Chapter 21
Chapter 21
gama abincin rana, kowa ya ci nasa amma banda ita, sai da ta gama gaba daya, bayanta ya amsa, kugunta ya rike, 'yan yatsunta suka shiga zafi da radadi sabida ba ta taba yin wanki irin wannan ba. Ta dawo daki ta kwanta, Habiba ta aiko dan autanta Hadi da filet din dafadukar shinkafa wadda duk ta bushe babu kuma alamun zata toshe mata dunkulalliyar yunwar da ke cinta. Ta gabatar da sallar azhar da la'asar a tare, sannan ta zauna tana cin shinkafar. Dai-dai lokacin Baba ya yi sallama ya shigo rike da kwanon samira, ya ce "Amshi nan Mairo ki kara, idan kuma kin koshi ki ajiye zuwa anjima kafin a gama na dare idan kinji yunwa sai ki ci". Cike da tausayin Baffanta mai son faranta mata, Mairo ta karbi kwanon samirar, hakan ya yi dai-dai da bayyanar Habiba a dakin tana huci kamar macijiya, ta ce "Wannan salon da zaka fito da shi bazan yi na'am da shi ba. Yazan bai wa yarinya abinci kamar yadda na baiwa kowa a gidan nan amma ka dauko naka ka kawo mata, cewa ta yi ba ta koshi ba, ko kuwa wani sabon kinibibin ne don a zage ni?" Ya ce "Idan ma kinibibin ne, ni ne mai kinibibin ba ita ba, tunda dai ni na dauko na kawo mata har inda ta ke, ba zuwa ta yi wajena ta roka ba". Ta sa hannu ta dauke na filet din, ta ce "Wallahi ba zata ci rabon mutum biyu ba, kai dai da ka zabi ka zauna da yunwar kai ta zama, amma na dauke wannan". Ko kulata bai yi ba, ya sa kai ya fice daga dakin, ta wani fannin kuma kunyar Mairon ya ji. Mairo ba ta saba ganin irin wannan rayuwar ta matan birni ba. Wadanda suka dauki miji, ba a bakin komai ba. A matsayinta na marubuciya 'articles' a take ta ji tana son yin rubutu akan mata irin Habiba da Hajara. Wannan ne ya tuna mata da mutum ma fi muhimmanci a gare ta a yanzu (Uncle Junaidu). Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, a take ta dauko full-scap da biro ta soma rubutun da tasan Uncle zai yaba da shi. A tsayin kwanaki ukun da ta yi gidan Baffanta, ta ga rashin mutumci da rashin darajja miji kala-kala wajen matan Baffanta. Sannan ta ga rashin tarbiyya da rashin mafadi wurin ‘ya’yan su, hart a soma yiwa kanta fatan kada Allah Ya sa ta yi aure a birni. Gara ta koma can Gurin-Gawa ta yi aurenta kada ita ma ta zamo daya daga cikin matan birni, wadanda ba su dauki mijinsu da 'yan uwansa a bakin komai ba. Wannan tunanin da ta yi, yasa ta yi murmushi. To idan ma auren zata yi wa zata aura? Babu wanda ya taba cewa yana sonta. Babu wanda ta taba gani ta ji tana so a duniya, ba ya ga iyayenta da Yaya Habibu. Wata irin faduwar gaba ta same ta, tare da jin wani dal-dal-dal a cikin kirjinta, gami da tashin da tsigar jikinta ta yi, duk a lokaci daya. A lokacin da zuciyarta ta ambato mata UNCLE JUNAIDU. Wani irin matsayi ne da shi mai GIRMA a zuciyarta, wanda a duk lokacin da tunninsa ya fado mata, ta ke tsintar kanta a cikin wannan yanayin. Mu biyo Mairo da Junaidunta a littafin na biyu, wanda tare suke da dan uwansa., Maman SAFAH da MARWAH ce…….! Ku nemi littafin FROM MY KITCHEN na HADIZA UMAR DOGON DAJI (Mrs. Jelani Aliyu) don samun kayatattun girke-girke na zamani dana gargajiya da suka sha banban da sauran littattafan girke-girken da kuka saba karantawa. Tuna sunan FROM MY KITCHEN (Daga Kichin Dina). An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels
Table of Contents