Chapter 12
Chapter 12
"Ai na ga alama, wannan patient din taka akwai raki da saurin kuka. Na dauka dadi zaki ji da kika ga Uncle sai kuma ki kama kuka?" Mairo ta maida idanunta ta rufe tana murmushi. Ta nemi ciwon da jikinta ke yi ta rasa, sabida kasancewar Uncle Junaidu tare da ita. Suna magana a kanta shi da Madam Serah ta gaya mishi wannan macijiya ta dade tana sarar dalibai, anyi duk iya kokarin da za a yi don ganin an fitar da ita daga makarantar an rasa. Wani zubin sai a yi tsammanin ma ta mutu don sai a yi shekaru biyu ba a ji duriyarta ba. Amma yanzu kam za a daukaka zancen zuwa federal da yardar Allah za a fitar da ita. Ya ce "Maryama ta kumbura, ta yi biyun yadda ta ke". Ta yi murmushi ta ce "Jini ne babu isashshe a jikinta, wanda aka zuke tare da dafin amma already an tafi a sayo wanda za a sanya mata a asibitin Aminu Kano". Hankalin Uncle ya tashi, ya ce yana son ganin Doctor Nanah, ta ce tana ofis ka karisa. Ya samu Dr. Nanah a ofis cikin tashin hankali. Ta ce "Yaya dai Uncle Junaidu?" Ya ce "So nike ki debi jinina idan ya yi dai-dai ki sanyawa student dina". Ta ce "To bari in diba kadan a auna a gani". Ta zuka kadan a sirinji ta mikawa lab asisstant ta auna, ya nuna (negatibe), ga duk wasu gwaje-gwaje da akayi, sannan dukkansu a 0+. Ya kwanta ta debi leda biyu ta ce ya ci gaba da kwanciya ya huta. Ta ba nurse ta sanyawa Mairo ta dawo tana fada mishi irin abincin da zai ringa ci har zuwa kwana bakwai. Nan da nan labari ya watsu cikin FGGC cewa Uncle Junaid ya yi donating jini wa Maryam. A'ah, cece-kuce ya soma (round) zagaye makarantar musamman daga 'yan ajinsa da daman suna hankalce da su. Yara kanana da su amma sun iya gulma. 'Yan manyan aji kuwa masu yi masa asirtacciyar soyayyah, wadanda a da ba su san da Maryam din ba suka zo suna kallonta, duk ta takura ta rasa inda zata sa kanta, balle da ta lura har da masu yi mata mugun kallo. Ranar da ta dawo hostel Kausar kunyarta ta ke ji, ko ido ta kasa hadawa da ita. Daga baya da ta ga Maryam din ma ba ta damu ba harkar gabanta kawai ta keyi, sai ta zo bakin gadonta ta zauna ba ta ce komai ba. Nabilah ta shigo itama ta zauna a katifarta abin da ko da wasa ba su taba yi ba. Suka ce "Don Allah don Annabi Maryam ki yafe mana. Wallahi sharrin shaidan ne, kuma mun gode da sacrifice (sadaukar da kan) da kika yi mana. Muna rokonki daga yau mu zama daya a makarantar nan, wato mu zama mu uku cikin amana". Mairo ta yi murmushi ta ce "Babu komi, ni dama ban taba kullatarku ba, mamaki dai kuke ba ni. Amma shi ke nan, komi ya wuce". Daga ranar Maryam, Nabilah da Kausar ba a kara jin kansu ba. To sai kuma ciwon ciki ya kama Kausar, kullum ba ta iya barci, sai murkususu da kuka cikin dare, haka suke kwana tsaye a kanta har asubah sannan zata samu barci. Da suka ga abin ya fi karfinsu sai suka yi reporting ga hukumar makaranta. Aka dauki Kausar zuwa maternity inda aka gano kabar ciki ke damunta. Nan da nan aka yi hamzarin mikata gida, domin abin ya fi karfin asibitin makaranta. Suka koma kewar Kausar tare da yi mata addu'a, kullum, har lokacin jarabawa ya matso. Kokarin Uncle shi ne Maryam ta saki ranta ta yi abin kirki a jarrabawarta, amma ina! Tunanin Kausar da halin da ta ke ciki ya hanata zama lafiya. Ranar da suka soma jarrabawa suka dawo hostel sai suka ga babu ko allurar Kausar a dakin. Captain da Metron sun kwashe sun bai wa iyayenta. A gigice Mairo ta fita kafarta ko takalmi babu, kanta babu kallabi. Nabilah ma ta bi ta dakin Metron suna tambayarta yaushe aka kwashe kayan Kausar? Ta ce "Allah sarki, wannan yarinyar diyar Gwamnan Jos, ta rasu. Tun satin da ya wuce". Suka rushe da kuka, suka zube anan suna ta yi. Tsoron Allah Ya kara shigar Maryam da Nabilah. Tun daga ranar suka koma wasu irin sukuku, ba fuss ba ass. Shi kansa Uncle ya girgiza da mutuwar Kausar, ya yi ta lallashinsu yana ba su baki. Ya ce da Nabilah abin da yake ankarar da ita ke nan kan daukan duniya da zafi. Shi Ubangiji ba ruwansa da ko kai wane ne, dan wane ne, wane ne ubanka face ayyukanka kyawawa. Nabilah ta fi Maryam ramewa, ta fi ta gigicewa, domion dai ta fi ta shakuwa da Kausar. Sannan ta kara rungumar Maryam a matsayin 'yar uwarta don sai ta ke ganinta kamar Kausar. Aka yi jarrabawa aka kare, sai hutu sati mai zuwa. Sai dai fa daga Maryam har Nabilah kowacce cike ta ke da zullumin sakamakonta. Uncle ya yi fushi da Maryam sosai, domin ta dauko na talatin da takwas yayin da Nabilah ta dauko na arba'in. Ta kaskantar da kai ta dinga ba Uncle hakuri, ta tabbatar masa zango mai zuwa za ta dage ta yi abin da zai ji dadi. Mutuwar Kausar ke nukurkusarta har zuwa lokacin. Ranar hutu malam Bedi sammako ya yi domin hedimasta ya gaya masa tun ana saura kwana uku, don haka a kwanakin nan barcin da suka yi kalilan ne sabida dokin dawowar Mairo. Barin ma Inna Hure da shiga goma, fita goma sai ta siyo abin da zata ajiyewa Maironta. Tun daga kan goriba, kurna, goba, magarya, dinya da ire-irensu wadanda tasan Mairon na so babu wanda ba ta nemo ta ajiye mata ba. Duk sammakon Baban Mairo bai isa makarantar ba sai da aka soma dadewa. Mairo da Nabilah na zaune karkashin dalbejiya dukkaninsu cikin damuwa suke na rashin ganin kowa nasu. Nabilah ta ce "Da na san gidanku Maryam da na zo kamin na wuce Lagos hutu wurin Auntyna". Maryam ta jinjina kai ta ce "Ba zaki iya zuwa gidanmu ba, can ne cikin surkukin kauye, cikin Fanshekara". Nabilah ta ce "Don ba kisan yadda nake son zuwa kauye ba ne, idan kuma kin musanta hakan ki gaya min ki gani". Ta dauko biro da jotter tana jiran ta bakin Mairon. Mairo ta ce "Fanshekara, motar Gurin Gawa, idan an shiga Gurin Gawa, sai a tambayi gidan Malam Bedi kowa ya sani. Idan kuwa yara ne kika ce musu 'MAIRON HURE' da gudu za su rako ki". Duka Nabilah ta dauke cikin jotterta, wanda ke bayansu ma ba su san da tsayuwarshi ba shi ma ya dauke cikin kakkaifar kwakwalwarsa. "Lah, ga Babana nan!". Mairo ta fada cikin matsananciyar murna, kamin ta kwasa da gudu ta rungume Malam Bedi. Nabilah ta dago daga rubutun da ta ke ta bi bayan Mairo da kallo, sai ta hango ta rungume da wani yagulallen tsoho, sanye cikin yadin algarara, kanshi duk furfura. Ta ce a ranta, "Ya za a yi ace wannan ne ya haifi Mairo? Ya fi kama da kakanta fiye da babanta". Ba tasan cewa ba wai shekarun da ya yi
Table of Contents