Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

daure yanzun nan mu tafi asibiti". Ta ce "Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai likitan da ya isa ya raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!" Ya ce "Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya saukar dashi tare da maganinsa ba". Ta ce "Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru…….." Cikin matsananciyar damuwa ya ce "Wane abu ne kike gudu Inna?" Ta ce "Zaman Mairo da Iyalan Abbas". Daga haka ta yi shiru. Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji Abbas, abin kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani boyayyen abun don yadda ba ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma. Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar ba ta taba zuwa ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin irin maganganun da Innan ke yi a kullum suna kara tayar mata da hankali. Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan gidan su ne. Ya dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya ba Junaidu. Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban dakin shan magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa Innan allura. Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata alhamis da daddare suna kwance ta ce "Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba, da na ce Junaidu YA AURE KI". Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce "Inna ke ko mai yasa kika yi wannan tunanin? Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani na daban ko ya ya game da shi a zuciyata. Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin wannan, sai mutunta juna". Inna ta yi murmushi ta ce "Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba ganin inda namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare na sunsunar takalmi, wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki gaskiya na hango miki abin da ke ba ki hango ba, cikin kwayar idon Junaidu. Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai cikin kwayar idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan, amma kina son Junaidu. Adadin soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa. To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce ba ki ambace shi ba? Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike ki da kauna ta gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun. Duk runtsi, duk wahala da tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki jira LOKACI ya fada miki……." Cikin gundura da zancen ta ce "Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki ce wai ya aure ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da ita? Ni kam gare ni har gobe Uncle Junaidu Yayana ne". Inna ta yi murmushi ta ce "Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina hango inda za a alkinta min ke". Ta ce (kamar ta yi kuka), "Ni dai don Allah Inna ki bari……..". Ta ce "Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki Junaidu na sonki, tun ba ki mallaki hankalin kanki ba". Ta yi narai-narai da fuska, ta ce "Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?" Ta ce "Na bari". Ashe karshen hirar tasu ke nan. Inna Hure ta tako da asubahi cikin dafa bango domin yin alwala, ta zo gittawa ta gefen da rijiyarsu ta ke, santsin cabalbalin gindin rijiyar ya kwashe ta ga kafafun babu karfi, ta zame ta baya sai ji kake cindummmm….! Ta fada rijiyar ita da butar da ke hannunta. Mairo wadda ba ta yi barci ba tun daren jiya, tana tunanin zancen Inna akan Uncle Junaidu, ta kasa yakice al'amarin a zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da fatan ina ma ace zancen Inna ya tabbata gaskiya? Uncle Junaidu ya so ta? Ita kuwa da wace irin sa'a zata yi a rayuwarta? A farkon shekatun karatunta ba ta tantance wane ne Junaid ba, sai da girma da hankali suka fara game mata jiki. Uncle Junaidu na daya daga cikin irin mazan da suka yi karanci a wannan zamanin. Ta fannin sura, halayya da kyawawan dabi'u. Ta kasance ma'abociyar karance-karancen littattafan nobels' na Turanci. Littattafan Shakespear, Wole Soyinka, Zainab Alkali, Abubakar Gimba, Ama Ata Aidoo da mabiyansu babu wanda bata karanta ba. A duk lokacin da ta ke karatun, takan rasa dalilin da yasa ta ke danganta al'amarin jaruman littafin da Uncle da ita kanta. Ba tasan dalilin da yasa a duk lokacin da aka ambaci managarcin mutum mai kyawun sura ta ke cewa cikin ranta, "Kaman Uncle Junaidu". Eh, Junaidu kyakkyawa ne, ma'abocin kwarjini, zati da kamala, wanda kwata-kwata bai dace da matsayin da yake kai ba, wato malamin makaranta. Saidai da yake ance (ra’ayi riga ne) Mutum ne da yasan mene ne 'dressing' wanda kuma kowanne irin kaya ke karbarsa, su dace da da zubin halittarsa. Kai kace don shikadai aka kirkiresu. Junaidu idan ya shigo waje dole kasan ya shigo, sabida kwarjininsa da cikar zati. Yana da fara'a amma yana da zucciya, abu kadan sai ya bata mishi rai, haka abu kadan zaka yi ya wanke laifinka nan take daga zuciyar shi. Ba ta san me yasa ba, komai Uncle ya yi burge ta yake koda kuwa ace fada ne yake mata. Ta sha tambayar kanta, anya za a samu mutum mai kirkin Junaidu? Ta taba ce da Nabilah matar duk da Uncle ya aura ta caba. Nabilah ta ce "Dalili?" Sai ta dauko mata littafin da ke boye a bayanta, GENDER STUDIES (wani bangare ne na sociology mai banbance jinsin maza da mata). Shafin da aka fasalta halittar maza masu gamsar da diya mace a shimfida, kuma irin mazan da matansu ba sa iya rabuwa da su komi wulakancin da zasu yi masu. Tana jan layi-bayan-layi tana fassarawa Nabilah. Ta kare tana murmushi, ta ce "Edactly Uncle ko?" Nabilah ta kama baki cikin mamaki, ita karance-karancen Maryam ya fara ba ta tsoro. Yadda ta nakalci harshen Turanci ko goyon Birtaniya dole ya sara mata. Ta ce "Ke

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21