Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

hakan lahani ne ga lafiya da kwakwala….”. Na tuna nasihar Baba Sa’idu, don haka na yi kokarin mantawa da wannan tunanin kada ya zamomin lahani ga kwakwalwa. Sati biyu a tsakani sai ga Ya Faruk ba zato ba tsammani. Ai kuwa na kwashi murna ba ji ba gani, na rasa ina naka-saka ina naka-aje da shi don farin ciki, inda duk yasa kafa cikin gidan nan nake mayas da tawa, na like masa tamkar cingam. Shima cike yake da farin cikin ganina, ya kara kyau da tsayi, ga wani irin gogewa da yake yi, jikinshi ya koma irin na Iftihal, mai santsi da taushin gani. A dakin Inna Dubu muke, na kwanta lamo aikinsa, cikin karamar murya na ce, “Ya Faruk Iftihal ba ta baka sako ka bani ba?” Ya ce, “Ta bani mana, fara kawo salala!”. Murmushi na yi, “Salalar me kake so?” Ya ce, “Ki daina wannan son jikin kamar mage, musamman kwanciya a jikin maza, ba kowa ne na gari ba, wani maye ne wani dan iska ne…”. Ba ni kadai ba hatta Inna Dubu ta ji kunyar maganarsa. Ta ce, “La’ilaha illallahu!…..” Amma shi din ko a jikinsa, iyakar gaskiyar shi ya fada zuciyarshi sak! Cikin sanyin jiki na tashi daga jikinsa na koma can gefen Inna na takure, duk raina ya baci. Bai kara bi ta kaina ba ya jawo jakarsa ya bude ya fiddo damin littattafan yara (junior readers series) na Turanci guda hudu ya miko mini. (An African Night Entertainment, Akin Goes To School, Suger Girl, da The Boy Slave). “Ga shi in ji ta”. Ya kuma fiddo wani takalmi (cover) rufaffe baki mai tsinannen kyau cikin kwalinsa, shima ya turo mani duk in jita. Ya sanya hannu ya fiddo ‘yar takardar littafin memo ta sha zanen shudayen furanni, ita ma ya miko mani. Na bude cikin zumudi, ga abin da ta rubuta layi daya kacal. “Abu plz, come soon”. Shi kansa Ya Faruk ya lura duk dokin zuwansa da nake, ya sagar min da gwiwa, don kuwa tunda na kwashi shirgina na haura kafa na yi dakinmu bai kara jin duriyata a gidan ba. Da daddare ya saba ni nake kai mishi abinci har dakinsa, amma yau sai Zulkiflu ne ya kai masa, domin Inna Rakiyar da ta kwashe tuwon ta yi kiran duniyar nan na yi kamar ban ji ta ba. Ganin Zulkiflu ya kawo mai abinci, ya tabbatar Abu dai fushi take yi. Ya yi cilli da jaridar da yake karantawa ya miqe ya shigo cikin gidan har dakin Innata. A lokacin ina cin tuwo, sai kawai yasa hannu cikin tuwona yana ci, na lura cin nasa har da mugunta ne, domin kan na kai loma daya ya kai uku gunduma-gunduma, nan da nan ya cinye mun tuwon. Na tsame hannuna na koma gefe ina ta kumburi, sai ya fita ya dawo da roba da sabulu gami da ruwa a buta. Ya soma wanke min miyar kukar. Inna ta ce, “Mulki sai mai shi”. Ya ce, “Kwarai, wannan Princess Diana ce”. Ban san sanda na yi murmushi ba. Ya ce, “To ko ke fa? Baki ga yadda kika yi kyau ba, da wannan murmushin naki mai narka zuciya, da wannan fararen idanun naki irin na Princess Diana, da wannan yalolon gashin naki irin nata. Na rantse da za ta ganki sai ta ce ke kanwarta ce. Duk namijin da Allah ya ba shi ke a matsayin mata, ya yi mai baiwa da rabin addininsa. Ga dai kyau ga kyan hali, ga hankali da addini. Ga Alqur’ani a cikin kanki. Ga ki da daukar rayuwa da sauki ban san ki da zuciya ba. A kullum kina auna abubuwa a mizani na hankali, ki yi hukunci wanda ya dace, ban san yaushe kika koma bin son zuciya ba….” Na toshe mishi baki cikin dabara ya cire hannun yace, “Is o.k, mun shirya ko Abuna? Taso maza muje ki gaya mun abubuwan da kika gabatar da bana nan, da kuma shirye-shiryen ki na tafiya babbar makaranta. Duk ‘ya’yan kirki suna makaranta sai ke ‘yar gatan Innarta da Ya Faruq”. Ya juya ya fita, Inna na ta mamakin mu. Da gudu na juya na je na sako bantena, na dora doguwar riga a kai, na daura karamin hijabi, na bishi muka fita waje muka zauna a kan dakalin kofar gida. Garin babu hasken lantarki sai na farin wata na daren goma sha hudu. Taurari birjik sun mamaye sararin samaniyar Subhana, sun kara haskakata. Da yake bayan isha ne duk almajiran Malam sun shiga gari bara, don ba duka Malam ke iya ciyar dasu ba saboda yawansu. Na sanya hannu na lalubo ‘yar akwatuna daga cikin bantena, Ya Faruq na ba na ce, “Ga amana, ka ajiye min. Domin Baba Sa’idu ya ce kada in sake in bari Inna ta kyautar min da zobban nan, a nan gaba za suyi mun amfani”. Cikin mamaki Ya Faruq ya soma kiciniyar bude akwatun, wani haske da ya fito ya dallare mana idanu ba shiri ya mayar ya rufe, daga inda nake ina iya juyo irin bugun da zuciyarshi ta shiga yi da sauri da sauri. Ya sake budewa domin tabbatarwa ya fiddo daya yana juya shi a hannunsa, hasken wata da taurari na kara masa walkiya. Ya ce cikin shakakkiyar murya, “Shi…… Baba Sa’idun… ne ya baki wannan da kansa Abu?” Na ce, “Allah shine, nima da fari na ji tsoro. Amma ya ce kar in sake in bawa Inna, to ni kuma na gaji da boyon su kullum tare dasu nake barci, har bandaki dasu nake shiga, shi yasa na matsu ka dawo”. Ya ce, “To ai nima wannan ya fi karfin in ajje shi wurina ‘sapphire’ ne (shudin yakutu) komai na iya faruwa. Shima Baban ban da abinsa bai dace da ya baki wannan ba yanzu, haba! Sai dai in kai banki”. Na ce, “Banki kuma Ya Faruq, ba kuxi ake ajiyewa a banki ba?” Ya ce, “Wannan ya fi karfin kudi, ya fi karfin zinari da diamond. Ana ajiye (valuable goods) wato kaya masu daraja a banki”. Ya yi shiru cikin tunani mai zurfi, da alama kanshi ya yi zafi. Can ya ce, “Gaya mun irin hirarrakin da kuke da Baba Sa’idu?” Na gaya masa irin nasihohin da yake yi mun ne kadai a kan sallah, sai irin wulakancin da Inna na ke mishi. Na ce, “Abin yana damuna Ya Faruq, shin me yasa Inna ta tsani Baba Sa’idu ne? Me ya yi kullum yake cewa ta yafe mishi tana wulakanta shi?” Akwai alamun rudewa sosai a tare da Ya Faruq, ya rasa amsar da zai bani, daga bisani ya daure ya ce, “Ban san yaushe kika koyi sanya ido a kan abin da bai shafeki ba. Ba tare kika tashi kika gansu ba Abu? To ki bisu da yadda kika gansu, nima ban sani ba. A yanzu haka Farfesa ya turo ni ne da wani al’amari mai girma wanda ban san yadda zan yi in shawo kan Innarki ba, don Malam ba matsala bane sai ita din mai tsatstsauran ra’ayi sa rashin kaunar duk wani al’amari daya shafi Baba Sa’idu. Ya turo ni ne da zungureriyar wasika zuwa ga Malam da ita Inna, kan su bada ke in tafi dake, an samar muku

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29