Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

mai shigowa sai dai ya amsa masa sallama ba tare da ya dago ba. Akwai aminci da mutunta juna na hakika tsakanin Ya Faruk da Rabi, ta yadda duk wata damuwar Faruk Rabi ta sani, komi nashi da ita yake shawara, haka duk wata ajiyar shi mai muhimmanci a dakinmu take, kai ba za ka ce kishiyar Mamansa ce ba. Halin dattaku irin na Ya Faruk daban yake da na kowa cikin gidan, yaro ne a zahiri, amma halinshi na manya ne, tun ina yarinya a ban san komi ba, na san Faruk kyakkyawa ne, dana kan karkace kai in bata lokaci ina ta kallon sa, shi din bai sani ba. Idan ya juyo muka hada ido sai ya ce, “Kyauta yaya ne kike kallo na?” Mai hazaka da mai da kai, kuma mai nasara a kan duk abin da yasa gaba. Faruk tun yana shekaru goma ya haddace Alkur’ani, haka har girmansa da shigar sa babbar makaranta bai daina zama yana daukar karatun buzu ba wajen Malam. Faruk ne mai taje min dogon gashina tun ina shekaru uku, ya kallabe shi kalba biyu, hagu da dama, shi yake zabar min kayan da zan sanya, ya kuma goya ni a bayan keken sa ya kai ni makaranta, in an tashi ya je ya dauko ni dai-dai da rana daya bai taba gazawa ba. In Innata na mun wanka, sai ya girka kujera ya zauna yana azalzalarta ta daina cudawa da karfi, fatar Abu bata da kwari, ba kya gani ja ce ne? Inna sai ta tsage jini ya fito? Rannan ya ce, “Inna Rabi daga yau kada ki sake yiwa Abu wanka ni zan dinga yi mata, don na lura wallahi da gayya kike cudawa da karfi, ba kya tausayin fatar Abuna”. Rabi ta yi dariya ta kira Malam ta ce ya raba wannan rigima ta Faruk. Malam ya ce, “Faruku namiji baya yiwa mace wanka ka yi hakuri. Daga yau babu mai kuma yiwa Zainabu-Abu wanka da soso”. Tun tasowata na san Innana Rabi na fama da wani bakin ciki na shekara da shekaru, wanda in har ya ciwo ta, takan shiga daki ta yi ta kuka. A irin wadannan lokutan, Faruk kadai ke iya tausarta da kwantar mata da hankali. Na kan gansu suna ta kus-kus, na ita damuwar da ke damun Inna Rabi, wadda yawan shekaru da yanayin rayuwa bai taimaka ba ko kankani wajen gusar mata da wannan damuwar ba. Ta kan ce da ni, “Kyauta rayuwa abin tsoro ce, haka zuciyar mutum sau tari makiyarshi ce. Ta kan umarce shi ga abin da ta san ba dai-dai bane kuma Allah ya yi hani da shi. Ki guje ma sharrin zuciya, kuma ki tsarkake zuciyar ki, daga sabon Allah komai kankantarsa. Ki nisanci ZINA, ki kiyaye al’aurarki, mutum da kike gani abin tsoro ne, musamman wanda kika taimakawa, dama kuma Annabi (S.A.W) ya ce, “Ka ji tsoron sharrin wanda ka kyautatamawa”. A wadannan shekarun, bana damuwa da irin wadannan kalaman nata, kamar yadda bana fahimtar komai a cikinsu, domin hankalin bai isheni ba. Abinda na sani ko kuma na fahimta kawai shine, Inna Rabi rayuwarta daban ce da ta sauran matan Malam, komi baya faranta mata. Haka mafificiyar kaunar da Malam ke gwada mata, bata burgeta. Tana da wani mummunan kullaci a kan mutane da al’amarinsu, haka gaba dayan rayuwarta cikin kunci take. Sau daya na taba ganin ta tayi dariya a tun tasowa ta, wato ranar da Faruk ya ce ba ta tausayin fatata. Kokarin Malam da Faruk a kullum shine farin cikin Rabi da farin cikina, amma hakan baya hanata zubar da hawaye a yawancin lokuta. Duk wata kulawa ta uwa da uba kusan in ce na same ta ne daga Ya Faruk, yana sona, yana kulawa dani tamkar ‘yar da ya tsugunna ya haifa. Haka nan komi nawa mai muhimmanci ne a awurin Faruk, shirme ne ko akasi. Ire-iren mutanen birni da ‘yan boko da kan zo wurin Malam, ba zan iya iyakance alhairan da nake samu daga garesu ba, kullum cikin sabbin kaya, kayan wasa, sabbin dinkuna, kayan zaki da kayan kwalam nake saboda farin jinin da Allah ya yi min. Wasu kuwa kan ce kyawuna ne yake sayo min farin jinin, kowa ya ganni sai ya tanka, ya kuma tambayi Malam game dani, don ko a farcen kafa bamu yi kama ba (komi nawa irin na mahaifiyata ne) tamkar ta yi kaki ta tofar. Amsar da Malam ke bayarwa a kullum shine, nayo Innata ne, wadda take Ba’abziniyar Niger. Ni kaina na san ni da Inna ta daban ne a cikin gidan, haka muke wal! Sai ka ce tocilan don haske a cikin jama’ar gidan, ko kuma ka ce wata ne a cikin taurari. Sai dai abin da yake matukar burge ni da rayuwar gidanmu shine, ba za ka taba ganin an nuna wariyar launin fata ba, da ni da su Indo da Hafsisi da su Dubu ke riko, duka su Inna Dubu sun dauke mu daya ne babu banbanci. Sai dai Malam da Ya Faruk a kullum, a komi kuma a ko’ina, su kan nuna nice ‘yar gaban goshinsu. Halin Innata da irin rayuwar ta kam ya riga ya zame min jiki, har baya damuna, ba ni kadai ba haka duk kishiyoyin ta babu mai nuna damuwa da yanayin rayuwar ta, don in da sabo sun saba. Sai ta wuni ba ta yi magana ba sai bin kowa da ido, haka kullum daren Allah cikin yi min nasihohi da tsoratarwa a kan ZINA take. Ni a lokacin ma ban san mene ne zinar ba, ban gama tantance ma’anar kalmar zinar ba. Abin da na fahimta kawai shine; zina wani abu ne da Innata ke matukar kyamata, kuma wani abu da Allah ya yi kakkausan hani da shi. Na alkawarta ma raina zan guje shi, kamar yadda take gargadina a kullum, zan nisanceshi, kamar yadda Allah ya yi hani da shi. Akwai sanda ta ce min, “Kyauta da ki yi zina, gara mun mutuwarki da rayuwarki”. Da hankali ya fara zuwa min sai na samu kaina a mai tambayar kaina, shin mene ne shi wannan zina, da Inna ke damuna da zancensa? Me ke damun Innana ne? Meye dalilinta na yi min hasiha kadai a kan zina? Shin zina shine kadai abin da Allah baya so? Tambayoyi ne da ke min yawo a kwanya, tun ina mitsitsiyata, suke neman tarwatsa min kwakwalwa tare da wargaza min tunani. Don haka ban san sanda na samu Ya Faruk a dakinsa ba dake a zaure, a wani maraice, hannuwana dafe da kaina dake neman tsagewa gida biyu saboda ciwon barin kai guda (migraine) da nake yawan fama da shi, sakamakon tarin tambayoyi da damuwoyin da na kimsawa raina, suke addabar kwakwalwata, suka kuma fi karfin shekaruna. Na damu kwarai da wannan al’amari da Innana ke damuna da shi. Na zauna a masangalin kujera kwaya daya tak dake dakin, na yi tagumi da hannuwa bibbiyu na rasa abin da ke min dadi. Ya Faruk ya aje jaridar da yake karantawa ya juyo ya zuba min ido sosai cikin nazari, “Kyauta meke damun ki? Na lura a ‘yan kwanakin nan ba kya cikin walwala, kina ta ramewa kamar kudin guzuri, akwai damuwa kwarai cikin kwayar idanunki,

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29