Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

Gurin Gawa. Shi da Malam Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su, ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da 'ya'yansa marasa adadi da rashin tarbiyya ta ke yi. Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki suka billa Yakasai ta nan. Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne ginin siminti mai dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana da samari suna ta shige da ficen su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi hamzarin jan Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un har ta samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai. Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin sanyin jiki Mairo ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar gidan, Uwargidan Hajiya Habiba ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu. Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta ba, ta ce "Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba". Ta dukar da kai ta ce, "Gurin-Gawa". Habiba ta kalle ta sosai na 'yan dakikai, nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci gaba da tukin tuwonta. Cikin halin ko'in'kula ta ce "Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki ki gaishe mu? Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba, sai dai kullum mu tuka mu ba ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata ke?" Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce "Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin Alhajin ne". Sai da ta mula ta ce "Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa". Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar. Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce "Bude motar ki kwaso kayanki mana ki shiga da su?" Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce "A'a, mu dai jira Baffan". Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce "Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne, gidan ubanki ne". A ranta ta ce "Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa". Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji Abbas wadda ta ke kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci kwalliya kamar me? Tana yafe da wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce "Ah! Yau wace rana?" Ta yi murmushi, ta ce "Ladidi ke nan, kuna lafiya?" Ta sake kyabe bakin (ga alama al'adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda kwata-kwata ba ya mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce "Gidan namu ne bai ishe ki shiga ba da zaki tsaya a zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki, ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce mun wulakanta ki?" Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba, ta yi ciki sai ta danne zuciyarta ta bi ta a baya. Suna shiga Habiba ta ce "Ai na dauka tafiya ta yi babu sallama, saboda uban nata ba ya nan". Ta sake kyabe baki, ta ce "Can soro na ganta a tsaye, salon ta ja mana magana wajen Baba". Amarya Aunty Hajara ta yane labulenta jin cece kucensu, ta ce "Wa nake gani kamar 'yar gidan Hure?" Habiba ta ce "Ke ma dai kya fada, ai ni na dauka batan kai ta yo". Hajara ta saki labulenta tana cewa, "Allah Sarki! Alhajin yana kan hanya don nasan dai ba wajenmu kika zo ba". Mairo dai na tsaye tamkar mutum-mutumi. Tana mamakin rashin mutumci irin na matan Alhaji Abbas. Babban mamakinta daga Habiba har Hajara babu wadda ta ce ta shigo daki. Haka Ladidi ta shige dakinsu na 'yammata ba ta kara bi ta kan Mairo ba. Ta ci gaba da tsayuwa sororo! Wannan yaro ya shiga, wannan ya fita duk ba su santa ba. Wannan ita ce rayuwar da Innarta ta ke guje mata ke nan ta matan birni marasa karah da rayuwar kowa yai ta kansa, ko kuwa abin nan da Bahaushe ke cewa, kowa tasa ta fishshe shi. Sai ta jiyo muryar Alhajin yana gaisawa da su Dagaci, ta yi ajiyar zuciya. Sun dade suna magana tana jiyo tashin sautin Alhaji Abbas yana ta kiran Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ita ma sai hawayen ya zubo mata. Can anjima ya shigo dauke da jakar kayanta da kansa, nan ya ganta tsaye a tsakar gida tana share hawaye. Ya ce "Sannu kinji Mairo, sannu Allah Ya jikan Bedi da Hure, Allah Ya ba mu dangana mu kuma Ya kyautata namu karshen. Ya ya zaki tsaya a tsakar gida kamar ba gidanku ba? Shige mu je wajen Habiba". Ta bi shi a baya. Ya shiga dakin yana cewa, "Habiba 'yarki ta zo kin barta a tsakar gida, ko ba ki ganeta ba ne?" Daga can kuryar daki ta amsa "A'ah 'yar Hure dai, don sanda na ce da uwarta ta ba ni na hada da nawa na rike cewa ta yi ba ita ba mu. Sai yanzu da ta zama budurwa gab gidan miji zata zo min? Wato na tattara jeren dakina na yi mata kayan aure?" Ya yi murmushi, ya ce "Ina abin ya ke? Wannan jeren naki ko dari biyu bazan iya sayenshi ba, sai ka ce yau kika fara aurar da 'ya'ya? Cewa nake ‘ya’yan yayyaenki duk kekika aurar dasu batareda kin taba kayan jeren naki ba?" Ta fito tana daura kallabinta, ta ce "Can dai, akai gaba. Da din ma da na ce a bani rashin godiyar Allah ne, yanzu kuwa ni ma sun yi min yawa, neman kai nake da su". Ya nunawa Mairo kujera ya ce ta zauna, amma ita sai ta zame ta zauna akan leda tana gayar da Baban. Ya kwalawa Hajara kira ta shigo tana tambayar "Lafiya? Bashi na ci ban biya ba ne?" Ya ce "Duk ku zauna". Sannan ya maida walwalar da ke fuskarsa ya ce "Hajara, Habiba, kowacce ta amsa da "Na'am". Ya nuna Mairo wadda kanta ke sunkuye, ya ce "Wannan wace ce?" Suka ce "Mairo". Ya ce "To madallah, tunda kun santa, wane ne ubanta?" Suka ce "Bedi". Ya ce "Bedi wane ne a gare ni?" Suka ce "Yayanka ne". Ya ce "A yau babu Bedi, wadda kuke gaba da ita itama babu ita a duniyar, wato Hure. Sabida haka duk duniyar nan Mairo ba ta da inda zata je sai gidana, tunda ba aure aka yi mata ba, saboda haka ga amana nan a hannunku, ku rike ta yadda

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21