Chapter 20
Chapter 20
don haka ya hanzarta juyowa cike da mamaki ya dube ni, da na wulwula ledar da ya bani na maka masa, niyyata ta fasa mun wannan bakin dake tozartani, ta illata wannan halittar da ke jan zuciyata ga abin da yake goranta mun a kanshi. Amma sai ya yi saurin dukawa ledar ta wuce ta saman kanshi, kayan shafar da ke ciki kowanne ya yi nasa wuri. Na yi murmushi na ce, “Baka da abin da za ka bani Imran, kamar yadda baka da maganin da zai yi maganin ciwo na, don ‘yan mazan naka da kake tinkaho, bai yi isar da zai isar da jarababbiya kamana ba. Amma ka san ina da surar da in maza dari nake so a rana zan samu, kuma daga yau zan fara, Allah za ka yi nadamar wadannan kalaman da ka gaya min”. Na wuce shi nan dafe da lebban shi yana girgiza kai kamar kadangare yana mamaki na gasken-gaske amma ya kasa magana. Kan mu zo makaranta kiris ya rage in yi kuka a gaban su Azizah, amma na yi kokari na daure na cije ina ta kukan zuci. Hirarrakinsu ko daya ban tsoma baki ba, haka fuskana babu annuri. A cikin aji ana ta aiki, amma ni ban rubuta komai ba, ashe wai har aikin aji (class work) malamin ya bayar suka yi suka gama ni ban sani ba, na yi nisa a tunanin rashin mutuncin da Imran ya yi mani. Malamin yana bin kowa yana sa mishi hannu har ya zo kaina, ya ce, “Ke ina aikin naki?” Na yi firgigit na dube shi, a sannan ne Azizah da Iftihal dake bencin bayana suka shiga zungurina da nasu litattafan, na mika hannu ta karkashin bencin na karbo na fito masa da shi kamar daga jakata na fiddo. Kuskuren da na yi shine, duka biyun na hada masa wato na Azizah da na Iftihal na kuma ba shi ba tare da na duba ba. Ya karba yana dubawa duka biyun, ya daga murya ya ce da ‘yan ajin, “Wace ce Azizah Sa’idu?” Gaba daya aka nuna Azzy da ta yi tsuru-tsuru. Ya sake cewa, “Iftihal Sa’idu Bindawa?” Wata kabila Ngozi ta nuna Ifty. Ya nuna ni ya ce, “Wannan kuma fa ya sunan ta?” Aka ce da shi, “Zaynab Aliyu”. Ya ce, “To ku taso dukkan ku mu isa wurin principal, yau idan uban ku gwamna ne ya daure ni har sai igiya tai rara. Dabbobin banza ni za ku mai da shashasha! Na zo duniyar na kuma je makaranta tun kan ayi cikin uwarku balle ayi tunanin haife ta, shine za ku mai dani sakarai?” Su Azizah suka tsugunna a kasa suna ta ba shi hakuri har da hawayensu, don ba abin da suka tsana a rayuwarsu irin a kai su wurin shugabar makarantar a ce sun yi laifi, don ta san Baba Sa’idu farin sani a take za ta gaya masa. Ni ko ko gezau, don zuciyata ta riga ta kekashe da bakin cikin Imran da ya yiwa zuciyata katutu, don haka don an duke ni gani nake dukan ba zai shiga jikina ba ko da kuwa da bulalar karfe ne. Ya ga ni ban ba da hakuri ba, karewa ma wani gefen daban nake kallo kai ka ce ba dani ake case din ba, kuma dama shine (discipline master) din makarantar baki daya, kowa ya san Malam GG watu Garba Gumel a wurin mugunta babu na biyun shi duk fadin makarantar. Ya ce, “Su Azizah su koma su zauna, ni kuma in taso in biyo shi”. Ban yi musu ba na karkade rigata na bishi a baya, Iftihal ta biyo ni tana ta ba shi hakuri ya daka mata tsawa ya ce ta koma mazauninta, ya kuma sanya monitar ajin Suhaila ta yi mai gadinsu, idan suka fito ta kira shi a waya ta gaya masa. Tafi-tafi ina bin shi kamar jela, ina gayawa kaina na cancanci a hora ni, wauta ce tun farko ta hanani gane Imran ai ba tsarana bane da zan kallafa zuciyata a kansa, don haka kome GG da Imran suka yi min dai-dain su ne. Wani kazamin (student toilet) ya sani in wanke kana tafiya kana karo da busasshen kashi, zarni kuwa ba a magana. Hankalina ya tashi, na soma hawaye amma GG in ban da narka min zagi ba abin da yake. Cewa yake, “So nake in ga matsayin ubanki a garin nan, in tabbatar da cikar ki ‘yar masu kudi. Allah yasa ‘Yar Aduwa ne ya haife ki, da kike wannan bunkasar. Kin ganni nan duk kyawun mace da farar fatarta ba ta burgeni, ko da kuwa ta hurul-eeni ce. Ko dai ta yi karatu ko in bautar da ita, bautar da uwarta da ubanta basu taba yi mata ba. Ke ni ko a aljannah bana fatan Allah ya hadani da mace, ba don komi ba sai don cewa ita ba komi bace face fitina a doron kasa, balle irin ku masu narka-narkan…….sai ku lalata mutum in ba ana wulakanta ku ba….” Na daga idona a hanzarce da hawayena suka kafe karaf, na dubi GG din nan na ‘yan dakikai don ji nake kamar Imran ne yake gaya mun hakan. Ashe dalilin Ya Im kenan na wulakanta ni, kada in lalata shi? Dalilin shi kenan na gaya mun abin da zai bata mun rai in ji har abada bana son mu hada hanya? Sai na ji GG ya yi gaskiya, na shiga kada kai ina mai gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa. Na duka na soma ture busassun kashi da tsintsiya, da wani amai ya taho min gabagadi sai na kwararo shi a kafafun GG kore shar da shi kamar atini, don rabona da abinci tun na safiyar jiya. Ji nake kamar hanjina nake amayarwa. Ya daka tsalle ya yi gefe yana kara zagina, ya ce, “Wallahi ba amai ba ko hantarki za ki amayar sai kin wanke toilet din nan fes, kamar tuwo na ya fadi in dauka, in ya so gobe a sallameni daga aikin gwamnati. Wannan ba abun damuwa bane ina da makekiyar gonar gado a Gumel, sai in koma gida in cimma sana’ar Uwa da Uba watau (noma)”. Ya kira wasu dalibai da za su wuce ya ce su dauko mai kujera, ya girkata can gefe daga nesa ya zauna yasa hankici ya toshe hancinsa, lokaci guda kuma yana wanke kafarsa da ruwa a gwangwani da na kwararawa amai. Haka ba yadda na iya na zage na wanke toilets dai-dai har guda shida, na kuma kwashe busasshen kashi na zuba a dustbin, sannan ya sani a gaba muka nufo ajinmu. Lokacin karfe sha biyu da rabi na rana ya rage awa daya a tashi. Na dauka shi kenan GG zai kyale ni, amma me? Ina sa kai zan shiga ajin ya juyo ya dakatar dani ya ce, “Haka za ki shiga musu aji kina warin kashi? Koma ki shanya kanki a rana har sai warin ya gushe tukunna, kneel down”. Na koma cikin rana na zube gwiwoyina idanuna a rufe. Tsayin awa guda da rabi sannan aka kada kararrawar tashi. Su Azizah suka rugo da gudu suka rungume ni suna tattabani suna tambayar abin da ya yi mini, ban ce musu komi ba illa hawaye da nake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29