Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

hankalinta ya tashi saboda irin dukan da yake yiwa su Hassan kamar ba mai rai yake bugu ba, da kyar Mama ta yi waje dasu bayan sun bugu, ko ina a jikinsu ya amsa ya haye ya yi suntum. Ta mike ta fice, dakinta ta shige ta kulle amma ba ta je ko ina ba. Abba ya rantse ya yi rantsuwa da Allah, “Wanda duk ya sake ce da Abu BARAROJI a cikin gidan nan sai dai ya nemi wani Uban ba ni ba, kun ji ko ‘ya’yan iska?” A ranar Mama da ‘ya’yanta kamar sallah, Abba ya wulakanta Hajiya Sa’a da ‘ya’yanta, su Iftihal kamar a rungume Abba kan su ya fasu, su a dole Abba ya fi son su da su Rufa’i. Azizah har kwarya-kwaryar liyafa ta shirya, inda ‘yan dakin Hajiya Sa’a su kai kwanan bakin ciki da takaici. **** [7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: Ai jin haka Innana ta yi hanzarin zuwa ta kamo kofar dakinta ta bame da mukulli, wato (Iftihal ba za ta shigar mata daki ba). Ba don yarinya ba ce kuma ba ta kawo komi a ranta ba, da ta gane abin da Inna ta ke nufi. Sai Inna Rakiya ta dauki kayan hannunta ta ce, “Muna maraba da Iftihal Basakkwata”. Ni da ita muka yi dariya, yayin da na yi wata asirtacciyar ajiyar zuciya. Da alama Iftihal yarinya ce mai saurin sabo da kuma wayewar kai, gami da karbar rayuwa a duk inda ta tsinci kanta. Kafa ta nade tana cin gyada, tana bani labarin Aziza (twin- sister) dinta. Ba ta daddara ba ta sake kallon gefen da Inna take, ta ce, “Innar Abu sammun rogon nan da kike tsamewa, hadawa nake da gyadar”. Inna ko kallon ta ba ta yi ba, yayin da kirjina ya shiga luguden uku-uku. Tsoro na Allah tsoro na kada Iftihal da ta zo yau din nan ta fahimci cewa gabar da Innana ke yi da Babanta itama ya shafe ta. Idan rogon Innar ya amsa mata, to ita ma Innar ta amsa. Ta sake maimaita tambayar ta na Inna ta ba ta rogon. Budar bakinta sai cewa ta yi, “Ai ba ubanki ne ya saya ba!”. Na yi saurin kai hannuwa na dafe kai, cikin wasu hawaye da suka ciko idona. Inna Dubu ma ranta ya baci da wannan halayya ta Inna ta. Ta zo tana dibar rogon cikin roba tana cewa, “Bari ta ci kasona, ai ni mijina ne ya saya idan ita ba Ubanta ne ya saya ba!”. Tana fadi ne cikin dariya, domin gusar da damuwar da fuskar ‘yar yarinya Iftihal ta shiga. Watakila ba a taba yi mata irin wannan gwasalen ba a rayuwarta. Ta kawo rogon ta dangwarar mana, tana cewa da Iftihal, “Ke ci ki rabu da ita, ba ta jin Hausa sosai, ba ta fahimci me kike cewa ba”. Ta ce, “Abu ma ba ta jin Hausar? To wanne yare suke ji?” Ta ce, “Abu ta fita jin Hausa, ita faransanci take ji irin na kasarsu, ai kin sani ko?” ta ce, eh na sanshi, ana koya mana a makaranta, Abu ina ce ce kasar ku?” Na yi dan diri-diri na rashin sani, don kuwa ni ban san da wata kasa ba banda wannan da muke ciki. Inna Rakiya dake gefe ce ta ce da ita, “Niger!”. Malam da Baba Sa’idu ne suka shigo, suna hirarsu irin ta wadanda suka aminta da juna. A yau ban yi gigin yin tsallen taren Baba Sa’idu ba, kamar yadda na saba. Duk da kankantata na san ba abinda Innata ta tsana kamar ta ganni a jikin Baba Sa’idu, don haka na yi ma kaina alkawarin na daina, daga ranar da hakan ya janyowa Baba Sa’idu wulakancin da bai taba gani ba. Sai muka russuna mu duka muna gaishe su, ni ina gayar da Baba ne, Iftihal na gayar da Malam. Murmushin jin dadi ya bayyana a fatar bakin Baba Sa’idu, yayin da Malam ke ta tsokanar Iftihal da amaryarsa. Ya ce, “Yanzu-yanzu zai kwashe kayan dakin Rabi ya sanya ta, don ita ta tsufa ita ko gata nan sabuwa gar a leda”. Iftihal tana ta dariya, ta ce, “Baba Malam ka ce da Abu ta rakani in ga gari don in ba Aziza labari”. Malam ya ce, “Maza Abu sako takalmanki ki raka amaryata gidan gonar Babanta, ki kaita har gidan Halima da Safiya, ki gaya musu diyar Babanku ce”. Muna tafe tare da Iftihal tana ta yi min hira, wadda duk rabin maganarta Turanci ne ba duka nake fahimta ba, amma ita ta kasa gane hakan ta hutar da bakinta, ni dama tuntuni Allah bai dauran yawan magana ba. Da alama yarinya ce mai surutun tsiya, fadi ba a tambaye ka ba. Takaicin al’amarin Innata a kan Baba Sa’idu ke damuna, abin har ya wuce kansa ya shafi ‘ya’yan cikinsa? Rabona da su Iftihal tun suna kanana da suka zo da babarsu wadda abin mamaki ita suna shiri da Rabi, sabanin uwargidan da suke narka matsananciyar kiyayya. Shin har yanzu lokaci bai yi ba da ya kamata in san duk musababbin wannan? Tambayar da Iftihal ta jefo min ta sake jefa ni a cikin rudani, “Abu Innarki na da tabin hankali ne?” Nayi gaggawar juyowa na dube ta tamkar ta soka min mashi a kahon zuci, amma na kasa ba ta amsa, don ban san me zan ce mata ba. Gaskiya ne al’amuran Innata sun fi kama da na masu tabi hankali, kuma a yadda kowa yake biyar da ita a gidan, ba a dauke ta cikakkar mai hankali ba. Kishiyoyinta basa kishi da ita, basa takaicin duk gwasalen da take musu. Mijinta bai dauki yanayin rayuwarta da muhimmanci ba, balle har ya damu da hakan, binta kawai ake da yadda take so, don a zauna lafiya. To amma ni ba zan taba yarda da cewa da ake wai Innata na da tabin hankali ba, musamman in aka yi la’akari da irin kalaman da ke fita a bakinta na hankali da sanin yakamata ne. Illa in ce yanayin rayuwa ne ya mai da ta hakan, ya sanya ta daina kaunar kowanne dan adam sai mu da muka zame mata dole. Na kan tambayi kaina don me kiyayyar ta ya fi yawa a kan Baba Sa’idu? Me ya yi mata? Me yasa ta tsane shi fiye da kowa a duniya? Me yasa kome zai mata don ya faranta mata baya burgeta? Tunda nake ban taba ganin mutum mai kirki, karamci da mutuncin Baba Sa’idu ba, kamar yadda ban taba ganin mutum mai arzikinsa ba!. Na daga kai na yi duba ga Gidan Gonarsa makeken gaske, dabbobin dake ciki dukkaninsu farare ne sol. Girman gidan gonar kadai ya isa a gina gidaje biyar manya-manya, ba tare da kowanne ya gogi dan’uwansa ba. Ita kanta Iftihal sakin baki ta yi galala! Tana kallon Agwagin ruwa farare kal sama da dari na yawo a cikin tafki, fararen Tantabaru rainon Ingila na tashi daga wannan daki zuwa wancan. Fararen Babba-Da-Jaka dika-dika goye da ‘ya’yansu cikin jikkunansu, fararen Dawaki kosassu na ta haniniya tare da harba kafafunsu cikin koshin lafiya, fararen kaji (buloras) wadanda ba za su kidayu ba, haka kwaikwayen da suka sassaka mutum goma ba za su iya kwashe su a yini

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29