Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

bai juyowa ba ya saki wata irin ajiyar zuciya ya ce, “To ni yanzu Abba ya ce in zo in koya miki karatu, me kike so in je in ce masa? Baki da lafiya ko-ko bakya jin magana?” Da sauri na lalubi jallabiyana na zurma, na daura mayafin ta cikin wani irin dauri maras fasali, cikin dasasshiyar murya na ce, “Ka yi hakuri Ya Im, bani da lafiya ne”. Da sauri ya juyo ba tare da ya yi tunanin nasa sutturar ko ban sanya ba, ya tako da sauri ya zauna a gaban gadona. Ya kai hannu goshina, “me ya same ki?” Wani irin shock ya same ni ya kuma taso da lalurar da ke kwance lumus cikin jikina. Jikina ya soma kyarma tun daga kai har yatsar kafata mazari nake. Ai Imran ba yaro bane, na san ya fahimci halin da nake ciki, sai ya yi azamar janye hannunshi a goshina ya ja da baya. Ya yi murmushi ya ce, “Zaynabu gaya mun irin ciwon da ke damun ki in ji ko zan iya maganin shi. Nima bani da lafiya amma nawa bai yi tsanani kamar naki ba. Kuma ni ina kokari a kullum in fi karfin zuciyata, in hana mata abin da na san ba alkhairi bane a tare da ita, in ce mata a’a, wannan ba dai-dai bane, bana biye mata domin sharrin dake cikin ta Allah ya yi yawa da shi. Sai ta kai ka garin DANA SANI ta baro, ita ba abin da ya dame ta. In yi hakuri in dauki kaddara, in roki Allah ya kawo mun sauki cikin al’amarina. Ni Imran da kike gani a duk sanda na ji zuciya na neman rinjaya na cewa nake, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’ouun!” Wallahi sai na ji matsananciyar kunyar shi ta saukar mun, na kuma shiga maimaita “Innalillahi…..” a fili da zuciyata. Wata nutsuwa ta musamman ta same ni, komi nawa ya koma normal, na sunkuyar da kai kasa cike da burin ina ma a ce…. kasar za ta tsage da na shige na huta da kunyar Ya Im, amma shi bai damu ba. Sharewa ya yi ya bagarar ta hanyar yin zaman direshan a gabana bisa carpet, yayin da ni nake zaune a gefen gado na zubo fararen kafafuna kasa, na tokare gefe da gefena da hannaye na biyu. Imran ya sunkuyo ya leka fuskata muka hada ido, ya sakar mun lallausar murmushinsa cikin son ganin na saki jiki na daina jin kunyar tasa. Na sanya tafukana na rufe fuska ina murmushi. Ya ce, “ZAY-NA-B”. Yadda ya kirayi sunan sai da tsigar jikina gaba daya ya kara tashi, ban iya na amsa ba. Ya ce, “Maza sauke hannuwanki daga fuskarki, kada ki sa in taba su”. Da sauri na sauke amma har yanzu ban bari mun hada kwayar ido ba. Ya ce, “Na ce ki gaya mun ciwon da ke damun ki, a kalla idan ban baki maganin sa ba zan baki shawara a matsayina na babba wanda ya fi ki shekaru. Idan kin barshi a ranki kin ki fadi, mai yiwuwa ne ya ci gaba da cutar dake ba tare da kowa ya sani ba, wanda a karshe hakan zai iya zamowa illa ga lafiyarki”. Ya yi shiru yana mai kokarin son mu hada ido amma na ki. Na yi tunanin dukkanin maganganun shi a kan hanya suke, ba wadda babu gaskiya a ciki. Don in ban mance ba Baba Sa’idu ma ya sha gargadi na a kan barin sanya abu a rai illa ne ga lafiya da kwakwalwa. To amma ni kaina wallahi ba na ce ga hakikanin abin da ke damuna ba, abin ya fi karfin bayyanuwa, ya fi karfin kwatance, ya fi karfin duk kokarin harshe na ya fassara shi. Unxpressable feeling kadai zan iya kiran al’amarina. Wanda in ban da ni da zuciyata da kuma Ubangijin da ya assasa mani shi a ruhi da gangar jiki, babu wanda ya san iyakar sa. Abin da na sani kawai shine, “I need Imran! I need Imran!! I need Imran a tare dani”. To amma idan na fadi mishi ai kamar na zubar da mutuncin kaina ne, na zubar da tarbiyyar gidanmu, duk da ban san wannan abun mene ne ba? Na san ba abun kirki bane, haka ba abin alheri bane kamar yadda ya fada mani. Don haka na kasa magana, tunda na fara tunanina bai katse ni ba. Ya yi nacin ya yi juyin duniyar nan amma na ki magana har ya gaji ya zuba mun ido da alamun ranshi ya baci, duk kuma sai na ji babu dadi. Wasu hawaye suka zubo min na sanya bayan hannuna ina sharewa. Ya mike zai fita ba tare da ya ce dani komi ba, har ya kai bakin kofa ba tare da ya juyo ba, ban san sanda na samu kaina ina mai cewa cikin rishin kuka “Ka yi hakuri Ya Im, mara ta ce take ciwo!”. Ya juyo a hankalce ya dawo, hannayenshi duka biyu cikin aljihunshi, ya dube ni sosai, na nutsar da kaina kas, kamar in ce, “Wayyo Allah!” Ya fi mintuna biyar yana kallo na kamin ya ce, “Al’ada kike yi ne ko zaki yi Zaynab?’ Da wata muhimmiyar kunya da haushin kaina mai tsanani suka taso suka kara lullube ni ban san sanda na fashe da kuka ba, yau tozarcin duniya na gama jin shi a rayuwata, da wanne ido zan daga in kuma duban Ya Im? Na wulakanta kaina na tozarta kaina na yi abin kunya. Imran ya ce dani kamar cikin tsawa, “Ba tambayar ki nake ba za ki sakar min sauti sai kin tara mana mutane a ka?” Na hadiye kukan gaba daya ji kake “mukut”, sai hadiyar rai nake tare da fyace majina da bakin dankwalina. Ya sake maimaita tambayar sa, wannan karon babu alamun wasa cikin maganarshi. Jikina na karkarwa na ce da shi, “A’a, ban ma jima da gamawa ba”. Ya yi ajiyar zuciya ya sassauta murya ya ce, “To meye abin kuka? Daga na tambaye ki don in san maganin da ya dace in amso miki sai ki bare baki ki fasa min kuka a zaci ma wani mugun abu nake miki, yanzu idan su Azizah suka zo suka ga irin wannan kukan da kike kamar na fitar rai suka tambaye ki me za ki ce musu? Maza share hawayen nan ki mai da mood din ki, mu yi karatun tun ban sa kafar wando daya dake ba”. Na koma cikin nutsuwata, na share fuskata tas na dauko littafin na budo mishi aikin. Ya zauna gefena yana dubawa, ya ce, “An excellent handwriting! Zaynab haka kika iya rubutu?” Sai yanzu ne na yi murmushi, domin dai ni mutum ce mai son yin abin yabo a yaba mani, yana kara (encouraging) dina. Cikin dan lokaci Ya Im ya fahimtar dani abin da na kasa har ma da abin da ban sani ba, da dabarun cimma nasara a darasin ‘Physics’ da muke cin kwakwa a kan shi ni da su Azizah. Ji na yi in zamu kwana muna karatun ba zan gaji ba, don kuwa Imran ba dai hikimar koyarwa ba. Imran S. Bindawa cool ne, reserve! Ga wani lafiyayyen kamshi da ban taba jiba dake fita bakinsa (Albaan mouth-fresh) in yana magana.

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29