Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

daya ba. Idan ka nutsa cikin gidan gonar sosai fararen ragunan Sudan ne buka-buka masu manyan kahonni suma cikin fili guda. Wannan ba zai burgeka ba sai ka ga fararen Balbelun dake shawagi cikin wayar da aka zagaye su. Ga kuma Tinkiyoyi da ‘ya’yansu suma farare sol-sol kai ka ce kullum sai an yi musu wanka, sun fi guda dari cikin fili guda. A can wani katon fili ‘zebra’ ne (jakin dawa) guda uku manya-manya masu zanen fari da baki. Babban swimming-pool cike yake da fararen kifi (salmon) manya da kanana, kai ka ce a (Dambatta-Dam_ kake. Iftihal bakinta ya kasa rufo da mamakin wai na ce wannan duk na Babanta ne. Ta daga kai ta yi duba ga Dawisu korra sharr dake ta shawagin su bisa doguwar katangar ginin kai ka ce katangar gidan Zoo ce saboda tsayi. Sun zubo dogon bindinsu kasa, wasunsu kuwa sun bude shi cikin nuna baiwar kyau da Allah yai musu dai bai yiwa wata dabba ko wani tsuntsu a duniya ba. Ma’aikatan wajen sun tsinko mata kayan marmari nunannu, sun wanke sun zubo mata a cikin kwando a matsayinta na bakuwarmu da ba ta taba zuwa ba, kuma diya ga Baba Sa’idu. Amma ta kasa sha, extremely puzzled! Sai tambaya ta take wai Baba shekaru nawa ya kwashe yana assasa gidan gonar nan? Wannan ai ya fi karfin a kira shi gidan gona sai gidan Zoo! Na ce, “Kin taba ganin gidan Zoo da babu zaki babu damisa? An ce Baba tun yana sakandire ya fara assasa gidan gonar da ‘yan tsirarun dabbobin da Malam ya bashi, amma bata fara habaka ba sai dawowar shi karatu daga Turai”. Ta ce a sanyaye, “Amma Baba mai yasa bai taba gaya mana yana da wannan gidan gonar ba?” Na girgiza kai na ce, “Ba zan sani ba, mai yiwuwa yawan abubuwan da ke kansa su suka mantar da shi ga yin hakan. Don shima sai ya zo garin nan sau uku bai zo nan din ba, duk albashin ma’aikatan ta hannun Malam yake basu”. Akwai shuke-shuke na kayan marmari musamman guava, Roman, fasa-dabur, inibi, tuffa, lemun zaki, ayaba, cashew da abarba. Muka debi iyakar iyawarmu a leda, daga nan muka tafi gidan Yaya Halima. A nan muka yi sallar magariba muka ci abinci. Na yi zaton Iftihal ba za ta ci ba, musamman da yake tuwon dawa ne miyar kuka, amma ita ce mai cewa a karo har tana side hannu. Yaya Halima ta ba ta dakakken yajin daddawa mai dadi da ta ce tana so. A kan hanyar mu ta dawowa gida Iftihal tace, “Shin Abu mai yasa Innarki ba za ta bari Baba ya tafi dake ba a sanyamu makaranta daya kamar yadda Babba ke so ba? Muma mun gama firamare, JSS 1 za a kai mu. Kinga ga Ya Faruk ba za ki yi kewa ba, za ki ji dadin zama da Mamarmu, don tana sonki”. Na yi sauri na ce, “Innata ma na sona, Iftihal ba za ta amince ba”. Na yi gaba abina na barta a baya. A kwanaki biyun da muka yi tare da Iftihal mun shaku sosai. Wasu halayen ta ne guda biyu, suka sa ta shiga raina; batasan mene ne girman kai ba, kuma ba ta dauki kanta a bakin komai ba. Duk wanda ta ga Babanta na so tana girmama shi. Da za su tafi mun sha kuka, ta rantse ba za ta tafi ta barni ba a barta a nan mu zauna tare. Sai da Malam ya yi mata alkawarin in Allah ya yarda WATARANA Zaynabu-Abu gidansu za ta koma baki daya, sannan ta hakura suka tafi. Inna na daga gefe ta ce, “Me kake nufi da da wannan alkawarin? To kada Allah ya yarda! In ma wani mugun nufi ne kuke da shi a kaina da Zainabu, kaida Sa’idun naka, to Allah ya fiku. Bani da kowa sai shi, don haka da shi na dogara. Na kuma tabbata zai fiddani da Abu daga kutunguila da sharrin Sa’idu”. Muna bakin motar Baba Sa’idu yana kara yi mun nasiha a kan muhimmancin kula da sallah a kan lokacin ta. Ya ce, “Zaynabu in kika kyautata sallarki, dukkan aiyukanki za su kyutata. A kullum ki yi kokari ki fi karfin zuciyarki, kada ki yarda ta fi karfinki. Ki kiyaye wadannan tsokokin guda biyu ‘harshe da zuciya’. Idan kika iya musu za ki iya ma dukkan rayuwarki. Idan suka yi kyau, dukkan al’amuranki za su yi kyau. Ki ci gaba da yi ma Innarki biyayya, kada ki taba yarda da kallon da ake mata na cewa ita din ba ta da hankali. Idan akwai mai hankali a duniya to ita ce, tana da kirki tana da alhairi yanayin rayuwa ne ya maida ta hakan. Kada ki yarda da yin mu’amala ko yaya take da namijin da ba muharramin ki ba, har sai kin san kanki, har sai kin san ke din WACE CE? Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki kamar Innarki, ta fiya kullaci! Domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwalwa. Jeki gida Allah ya bamu alkhairi”. Na juya ina tafiya sannu-sannu, har na kai bakin kofar gida na sake juyowa, shima Baban bai shiga motar ba kallona yake. Na dawo da sauri, da na tuna ban yi masa addu’ar da na saba ba, na ce, “Baba Sa’idu Allah ya kaika lafiya”. Ya ce, “Amin Zayanabu, Allah yai miki albarka….”. Muna dagawa juna hannu ni da Iftihal direba ya ja suka tafi. Ban koma gida ba sai da na ga bacewar su cikin rairayi da kurar da ke bisa hanya. Dawawo ta kenan har zan shiga dakin Inna, amma jin muryar Malam yana ta fada yasa ni dakatawa ba don na so ba. “Kin dauka har yanzu Zaynabu yarinya ce ne? Irin abubuwan da kike nunawa Sa’idu a gabanta zai sanya ta sanya ma kanta ayar tambaya. Abu anyi shi ya wuce shekara da shekaru ya wuce amma kullum sabo kike mai da shi. Rabi kullum kina girma amma kina mai da kanki baya, idan don kin ga ba ta yin magana ne kike yi masa hakan a gabanta, ni na gaya miki wataran za ta tambaye ki dalilin haka, me za ki ce mata? Allah ma muna mishi laifin da ya fi wannan ya yafe mana, balle ke mutum dan adam? Wace ce ke da ba za ki yi afuwa ga wanda ya saba miki ba? Inda Allah baya yin afuwa a garemu, da tuni bai nade duniyar ba saboda dimbin sabon da ke cikin ta? Ina jiye miki ranar da ABU ZA TA JUYA MIKI BAYA A KAN SA’IDU, wannan a rubuce yake! Don haka ki sanyama ranki salama….” Na yi hanzarin juyawa na koma soro ina ta yarfe gumi da hawaye. Ni ZAINABU ABU wace irin rayuwa ce wannan? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi, ba’a yi musayen yawu a kaina ba. To ni din WACE CE? Kenan ba daya nake da sauran ‘ya’ya su Hafsisi ba, tunda kuwa ban taba jin an samu sabanin ra’ayi a kansu ba. Kai ba wanda yake zancensu cikin gidan, kowa ya bude baki ZAYNABU…. KYAUTA… ABU.. ... “Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki tamkar Innarki, domin

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29