Chapter 18
Chapter 18
dai wallahi shegen karance-karancenki sai ya lalataki. Yanzu ina ke ina littafin 'yan jami'a? Tukunna ma ina kika samo shi?" Ta yi dariya cikin nishadi ta ce "A wurin Uncle na dauke rannan daya aikeni in kai mishi littattafi staff-room na ganshi cikin lokarsa shi ma bai sani ba na dauke". Nabilah ta ce "To wallahi ki bar karanta sociology za ki hauka ce". Maryam ta ce "Da Uncle bai hauka ce ba? Ya gaya mini digirinsa ya yi shi ne kan sociology. (With first-class honour) Nima insha Allahu abin da zan karanta kenan". Nabilah ta ce "Sai ki yi azama, me ake da abin da zai juyawa mutum tunaninsa zuwa na Yahudu da Nasara?" Ta ce "Eh, idan kin amince da abin da suke fada ba? Ni dai ina so tunda Uncle shi ya karanta". Nabilah ta kyabe baki ta ce "Kya karaci gulmarki dai, kina son mai abin kina cewa abin kike so". Ta bude baki cikin mamakin Nabilah, ta suri bokiti ta yi waje tana yi mata dariya, tana cewa, "Ku gama kumbiya-kumbiyar taku a yi candy mu zo Galadanchi mu kawo amarya….". Ta bi ta da duka ita kuwa ta falla da gudu. To sai ga shi yau Inna ta fadi wani abu kwatankwacin na Nabilah. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce a ranta "Shin ko dai Nabila da Inna gaskiya suka fada ne? I fall in lobe with Uncle Junaidu? Neman tabbacin hakan abu ne mai matukar wahala a kwawalwarta". Ta mike ta fito ganin shiru-shiru Inna ba ta dawo ba daga fita alwala har gari ya waye, gabanta ya soma bugawa da sauri da sauri, cikin matsananciyar faduwar gaba. Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa, babu Inna babu alamarta. Ta matsa kofar bayin ta kasa kunne babu motsin Inna. Cikin karfin hali da matsanancin firgici ta ce, "Inna kina ciki ne?" Shiru babu amsa, ta ce "Inna ki yi min gyaran murya idan ba za ki magana ba". Nan ma shiru, sai amsa kuwwar raunanniyar muryarta da ginin kasa ya dauka, ya dawo mata da abinta cikin kunnuwanta. A lokacin ne ta ankara da zanin da ke daure a jikin Inna wanda karfen guga ya makale ya yage. Ba ta son gasgata abin da kwakwalwarta ke son ankarar da ita. Ta matsa ga rijiyar ta leka jikinta babu inda ba ya kyarma. Kafafuwan Inna ta gani a sama, maganar motsi kuwa babu shi a tare da su. Sai ta yiwo waje da gudu tana ihu tana kururuwa a kawo mata agaji, kanta ko kallabi babu, kafarta babu takalmi, hawaye shabe-shabe a idanunta. Abinki da jama'ar kauye, ma'abota hadin kai da taimakon junansu, nan da nan gidan ya cika makil da dan Adam, makotansu da abokan arziki kowa yana ta Allahu Akbar! Hure Allah Sarki!! Nan da nan wasu samari majiya karfi suka hada doguwar igiya suka cilla, biyu suka kama hancin suka rike, daya ya bi ya dauko Hure suka fiddo su. Mairo ta daga ido ta ga wai yau Innarta ce wannan babu numfashi, ta tafi har abada ta barta. Innan da ta rage mata a duk fadin duniya, ita ma ta tafi. Sai ta fadi, wuni guda cur ba tasan inda kanta yake ba. *** F arkawa ta yi ta samu kanta a gidan makociyarsu Karime. A lokacin har an yi wa Innar sallah, an kai ta makwancinta. Mairo ta ja jiki ta takure wuri guda sai a lokacin kuka ya zo mata. Ta yi ta kuka kamar ranta zai fita. Karime na ba ta baki tana rarrashinta. Ta ce, "Wannan ba shi ne karshen rayuwarki ba Mairo. 'Ya'ya nawa ne iyayensu suka mutu tun a wurin haihuwarsu, kuma sun rayu? Ki godewa Allah da Ya nufe ki da tashi tare da su, kika san dadinsu. Ni kin ganni nan ban taba sanin uwata da ubana ba, cikina da wata biyar Babana ya rasu, lokacin haihuwata uwata ta rasu, amma gani nan da nawa 'ya'yan goma sha uku. Ina yi miki ta'aziyya Allah Ya jikan Hure, mutumiyar kirki, mai alheri". Mairo ba ta fasa kukanta ba, addu'a ta ke Allah Ya dauki ranta ita ma ta huta, maraici na uwa da uba ba karamin abu ba ne. Tunaninta shi ne, ina zata kuma samun mai kaunarta a duniya kamar iyayenta? Ina zata je? Da wa zata zauna? Mene ne amfanin sauran rayuwarta? Ba ta da kowa ba ta da komi sai Allah, domin ta fidda lissafin Habibu a zuciyarta. Ta samu kanta cikin kullatar Yaya Habibu, kullata mai tsanani. Ba ta ga ranar da haihuwarsa tai wa iyayensu ba. Karime ta shigo da dambun masara a kwano da ruwa a kofi, ta sa ta gaba lallai sai ta ci. Ta dauki loma ta kai bakinta tamkar mai taunar madaci, haka ta ke taunar abincin. Ta tsame hannunta tana sharce wasu dunkulallun hawaye da suka zubo mata. A lokacin ta tuna babban kuskurenta a rayuwa, ba ta yi wa Inna addu'a ba. Ta mike ta je ta dauro alwala ta zo waje mai tsabta a dakin Karime ta shimfida sallaya, ta suturce jikinta ta tayar da sallah. Tana sallah hawayenta ba su bar ambaliya ba. Da ta idar ta bude Alkur'ani mai Tsarki ta shiga karantawa Inna suratul Yasin da suratul Rahman ta rufe da (du'a'ul mutawaffa) tana addu'ar Ubangiji Ya yi mata masauki da aljannah. Ranar kwana uku da rasuwar Inna Hure ta tattaro duk ajiyarta kudin mota kawai ta barwa kanta, ta ba wa Karime aka yiwa Inna sadakar gumba, waina da kosai. Mijin Karime da Dagacin Gurin-Gawa suka zo suka same ta har dakin Karime suka fara da yi mata ta'aziyyah, sanan Dagaci ya ce sun zo ne su kai ta gidan kanin mahaifinta su damkata a hannunsa, wannan ita ce amanar da za su sauke. Hankalin Mairo ya tashi, zancen Inna ya dawo mata sabo tar! A kwanyarta, "Wata kila abin da nake gudu ne dole sai ya faru... Zaman Mairo da iyalan Abbas". Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta ki ba su amsa, Malam Tanimu ya ce "Hakuri za ki yi Mairo, mutuwa riga ce akan kowa, tafiyarki birni ya zama dole, domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan Abbas mutum ne mai ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da yakinin zai rike ki da amana tamkar mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure". Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana hada kayanta tana kuka. Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura karkashin gadon bononta. Ta tattara 'yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk zuwan da ya yi, da kudin motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta. Suka fito Karime ta datse dakin da kwado, tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen suka zubo. Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da salansa ba abin da kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida gwaruwar da kanta ke yi da jikin motar sabida rashin kyawun birjin
Table of Contents