Chapter 6
Chapter 6
ta yarda wai shekaru shidda zai yi bai dawo ba. A ganinta shi ne Habibu na iya dawowa yau, ko gobe, don kawai ya rutsa ta, ya ga irin kwazonta. Saboda haka cikin shekara guda kacal, Maryam Bedi, ta zama zarrah a ajinsu na boko, kan gaba a ajin islamiyyah, wadda ke da haddar izfi ashirin na Alkur'ani a cikin kanta. Sauran littattafan addini kuwa idan ta bude su tana karantawa tana fassarawa Inna tsarki da alwala, da irin sallar khashi'ai da sallar da ake dunkulewa a jefowa bawa kayarsa, tun kamin ya tashi akan dardumarsa. Sai Inna ta sa habar zaninta tana share hawaye, ta ce "Ba karamar cuta na so na yi miki ba Mairo". Shekaru uku ke nan cif da tafiyar Habibu, kuma a yau ne ranar saukar su Mairo. Ta sha wanka da sabon dinki na atamfa (hitarget) da suka yi anko gaba dayansu. Ta dora wani sabon farin hijabi akai, wanda ya tabo har gwiwarta. Ta azalzali Innarta ta yi sauri ta gama shiryawa su tafi kada wajen zama ya cika ta rasa inda za ta zaunar da ita. Innar kuwa sai sake murza kwalli ta ke a idanunta yadda zata fito radau! Ta kuwa fito din, sai kyallin wanka da basilin ta ke. Suka jera abinsu Mairo na ta addu'ar samun nutsuwa cikin zuciyarta sakamakon ganin cincirodon al'ummar kauyensu wadanda ake nufin ta yi karatu a gabansu. Tuni Malam Bedi ya isa wajen tun kamin su zo, yana cikin rumfar iyaye maza, a sahun gaba, yana ta ware ido don ganin ta inda Mairo zata bullo. Can ya hangota rike da hannun Innarta, ta samu wajen zaman da ya dace da Innar ta zaunar da ita, sannan ta karasa cikin 'yan group dinsu suka yi sansani. Taro ya yi taro, mai gabatarwa ya fara gabatarwa bayan bude taron da addu'a, daga limamin garin Gurin-Gawa. Maryam Bedi, ita ce wadda aka fara kira ta bude taron da karatun Alkur'ani cikin daddadar kira'arta kai ka ce diya ce ga Khusairi, inda ta karanto karshen suratul Fathi, wato ayar nan ta "Muhammadurrasulullah…...." Gaba dayan jama'ar dake wajen jikinsu ya yi sanyi, sai ga Malam Bedi yana kuka. Da ta dasa aya aka dauki kabbara kowa na cewa "Ai Mairon Hure ce, diyar Malam Bedi". Innar kuwa sai washe baki ta ke, bakinta ya ki rufuwa don kuwa duk matan da suka san ita ce babar Mairo, sai gaisawa suke da ita. Yayin da 'yan bakin-ciki, wato wadanda ke da 'ya'ya a makarantar ba a kuma kirawo 'ya'yansu ba sai zumbure-zumbure suke yi mata, ko a jikinta wai an tsikari kakkausa. Haka nan Mairo ce dalibar da aka fara kira ta amshi allonta daga hannun Mai girma shugaban karamar hukumar Kumbotso. Malaminsu ya karanto mata farkon suratul Bakara tana bi tiryan-tiryan cikin kira'ar da ta fi ta malamin. Bayan nan Mairo ta karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya Tajwidi, sannan daliba mafi da'a a gaba dayan daliban shekararsu. A sa'ilin da maigirma Chairman ya amshi lasifika domin gabatar da jawabinsa na babban bako mai jawabi. Budar bakinsa sai cewa ya yi "Na dauki nauyin karatun wannan yarinya MARYAM BEDI a makarantar sakandiren 'yammata ta gwamnatin tarayyah da ke Minjibir". Gabadaya aka sa kabbara. Abokan Malam Bedi suka shiga taya shi murna, ya rasa inda zai sa kansa don farin ciki. Mairo ta riga su komawa gida domin an ce su tsaya za su gana da Chairman. Inna Hure na shigowa ta suri Mairo ta goya a baya, ta sa zane ta daure ta, ta sa majanyi ta kara daurewa. Ta shiga zagaye dakin da ita, ita kuwa sai dariya ta ke. Kamin su zauna gabadayansu. Malam Bedi ya gabatar musu da bayanin da maigirma chairman ya yi masa na cewa, zai tallafawa karatun Mairo a babbar makaranta ta gwamnatin tarayya. Zai mika komai ta hannun shugaban makarantarsu ta boko tunda dama gab ta ke da zana jarrabawar fita firamare. Ya kare da cewa. "Amma fa makarantar ta kwana ce". Nan da nan farin cikin da ke makale a fuskar Inna Hure ya yaye, Mairo ta lura da hakan, ta ce "Haba Inna, wannan ba wani abu ba ne. Zan dinga zuwa hutu kuma ana zuwa ziyara. Kin san Lanto ma ta gidan Kado tana makarantar kwana a Kwa. Duk bayan watanni uku dawowa ta ke. Sannan bayan kowanne wata ana zuwa ziyara". Inna ta ce "To ni wa zai kai ni birni? Har in gano ki a kowanne wata?" Ta ce "Allah Shi zai kai ki, ga iyalin Baba Abbas za su iya raka ki". Nan da nan Hure ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Ke, raba ni da wadannan mutanen. Ni dai na yi hakuri har ki zo hutun". Mairo ta yi murmushi ta ce "Shi ke nan Inna". Malam dai jinsu yake a zuciyarshi yana mamakin dalilin Hure na kin son yin zumunci da iyalin dan uwansa. Bai sani ba ita a ra'ayinta shi ne, idan har zata ke shiga shirginsu wata rana za su sake yin yunkurin rabata da Maironta don taje tayi masu bauta amma ba don Allah ba. Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Mairo aka kammala zana common entrace, aka zauna gida zaman jiran sakamako. Ba jimawa ya fito, shugaban makarantarsu ya mikawa Chairman. Cikin sati uku sai ga takardar daukar Maryam Bedi, cikin sabbin daliban FGGC Minjibir na shekarar. A na so kuma ta isa makaranta cikin sati biyu, hedimasta ya kira Malam Bedi ya damka masa ya kuma gaya masa ya hadawa Mairo kayan abinci da ake hadawa dan makarantar kwana, ya kuma ba shi katifar Mairo da filo, domin makarantar ba sa bukatar akwatun karfe. Malam Bedi ya dawo gida shi da Hure aka hau shawarar abin da za a hadawa Mairo, Hure ta daka mata kuli-kuli ta kuma shanya mata Rama mai yawan gaske, da zata dinga jikawa idan ta yi sha'awa ta kwada ta ci, kwaki kwano biyar, kanzo kwano uku, yaji rabin kwano, omon wanki da sabulun wanka. Man shafawa da man kitso, man kuli da manja. Mairo ta ce, su sayo mata brush da maclean, aka siyo a Fanshekara. Shi ke nan kaya sun hadu sai tafiya. A daren Inna Hure ta kwaba lalle ta yaba mata a kafafunta aka daure aka kuma zura hannun dama cikin dumar lalle, shi ma kan safe ya yi jawur kamar jini, duk adon tafiya makaranta ne. Aka tsefe kai aka yi mata kitson doka guda takwas. Babanta da Hedimasta su za su kai ta Minjibir, don haka tun karfe bakwai hedimasta ya ke buga musu zaure da yake shi ma Chairman ya cika shi da abin arziki duk don ya kula da karatun Mairo. Mairo na kuka Innarta na yi, a haka suka rabu. Hedimasta dauke da katifar kwanan Mairo, malam Bedi rike da dindimemiyar (Ghana Must Go), a haka suka doshi tasha. Hedimasta na ce da Bedi daga wannan zuwan da zamu yi da kai, duk hutu kai kadai zaka dinga kawota, don haka ka dinga kula da duk abin da na yi". Malam Bedi ya ce "To, angode dai". Suka samu bayan motar rake suka dane, ta fito da su Fanshekara, daga nan suka hawo motar Bata/Kuroda. A nan suka hau
Table of Contents