Chapter 12
Chapter 12
ba. Ta sake ni bayan ta ja wani mikakken tsaki da wasu dunkulallun hawaye da suka biyo kumatunta, ta shige dakinta. Bammm! Ta danno kofa, muna ji bayan sakata da ta sanya har kuba tasa ta kara kulle dakin. Allah kadai ya san halin da take ciki a yau. Haka ya ci gaba da durkuson bai dago ba. Malam ya samu wuri ya zauna yace, “Sa’idu lokaci ya yi da kai da Rabi za ku fuskanci gaskiya, ku daina aiki da karya, lokaci ya yi da za ku fuskanci abin da ya dace, wannan rayuwar ina za ta kaimu? Meye amfaninta?” Ya dago ya dubeni yana murmushi. “Yanzu cikata in aike ta tukunna”. Baba Sa’idu ya cikani, ba tare da ya dago ya dubi Malam ba. Ya ce, “Maza Zaynabu-Abu a samowa Sa’idu ruwa a randar Inna Dubu”. Na ruga da gudu dakin Inna Dubu amma kamin in shiga sai da na rabe na share hawayen idanuna. Na ce, “Inna kawo sabon kwanon shan ki a bawa Baba Sa’idu ruwan randarki”. Ta ce, “Abulle ‘yar gidan Sa’idu, ko dai kema can Sokoton za ki bisu ne wajen Yayanki?” Na yi murmushi domin ta yi mun susa a inda ke min kaikayi, na ce, “Ai kema kin san Inna ba za ta bari ba. Tun yaushe Baba Sa’idu ke cewa in bishi muje Sokoto a sani a makarantar su Iftihal, in na fadawa Inna tasa ludayi ta bubbuge min baki”. Ko kamin na iso sun gama maganar Innana sun koma ta karatun Faruk da amfanin gonar Baba Sa’idu dake nan Gwarzo. Isowana duk suka maido hankulansu gareni suna min murmushin su mai cike da kauna. Tsakanin Malam da Baba Sa’idu na kasa tantance wanda ya fi kaunata, dukkaninsu abu daya nake gani cikin kwayar idanunsu tun ina jaririya. Na russuna na mika mishi ruwan randar Inna Dubu, garai-garai da shi, ga sanyi kamar na firinji, duk gidan shi muke sha, abin kamar karama, ruwan randar Innar Ya Faruk ya fi na randar kowa sanyi, gardi da ratsa zuciya. Don haka ne kowa ya zo cewa yake a debo mishi ruwan randar Inna babba, ban da Ya Faruk mai son na Inna Rabi. Ya kan ce shi ta fi mishi ta kowa sanyi, duk da a zahiri ba hakan bane, illa kasancewar shi wani mutum mai son faranta mata a koyaushe, da kokarinsa na gusar mata da bakin cikin dake damun zuciyarta, amma duka a banza, wai kirari a gidan kurame. Baba Sa’idu ya ce, “To Zaynabu ni za ni koma, yau ban kawo miki komai ba saboda nima tafiyar ban shirya mata ba. Na je taron ‘convocation ’ ne a nan cikin Jami’ar Bayero, na ga don me zan koma ban biyo ba tunda gani a cikin Kano?” Na ce, “Babu komai Baba Sa’idu, Allah ya kaika lafiya”. Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kamo hannuna ya ce, “To meye sakonki ga yayanki da su Aziza?” Na washe dukkan hakorana ina fara’a, don jin dadin ya tuna min da Ya Faruk wanda dama ke makale cikin raina. Na ruga da gudu dakin Inna Dubu inda na boye kullin (awara da yaji) da Innar ta soya dazu, kasancewar shi mai son ta. Haka kawai yake sayo waken suya (soya-bean) ya kawowa Inna Rabi ya ce tayi mishi Awara, ya yi ta ci yana dangwala yaji yana santi. Wani zubin ya kan ce, “Amma dai ana hadawa da kwai ko Inna?” Sai ta yi murmushi ta ce, “Eh, ana hadawa amma kwan wake”. Na dawo da gudu na kawo mishi, na ce, “Ka kai mishi wannan”. Bai damu da maikon da ya mamaye ledar ba ya karba ya sanya a aljihun farar sassalkar shaddar dake jikinshi da a kalla ta ba naira dubu talatin baya. Ya ce, “To ina na su Aziza?” Na sunkuyar da kai ina murmushi na ce, “Ai basu sanni ba, kuma su ‘yan gayu ne basa cin awara”. Daga shi har Malam dariya na basu. Ya ce, “Wa ya gaya miki haka? Kada in kara jin haka, dake dasu duka daya kuke, sai ma ke da kika fisu. Ke da kike da haddar Izfi talatin a cikin kanki, su ko ko izfi biyu basu haddace ba, wawaye ne kurum! In zan dawo zan kawo miki su suyi sati tare da ke, ki dinga koya musu irin karatun nan naki mai dadin sauraro, mai kira’ar ‘yan Aljannah (warshu), kin ji Zaynabu?” Na ce, “Na ji Baba Sa’idu. Allah ya kaika lafiya”. A ranar sai a dakin Inna Dubu na kwana, don Inna na har washegari ba ta bude kofar ba. Kayan abincin da Baba Sa’idu ya zo mana dasu su doya da dankali, da safe Inna Dubu ta kasa ta kaiwa kowacce kasonta kofar dakinta. Inna na bude kofa ta ci karo da tsarabar Baba Sa’idu, ni kuma ina gefe ina rubutuna a allo da ban samu jiya na yi ba saboda zuwan Baba Sa’idu. Sai gani na yi ta samu fanteka tana jida tana fita dasu tana kaiwa almajirai. Tana dawowa ta hango katon din taliya da na kayan shayi a gefe, suma ta kinkima ta je soro ta rabar. Daga matan gidan har ni babu wanda ya yi mamaki, kamar yadda babu wanda ya daga ido ya dube ta, don in da sabo mun saba ganin abin da ya fi haka. Akwai sanda ta zuba turamen Holland da ya kawo musu da sallah cikin masai, ta gidan gabadaya, ranar ne ta ga bacin ran Malam irin wanda ba ta taba gani ba, Inna Dubu ce ta gayamasa, yace, “Wannan almubazzaranci ne, kuma masu almubazzaranci iyalan shedan ne. In bazata daura ba to ta bayar, amma ba za ayi wannan almubazzaranci a gidansa ba”. A dan tsukin na dage da addu’ar Allah yasa in ci makarantar sakandiren da nake so wato GGSS Kabo, ba don komi ba sai don su Hafsisi ‘yar dakin Inna Dudu da Indo dake can aji biyu ‘yar dakin Inna Rakiya, mun shaku dasu sosai, musamman Hafsisi da take kusan tsarata, shekaru biyu kawai ta bani. A satin Ya Faruk ya zo, amma ba jimawa zai yi ba don basu yi hutu ba. Na rasa inda zan sa raina in tsaida murnar, haka shima. Yayo min saye-saye masu yawa har da sabuwar jakar makaranta da wata na’ura mai koyar da harshen Turanci. Na ce, “Ya Faruk ina ka sami kudi haka, kai da kake karatu?” Ya ce, “Karatun ma ai don ku nake yin shi Kyauta, haka komi nawa naku ne. Kada ki damu da wannan alawus din dalibai ne da ire-iren kudin da Farfesa yake bamu ni da Imran wanda ni bana bukatarsu, saboda ci da shana da makwancina duk a gidansa yake. Iyalin Farfesa mutane ne masu karamci da suka san hakkin dan adam, suna kyautata mani sosai, haka shima Abban komi bai banbanta ni da Imran”. Na tambaye shi ko wane ne haka? Ya ce, “Shine babban dan Farfesa tare suke karatun. Ya ce, “Imran mutum ne mai kirki da dadin mu’amala, yana da saukin kai kamar Farfesa, I would like you to meet him even once (zan so kwarai watarana ki hadu da shi ko da sau daya ne). In kika zauna da shi wuni daya, za ki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29