura jibgegiyar rigar sanyi mai hade da hula bisa. Duk hazo ya ba ta tsararren gashin idonsa, girarsa da sajensa. Mairo ta ce a ranta, Allah Sarki Uncle! Cikin wannan sanyin ya taho tun daga Minjibir sabida rashin komawata makaranta. Tun daga nesa ta ke yi masa murmushi amma shi fushi yake sosai. Ta kariso cikin nutsuwa, tana karasowa ta russuna tana gayas da shi ya ce "Ni bana son wata gaisuwarki, kawai shiga ciki ki hado kayanki ki zo mu tafi". Ta girgiza kai kamin ta wuce cikin gidan ya bi ta a baya. Ta fara da sauke tukunyar daga kan wuta, kana suka karasa dakin Innan da sallama. Shi kansa ya girgiza da ganin ramar da Innar ta yi, tana kwance bisa katifar auduga ta amsa sallamar su. Nan ya gano amsarsa ta rashin komowar Mairo makaranta. Jikinsa ya yi sanyi, ya daga manyan idanunsa ya dube ta suka yi wa juna kuri da ido. Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A yanzu kam ji ta ke ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da Alhaji Abbas na iya kokarinshi akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan cikin matsananciyar damuwa, ya ce "Sannunku da jiki Inna, amma ya dace ki

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21