Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

A Bari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kafarshi cikin rufaffen takalmi baki (cober) sumar kanshi kwance lub a kanshi, sai sheki yake. Eh, gaskiyar Ilu ne, yana yanayi da jinsin Larabawa sabida murdaddiyar suma ke gare shi irin tasu. Mamakinta da farin cikinta ya kasa boyuwa, bakinta ya kasa rufuwa. UNCLE JUNAIDU ne tsaye yau a kofar gidansu. Ta kai hannuwanta biyu ta rufe bakinta ta kasa cewa komi. Shi kuwa murmushi ya yi, murmushin nan nasa mai aji da tsada da ba kowa yake yimawa ba. Ta bude baki a hankali ta ce "Uncle…….." Sai kuma ta juya gida da gudu ta yayibo sabuwar tabarma ta shimfida masa a tsakar gidansu, Innar na ta tambayarta wane ne, amma ta kasa magana, ta komo ta ce "Inna debo ruwa mai sanyi, Inna Uncle Junaidu ne". Ta fita da gudu ta shigo da shi. Lokacin Inna ta debo ruwa cikin kwanon sha mai tsafta, mai sanyi daga randarsu. Ta tsugunna daga can gefe suna gaisawa da Uncle tana ta yi masa godiyar dawainiyar da Mairo ta gaya masu yana yi da ita. Cikin girmamawa ya dukar da kai yana cewa "Babu komai Goggo. Maryam kanwa ce a gare ni". Innar ta mike ta shige daki, ya dubi Mairo suka yi murmushi, sannan ta duka tana gayas da shi cikin ladabi. Sau tari tana jin nauyin Uncle Junaidu kasancewarsa malaminta, duk da shakuwa da amincin da ke tsakaninsu. Ya ce "Zuwa na yi na ji shin sau nawa kika yi bita a tsawon hutunki, ko kuwa tunda kika shigo gida kika jingine jakar shi ke nan?" Ta ce "Wallahi Uncle kullum da dare ina yin karatu, kuma ka tambayi Innata". Ya ce "Shi ne kuma ranar hutu kikayi tahowarki ko ki neme ni in gaisa da Baba?" Ta mike ta sa silifas tana cewa, "Jira ni in zaga gona in kira Baban, ya yi min shaida akan lokacin da na bata mishi ina nemanka". Dariya ta ba shi sosai, yarinyar ta kan burge shi haka ta ke 'frank' komai da ke zuciyarta fade ta ke iyakar gaskiyarta. Ya ce "Dawo zauna abunki, barshi ya dawo da kansa kada ki katse masa aiki. Na yarda kin neme ni ba ki ganni ba, don ni kaina nasan na koma gida da wuri sabida ciwon Sagir, abin da ban yarda ba shi ne, ba ki yi kewata ba Maryam, don ga ki nan kin yi kiba abinki. Ni kuwa dubi yadda duk nabi na rame sabida kewarki". Yana fada yana taba kashin wuyansa wai yana nuna mata ramar. Dariya ta yi, wadda ta fiddo jerarrun hakoranta farare kal, da siririyar wushiryarta. Ta ce "Allah Shi ne shaidana akan hakan. Babu ranar da zata fito ta fadi ban tunaka ba Uncle, ban kuma yi wa Inna da Baba tadinka ba. Idan ba ka yarda ba na kira Inna yanzu ka tambaye ta". Ya kama baki "Ke kuma haka kike da son a yi miki shaida Maryama? Tunda kin ce Allah Shi ne shaida ai kin gama magana. Na yi kewarki Maryama yadda ba kya zato, nayi-nayi in bari kwanaki biyun nan su cika ki koma makaranta in ganki a can na kasa. Ban san mai yasa kika shiga raina har haka ba". Kalamanshi sun yi mata tsauri, kuruciyarta ta fito a fili, cikin halin ko'in kula ta yi murmushi kawai ta ce "Ina Ilham? Wane irin ciwo ke damun Sagir?" Ya ce "Ilham tana gaishe ki. Ga aike ma ta ce na kawo miki". Ya zura hannu cikin aljihunshi ya fiddo wani abu kulle cikin leda. Ya mika mata ta amsa cikin jin dadi tana kuncewa, ya ce "Sagir sikila ce ke damunshi, tun yana yaro". Ta ce, "Ayya Allah Sarki, Allah Ya ba shi lafiya". Ga yadda ta lura Uncle na son 'yan uwansa kamar yadda ta ke son Yaya Habibu. Awarwaraye ne na silba sirara masu kyau guda shidda. Ta sanya a hannunta tana murmushi, ta ce "Ka ga Uncle sun yi min dai-dai, ka ce da Ilham na gode". Shi dai kallonta kawai yake yi, shi kadai yasan abin da yake sakawa a zuciyarsa. Ba ta kula ba ta ke shaida mishi jibi da kanta zata dawo makaranta. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, kansa dauke da kullin hatsi, kafadarsa rataye da fartanya da lauje, su duka biyun suka mike suka karbe shi suna yi mishi sannu da zuwa. Ya bi bakuwar fuskar da kallo cikin mamaki, kamin ya tanka Mairo ta ce "Baba Uncle Junaidu ne". Da sauri Malam Bedi ya mika masa hannu suka yi musabiha, sannan suka zauna a tabarmar da Mairo ta shimfidawa Junaidun suna kara gaisawa. Ya yaba kwarai da nutsuwar Uncle, haka kawai ya ji yaron ya shiga ransa. Ya yi masa godiya mai tarin yawa kan hidimar da Mairo ta gaya masu yana yi mata. Ya ce "Don Allah ka kula min da karatun Mairo ko bayan raina, na baka amanar Mairo a wannan makarantar, ba ta da kowa sai Allah, Ba don alkawarin da na daukarwa Habibu ba, da bazan barta ta je ba". Jikin Uncle ya yi sanyi matuka da kalaman Baban Mairo. Ya ce "Insha Allah Malam lafiya Maryama za ta gama karatunta ga dukkan alamu yarinya ce mai hazaka da nan gaba za a amfana da ita. Na dauki wannan amanar ta tsayawa akan karatunta iyakar karfina. Ku dinga yi mana addu'a". Ya ce "Addu'a ga 'ya'yan musulmi duka muna yinta kullum. Sai dai daga yau JUNAIDU kana cikin addu'ata ta safe da dare, har zuwa ranar da na daina numfashi". Uncle Junaidu bai bar kauyensu Mairo ba sai yamma lis. Ya tafi cike da tunanin Baban Mairo da tausayinsu. Bai san mai yasa yake jin tausayin Malam Bedin ba, bayan ba ya da hujja na yin haka, Tunda kuwa bai rasa ci ba, bai rasa sha ba, kai a fadin kauyen Gurin-Gawa ma yana daga cikin attajiran garin. Manomi ne mai zuciyar neman na kansa, bai dogara da kowa ba. Baya kuma nema a hannun kowa. To ko Maryaman yake tausayi sabida iyayenta dattijai ne? Bai sani ba, abin da ya sani kawai shi ne, yana kaunar Maryam da iyayenta. Wannan amanar kuwa da ya daukarwa Malam Bedi, yana rokon Allah Ya ba shi ikon rike ta. Litinin, Mairo ta yi shiri, tun da asubah Malam Bedi ya rakata tasha ya sata a mota sabida ta dage ita kadai zata dinga kai kanta tana dawo da kanta, don ta saukakawa Babanta. Kafin azahar tana cikin Minjibir, suka game da Nabilah suka gyare dakinsu suka durfafi karatu da kwarin gwiwar Uncle, da kulawarsa gare ta. A karshen zangon sai ga Maryam Bedi da sakamakon (5th position), wato ta biyar a ajinsu. Ga yadda Uncle dinta ya ce da ita, wannan alama ce mai nuna wata rana zata fi hakan. Haka nan ita kadai ce ta fito da (80%) a darasin da ta fi so (Ingilishi). Sai dai a cewar 'yan ajinsu, ba wani nan, sama da fadi ne Junaid ya yi mata, kasancewarta 'yar gaban goshinsa. Amma ina za a ce wannan bakauyar ta fi su iya Turanci daga zuwanta a zangon baya? Koma dai me ye, Maryama ba sune a gabanta ba, burinta ta cimma burinta na cika alkawarin da ta kaukarwa Yayanta Habibu. Kwanci tashi ba

Table of Contents

Chapters

21 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21