Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

za ku rike 'ya'yanku har zuwa sanda Allah Zai kawo mata mijin aure. Wannan yarinya marainiya ce, don haka wadda duk ta zalunce ta cikinku Allah ba zai barta ba. Idan ta yi ba dai-dai ba ku kwaba mata, ku sa ido akan tarbiyyarta kamar yadda zaku yi wa 'ya'yan cikinku. Ke kuma Mairo wadannan iyayenki ne, ba ki da wanda ya fi su, don haka ki yi musu biyayyar da zaki yi wa iyayenki. Ki kai kayanki dakin Ladidi ku zauna tare, Allah Ya jikan Bedi da Hure". Cikin zuciyarta ta ce "Ameen". Hawaye suka kawo mata zarya. Habiba ta ce "Dakata Alhaji, amanar maraya ka ce ka bani ko? Idan na ci Allah Ya ci tawa, to ban karba ba, balle ace na ci amana. Sai dai zama na kinzo-na-zo kowa zaman kansa yake. Ita zaman uba ni zaman miji". Hajara ma ta ce "Ato! Gaskiyarki Yaya, ni ma abin da zan ce kenan sabida rikon maraya wuya gare shi. Da idan ba wanda ka haifa ba ko goyonsa zaka rika yi kullum ba zaka fita ba. Dubi Mairo gansamemiyar budurwa ce da tasan abin da ta ke yi. Don haka ta yi wa kanta fada, kada inyi ace don ba 'yata ba ce". Suka karkade zannuwansu suka yi daka. Daga Mairo har Baffanta kowanne gwiwa a salube, ya dade kai a duke, haka ita ma. Daga bisani ya ce, "Ki yi hakuri Mairo, na rasa me ke tsakanin Hure da su Habiba, ki rabu da su ki yi rayuwarki cikin walwala, duk wata matsalarki ki yi kokarin sanar da ni. Ya ya batun makaranta kuma?" Ta ce "Nan da kwana uku nake son komawa idan na natsa". Ya ce "To gaya min abubuwan da kike da bukata gobe sai na sayo miki". Ta gaya mishi yana rubutawa, ya sanya takardar cikin aljihun gaban rigarshi ya mike ya ce, "Zo dauko kayan na nuna miki dakin Ladidin". Ta sungumi jaka ta bi shi ya nuna mata dakin ya fita. *** MAIRO A GIDAN BAFFANTA M airo ta yi zugum ta zubawa jakar kayanta ido cike da tunanin yadda za ta yi rayuwa a wannan gida. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah. Ta ji tausayin Baffanta Alh. Abbas da bai yi dacen matan aure ba. Da ganin shi ba shi da katabus a gidan. Ba ta gama tunaninta ba Ladidi ta yane labulen dakin ta shigo fuskar nan a turbune, kamar wadda aka yi wa shegen duka. Wannan fushi ba na komai ba ne, sai don hadata da Mairo daki daya da Baban ya yi, ba ta kuma da yadda zata yi. Mairo ba ta kulata ba, ta maida kai ga littafin da ke hannunta tana karantawa. Allah-Allah ta ke litinin ta zo ta koma makaranta, wannan ne kadai ta ke ji zai sanyaya mata zuciya. Washegari tun bayan da ta yi sallar asuba ba ta koma barci ba, ci gaba ta yi da lazimi har gari ya soma haske. Ta mike ta ninke sallayar ta fito tsakar gida ta tarar da tulin wanke-wanke a gindin famfo, ta nade zaninta ta ja kujera ta zauna ta soma wanke kwanukan, duk gidan ba wanda ya fito, ta gama ta share tsakar gidan tas! Dai-dai lokacin Habiba ta fito zata yi alwala ta ganta tana sharar ga kwanukan ta wanke mata, ranta ya yi dadi, ta dan saki fuska, ta ce "Ah'ah Mairo daga zuwanki? Ai aikin gidan nan ya fi karfinki, kada ki dorawa kanki abinda ba zaki iya ba". Ta yi murmushi, ta ce "Ai babu komai Mama, abin da jibi zan koma makaranta har ina aikin ya ke?" Ta wuce bayan gida ranta ya yi dan sanyi da Mairo, tunda da alamun za a yi zaman lafiya da ita, tunda ba ta da kiwa. Da ta gama ta yi wanka, ta shafa mai ta sanya atamfa nichem wad, ta ci gaba da karance-karancenta. Ladidi ta shigo musu da kwanon koko da kosai, ta debi nata ta turawa Mairo ragowar ba ta ce ko uffan ba. Mairo ta rasa wace irin yarinya ce Ladidi kamar ita ba jininta ba ce. Ta ga ba ta da alamun yi mata magana kamar ba daki daya suka kwana ba. Wannan sam ba ya daga cikin tsarin musulunci, don haka ita ta sauke kai ta ce "Mun kwana lafiya Ladidi?" A lalace ta ce "Lafiya lau". Da haka Mairo ta ja bakinta ta yi shiru, ita kuma Ladidi ta yi wanka ta fice daga gidan. Da yamma Baba ya dawo, har dakin ya bi ta, ya same ta da ledoji niki-niki ya yo mata sayayyar komawa makaranta. Ta yi hamzarin mikewa ta karbe shi, ya ce "Duba ki gani, idan da abin da babu ki gaya min na koma na karo". Tana bude kayan tana dubawa ta ce, "A'ah komai ya yi Baffa, madalla na gode, Allah Ya kara budi". Ya fita yana cewa "Ki dai saki jikinki a gidanku, don Allah Mairo". Tana kokarin hada kayan don ta maida su cikin ledarsu. Tsulum! Aunty Hajara ta bankado labulen dakin ta shigo. Idanunta akan kayan ta kama haba ta ce "Iye! Gata maganinka Allah! Mu yaushe aka taba saya mana kayan masarufi haka a gidan nan? To wallahi ba zata sabu ba, biyu zan raba su na dauki rabi". Ta soma kasa kayan bayan ta zazzage su daga ledojinsu. Ta kwashe rabi ta zuba a leda guda ta yi waje da su, ko kunya babu. Mairo na zaune tana kallon ikon Allah, ashe ba ta gama mamaki ba, don Habiba ganin Hajara ta fito da kaya fal leda ita ma ta zabura ta yi dakin, ta ce "Mairo miko kayan nan a cire na Ladidi". Ba musu Mairo ta mika mata buhun baccon, ta kwashe na arzikin su kayan shayi da sabulai, ta tura mata sauran da ko sati ba zasu yi mata ba. Ita ma ta fice tana fadin "Gara mu ci arzikin albarkacinki, don idan namu 'ya'yan ne ai ba za a siya musu haka ba, ita ma Ladidi ta sha shayi ta ji ya dandanonsa ya ke". Da ta ga idan ta biyewa wadannan mutanen za su sanyata kuka, sabida rashin imaninsu, sai ta dauko littafin addu'o'i na Hisnul Muslim ta soma karantawa idanuwanta cike taf da kwallah. Wadannan su ne 'MATAN BIRNI' ke nan. Wato duk matan birni ba su da kirki, daga na masu kudinsu har talakawansu. Al'ummar kauye ba haka suke ba, mutane ne masu kara da karimci. Matan birni dansu shi ne nasu, dan wani kuma ko oho! Ta yarfe hawayen idanunta. Wajejen karfe sha biyu na rana, Hajara ta kwaso jibgin wankin yaranta ta jibge a gindin famfo, ta kwalawa Mairo kira wadda wani matsiyacin barci ya soma fizga kadan-kadan. Nan da nan ta gyagije ta amsa, ta fito "Ga kayan kannenki nan ki taimaka ki wanke musu kan la'asar, saura ki zauna kailula har uban naki ya dawo ya ce don me na saki aiki". Ba musu Mairo ta amsa da "Zan yi sauri Aunty Hajara". Ta soma dirzar dukunkunannun kayan wanda kamin ta wanke wando daya ya fita, sai an yi minti ashirin sabida tsabar daudar da suka yi. Don haka wankin ya kai ta har karfe hudu. A lokacin an

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21