Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

da ta gurbata a dalilin son zuciya irin nasa…” Da maganganun Inna na kwana ina taunawa ina cizawa, ina hurawa a cikin raina. Abubuwa da yawa na kasa fahimtarsu, I’m confused! Da maganganunta masu daure kai da caza hankali, illa na samu kaina a daukan ‘Diary’ dina na rubuta kalmar “MAINASARA KANGIWA” da wasu cikin kalamun ta da ban fahimta ba. Nake fatan duk ranar da Allah ya dawo da Ya Faruq zan sanya shi ya fidda ni duhun da ke cikin su. Hutuna na wannan karon a Gwarzo na ji dadin shi fiye da na ko yaushe, don muna tare da mutanena su Hafsisi. Ita Indo an sa mata rana da wani malamin su a can Kabon, ita ko sarkin rigima Hafsisi ta ki kula kowa wai ita Faruq take jira, shi kadai take so duk fadin duniyar nan, idan ba shi ba sai dai ta mutu ba ta yi aure ba. Na yi dariya har da fidda hawaye, na jinjina kai, na jinjina mata, don ni dai tunda nake da Ya Faruq dai-dai da rana daya ban taba jin ya ambaci wata ‘ya mace a duniya da sunan so ba, balle wata Hafsisi. Sanda muke aji hudu ne ma Azizah ta taba rubuta mishi leta wai tana son shi, in ta kare karatu ya gayawa Abba yana son auren ta. Tun lokacin ya kirata kamar abin arziki, ya kwakkwada mata mari ya ce kuma ba shi ba, ko wani daban ta sake cewa tana so sai ya gayawa Abba, in yaso a cire ta makarantar ayi mata auren da Shehu direba dai amma ba da shi ba. Tun daga lokacin ko da wasa Azizah ba ta kara shiga shirgin sa ba, shima kuma sai ya rage wasan da yake dasu duka. Na ce, “Hafsisi in za ki ji shawarata, ki samu wani mai sonki tsakani da Allah ki yi auren ki ya fiye miki alheri, don shi wannan Ya Faruq da kike gani ko zancen aure baya yi, kuma nan da shekaru biyu ma albarka ya dawo. Azizah ma bai karbeta ba balle ke?” Hafsisi ta kulu, ta kawon duka ta ce, “Me Azizar ta fini ban da Turancin banza, nima yanzu meye ban sani ba a Turacin?” Na ci gaba da dariyar da ta kara kular da ita, cikin zolaya na ce, “Turancin ma ba fa fiki ba”. (maganar da na zo ina dana sani da ban yi ta ba). Budar bakin Hafsisi sai cewa ta yi, “Ba wani nan, ai dama ba tun yau na san kin fi son su Azizah dani ba, saboda su masu kudi ne kuna samu a jikinsu kuna ci ke da Malam da Ya Faruq din naki. Duk kun ki mahaifarku kun je kun tare masu a gida saboda tsabar kwadayi. In dai don dan abin da ake ikirarin Malam ya yiwa Alhaji Sa’idu ne da yana karami, ai yanzu ya biya shi har da riba, tunda har Makkah ya kai shi sau ba iyaka. Kada dai kuke mantawa a kullum an ce, inda kwadayi…..” Ta murguda baki ta yi tafiyarta ta barni da baki bude. Maganganun Hafsisi sun haifar min da ciwon kai, na dade ina maimaita kalamanta a zuci. Babu shakk duk abin da ta fadi gaskiya ne, kuma kalamanta duk shigen na Innana ne. Sai na ji wasu dumammun hawayen tausayin kaina masu zafi sun digo a kan yatsun kafata. Mafari kenan da Hafsisi ta daina yi min magana, ta dauki gaba dani, ta shiga nuna kyashin ta dani muraran. Tun daga lokacin na ji Sokoto ta fice min a rai, na rika gudun cikar kwanakin hutuna. Na alkawartawa raina ko da na koma gidan Baba Sa’idu da na kare makaranta ko kwana daya ba zan kara ba zan dawo gida. Don haka a komawata wannan karon su Azizah sun ga sauyi da yawa, gaba daya na yi sanyi, na mai da kaina bare a cikinsu. Na daina amfani da kudin da Baba yake bamu sai dai in ajiye kawai. Shima don ina jin nauyinsa ne amma da na ce ya daina bani. Na rage cin abincin gidan, idan na ci da karfe biyu bana kuma ci sai dare, na daina karin kumallo, don a ganina duk hakan yana cikin kwadayin abin hannun su. Daga baya ma in an tashi daga makaranta sai na dinga shiga restaurant din makaranta in saya in ci, in mun dawo ba zan ci na gidan ba. (Na manta cewa shi kansa kudin da nake sayin ai daga aljihun Baban yake fitowa). Su Azizah dai na kallon ikon Allah sun rasa ta cewa, sai Iftihal ce rannan ta ce, “Anti-Abu dai ta zama waliyyah”. Ranar wata alhamis mun dawo daga makaranta, a harabar gidan muka tadda Hajiya ta yowa wata kyakkyawar budurwa rakiya, ga wasu ‘yammata uku suna takewa budurwar baya sun rike mata jaka, za ta yi shekaru ashirin da shida. Baka ce amma a goge take, ko ina a jikin nan nata sumul-sumul, ga sullubebiyar mota ta (end of discussion) baka sidik sai daukar ido take. Tsayawa fasalta sittirun da ke jikinta ma bata lokaci ne, sai jifa mu take da wani irin murmushinta kamar madara, da hakoranta kamar kankara. Ta yafito mu da hannu muka je ta kama hannunmu mu duka tana tambayar mu ya ya shirye-shiryen (WAEC). Mamaki ne ya kama mu na yadda akai ta sanmu har ta san jarabawa zamu yi. Hajiya ta shiga yi mata bayanin mu, wai wadannan Azizah ne da Iftihal (twin sisters) din Imran. Wannan kuma Abu ce kanwar Faruq. Ta ce, “Lah! Ke ce Abun Faruq Aliyu?’ Ta makale ni sosai a jikinta ta sake cewa, “Ina jin labarinki sosai a bakinshi, amma ban zaci haka kike da kyau ba kamar Baturiya. Dan’uwanki ya damu da ke sosai Zaynab, da wuya a zauna da shi bai yi zancen ki ba, ina taya ki murnar kasancewa ‘yar’uwa ga mutum irin Faruq Gwarzo”. Na lumshe ido wani dadi ya kashe ni. Kowa ya budi baki alheri yake fada a kan Ya Faruq, ban taba jin wanda ya aibata shi ba, dai-dai da rana daya. Haka duk wanda ya san shi in ya ganni zai ce ya sanni, Faruq yana yawan ambato na. wannan ne yasa har abada ban da mutum mai kimar Ya Faruq. Ta mikawa ta bayanta hannu ta miko mata jakarta, ta sanya hannu a ciki ta damtso kudi da ba ta san adadinsu ba, (American-Dollars) ta fito dasu tsurar su ta raba su gida uku, ta mika mana. Azizah uwar son kudi ta riga kowa amsa, har da mu aka rakata bakin motar ta, ta ja ta fita cikin wani irin ubansun tuki. Azizah ta buga tsalle ta yi cikin gida tana cewa, “Yanzu zan shirya in tafi canji, in Allah ya yarda sai na zama MAMI ABDULHADI”. Na samu kaina a maimaita sunan Mami Abdulhadi fiye da cikin carbi, na so in ji sunan a baya amma na rasa daga inda na ji shi. A dakinmu na ce da Iftihal “Wai ita wannan Mami wace ce?” Ta ce, “Baki san Adda Mami ba? Diyar Gwamnan Sokoto Abdulhadi Talata Mafara, budurwar Ya Im?” Wallahi ban san sanda na saki kudin da ke hannuna ba suka tarwatse a kasa, a take na

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29