Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,230 words 0 views Progress saved
Download Book

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels FATAN ALHERI Fatan ALHERIN littafin na sabon jaririn dana Haifa ne, AHMAD AL- KHAZRAJY. TUKUICI Tukuicin littafin na mai sunan Mamin mu ne, AMINAH SHEIKH AL-FATIH (Leena). A BARI YA HUCE... 1 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR takori88@yahoo.com Hakkin Mallaka; Takori Copy write; Takori Shekarar Rubutu; 2012 GARGADI Juya littafin ta kowacce hanya ko sake bugawa (reprinting) ba tare da izni ba abin tuhuma ne daga Lauya na Barrister Abdurrahman Yunusa ESK. idan kunne ya ji……! GODIYA Godiya ta mussamman ga aminiyata Haj. Zainab M. Ahmed Sultan Road, Kano. Banida abinda zan biyaki face addu’ar nan da kullum nake mana. Allah ya raya Mukhlis, Muhsin, Muslim, Munifa da auta Hanifa. GORO Goro ne ga Hadiza Umar Dogon-Daji (Mrs. Jelani Aliyu) Michigan, USA. Allah ya raya mana Amira, Mubarak da Asma’ul Husna. KUNA RAINA Hajiya Zulaiha Zubair (Zulai), Mrs. Tafida Ahmad-Khazrajy ya gode. Tareda ‘yar uwarki Haj. Zuwaira Ahmad Rufa’I (Mrs. Engineer Baffa Sayyadi) Marubuciyar littafin Sanadin Kaddara. DOMIN KI Littafin ba zai manta dake ba, da kuma dimbin kaunar da kike yiwa mai shi, Haj. Habiba Umar, Ireland, UK…out of sight.. is neber out of mind! TUNA BAYA …….! Wai Takori tace Tuna Baya Shine Roko; Mariya Usman Sarki Zuhra Amin Nasir Galadanchi Nafisah Ahmad Muhammad Sadiya Ahmad Muhammad Allah ya taimaki malaman Galadanchi, Allah ya taimaki ZUBAIRIYYAH ISLAMIYYAH! ASSALAMU ALAIKUM Masoyan TAKORI, sallama a gareku. Yaya gida, maigida, karatu da harkoki? Dafatan ALHERI, domin ALHERIN nake nufinmu dashi bakidaya, shiyasa nake yin rubutun. Masu rubuto ‘tedt’ Takori bata (replying), masu bugo waya Takori bata dauka ba, masu rubuto sako ta ‘facebook inbod’ Takori bata bada amsa ba, da masu aiko ‘friendship rekuest’ Takori batayi ‘accepting’ ba. Gabadaya sai in hada inyi muku jimillah, in baku hakuri in taushi zuciyarku, sabida al’amarin ne yafi karfi na, ya kuma shallake tunaninku. In kun duba karancin lokacin da ake fama dashi a yanzu zaku yi min uzri. Sannan rubutun ba sana’a ta bace. Har yanzu ni Daliba ce. Ga RAINO ga sauran al’amura da suka sha gabansa. Masu kiran waya kuma in ban dauka ba a zazzageni sai ince kada ku zargeni, tunda nace (tedt only). “Ai karya take bata da wani ‘hearing problem’ don kar a dameta ne kawai” wata kuma tace “kedai kawai ki fadi gaskiya, bakya daukar wayar da bata ‘yan uwanki, kawayenki da wadanda kika sani ba” da sauran su. Kalilan ne, kuma masu hankalin ke cewa “Allah ya yaye miki TAKORI”. To masu yimin wannan addu’ar, nima ina yi muku addu’ar Allah ya biya muku bukatunku na ALHERI. Duk masoyana ina sane daku, koda kuwa ace sau daya ne muka taba gaisawa. Musamman Sokkotawa, ‘yan Gusau da Katsinawa. Wallahi duk ina sane daku, kuma ban mance da sunan kowa ba. Ga masu cewa wai bani na rubuta littafin ALKAWARI BAYAN RAI ba, sabida yayi (short) kuma salon sa da tsarinsa ya banbanta dana sauran littattafan TAKORI, da yawama kai tsaye sun ce bai yi musu dadi ba, to sai ince “halin rubutun kenan”. Amma ni na rubuta shi. Saidai ba lallai ne kullum marubuci yayiwa makaranci yadda yake so ba. Yadda rubutun yazo masa haka yake rubuta shi. Ba tareda tunanin zai yiwa makaranci dadi ba ko a’ah? Ga masu cewa sunan littafin bai dace da labarin ba, abinda nake nufi anan shine; Allah ya riga yayi ALKAWARIN Lanto zata auri Mu’azzam a BAYAN RAN Sageer. Wassalamu alaikum Maman Safah da Marwah ce…….! A BARI YA HUCE...-1 G urin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu. Akwai sanannen hadin kai tsakanin al'ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin. Duk da haka wannan bai hana al'ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba. Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21