Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

ta sharewa ina fyace hancina da ya toshe don azaba, suka tabbatar ba za su ji kalma ko daya a bakina ba sai suka hakura suka kyale ni. Muka zo gindin bishiyar dalbejiya inda muke tsayawa Shehu direba ya zo ya dauke mu, shiru-shiru bai zo ba har dalibai suka fara karewa. Su Azizah suka kulu matuka, ni kuwa ta kaina nake da kuguna da ya rike kamar zai balle saboda durkuson da na yi na awoyi da dama. Sai misalin karfe uku na yamma sannan muka hango hancin motar Abba (Vanquish), muka shiga ware ido cike da mamakin yau Abba da kanshi ya zo daukar mu, to ina Shehun? Ashe dan duniyar ne ka janye da motar da Faruq a kujerar mai zaman banza. Suka saki baki suna kallon ikon Allah, don ni har zuwa lokacin kaina a durkushe yake, tunda na yi musu kallo daya ban sake dagowa ba. Ya daka mana tsawar da ta firgitamu ya ce, “Da Allah malamai za ku shigo ne ko kuwa mu juya ku kwana a makarantar, ruwan wa? ‘Yan kauye kawai kun saki manyan bakunan ku kuna kallon mutane kamar baku taba shiga mota ba a duniya…” Faruk ya katse shi da cewa, “Haba babban Yaya ayi musu a hankali man da me za su ji? Da yunwar dake damun su ko da shanya sun da aka yi kamar kayan wanki, ko-ko da fadan ka kamar barkono bayan basu suka kar zomon ba….?” Ya ja tsaki “Tsut-tsut!” Kamar ya ci kansa don bala’i. Mu dai tuni mun nabba’a a bayan mota babu wadda tai magana, ya fizgi motar da gudun ta mai kamar na tashi sama, kan ka ce meye wannan sai gamu a gida. Kamin mu fita Ya Faruq ya dubi Azizah ya ce, “Ya ya ne Azzy, na ga mutuniyar tawa ba yada take?” Azizah ta dan saki ranta ta jinjina kai ta ce, “Kai dai bari Ya Faruq, wani mugun malami ne Allah ya hadata da shi yau ya zane ta ya sata kneel down a cikin rana wajen awa daya wallahi”. Iftihal ta ce, “Kai ina jin ba zane ta ya yi ba, wankin kashi ya sa ta. Baki ji ba yana cewa ya za ta shigo mana aji tana warin kashi?’ Haushin su ya ishe ni na bude motar fit na fice kamar guguwa, Faruq yana danne dariyar sa ya ce, “Asshah! Abu bai yi dadi ba, galleliyar yarinya kamar Abu na a ce an sata wankin kashi?” Imran ya daga murya da karfi yadda zan jiyo yana cewa, “Ai madallah, kai madallah, wannan malami ya burgeni. Yanzu haka ba ta karatu sai SOYAYYAH! Ai ni wallahi ya yi min dai-dai, da zan ganshi da na sa Abba yasa an kara mai girma zuwa principal din F.G.C baki daya. Me ake da yaron da ba zai tsaya ya yi karatu ba? Kuma ku shiga taitayinku wallahi don gobe insha Allahu zan je na neme shi mu kulla abota, in ba shi izinin duk wadda ta ki tsayawa ta yi karatu ya ba ta aikin kashi….” Ni dai ban juyo ba sai kuka nake, sai Faruq dake ta shan dariya kamar me. Su Iftihal duk a kumbure suntum suka fito cikin dana-sanin da basu gaya musu ba. Wannan wulakancin da Imran ya yi mani, idan da zuciyata mai hankali ce da ya isa a ce ta saduda ta fidda shi a cikin ta da duk wani al’amari da ya shafe shi. Amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Tun daga lokacin ya daina kaf-kaf din da yake dani ya koma treating dina yadda yake horas da su Azizah. Duk wani wasa da shakuwa dake tsakaninmu ya janye shi, kullum sai fada kamar Babana. Kai ni ko Babana bai taba yi min bala’I da sababi irin na Imran ba, da abin da ya isa da wanda bai isa ba, haka takurar da yakewa su Azizah ya kara ninkata. Ya hana mu kallon talabijin balle kallon fina-finan India wai mun fara lalacewa. Su Azizah da basu san hawa ba basu san sauka ba mamakin su ya kasa boyuwa, suka kai karar shi wajen Abba kan ya takura mana ko music ya hana mu ji a radio wai duk a nan muke debo lalata. Ya sayo kasusuwan kira’ar Jabir ya rika sanyawa duk gidan. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na runtse idanuna da karfi, wani sanyi ya ratsa zuciyata tare da yin wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, amma na kasa bude idon. Babu shakka Ya Im ya yi min bazata, ya shammace ni ya kuma gigita ni. Na rasa da idanun da zan bude in dubi su Azizah. Wata irin kunya da nauyin su da ban taba ji ba suka taru suka yi min mayafi, na bushe a zaunen da nake. Su Iftihal kan su bushewar suka yi, kamar sassakakkun gumaka. Cikin mu babu wanda ya san fitar shi, sai bude ido mu kai muka ganmu a cikin mota, direba ya ja, ko uffan babu wadda ta yi kokarin cewa a cikinmu. Sai me? Mun fito break kenan muka ga motar Ya Im a kofar ofishin principal, aka aika in zo, wani irin kululuuu! Da cikina ya bayar ban san sanda na tsugunne a kasa ba na dafe cikina dake hargagi, ita kanta Iftihal a tsorace take, don dukkan mu munyi tsammanin karar Malaman mu ya kawo da Azizah ta ce suna bamu amsa. Na shiga na tarar ashe ba a nan gizo ke sakar ba, zuwa ya yi a kan makarantar ta yi mun iyaka da su GG da ke cewa suna so na, domin ni matar shi ce an daura mana aure tuntuni. In ka kalli fuskar nan mai bam sha’awa ta Ya Im, ta juye gaba daya da harbadadden kishi zuwa na wani mutum daban mai zuciya da razanarwa. Na yi hanzarin daga ido na dube shi, in tambaye shi dalilin shi na yi mun haka? Wata uwar harara da ya jefe ni da ita ba shiri na dukar da kaina kasa na mai da bakina na dinke na kasa cewa komai. Principal ya ba shi hakuri, ya kuma tabbatar mishi za a tsawatar don wannan dokar makaranta ce dama. Shi kuwa GG anyi neman duniya cikin makarantar ba a ganshi ba ya gudu, tunda ya ga motar Ya Im ya tsere don bai san yau da wacce ya zo ba. Na cika na yi famfam na fito ina hada hanya saboda takaici, wai me Imran ke nufi dani ne? Ya hana mun kurbar ruwa a duniya ko me? Saboda kawai ina zaman cin arziki a gidansu? Ya sanya ni cikin wani hali na matukar kunyar su Azizah, ban fita daga wannan ba ya zo ya lankaya min auren da Allah bai lankaya min ba. Inda na gode Allah daga Azizah har Iftihal babu wanda ta yi mun tambaya ko daya, domin dai su yara ne nutsattsu kuma wayayyu da basu faya mai da hankali a kan abin da bai shafe su ba. Na dawo gida ina ta fushi, da dare kowa yana falo amma ni na kasa fita, gani nake kamar su Azizah za su fadawa kowa abin da ke tsakanina da Yayan su, na ji ni duk na zama wata bare

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29