Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

ko yanzu da manyan almajiran Malam su Lawal da Harisu suka tasa. Baba Sa’idu Malam ya dankawa alhakin nemawa Faruk gurbi a Jami’ar Ahmadu Bello, inda Faruk ya jima yana burin shiga, sai dai shi Farfesa so yake Faruk ya je UDUS don ya zauna kusa da shi, don haka ba tare da shawara da Faruk ba, a can Danfodiyon ya nema masa gurbi mai kyau, inda za ya karanci (computer-science). Dole Faruk ya koma gidan Farfesa kwata-kwata, sai bayan watanni uku-uku yake zuwa mana hutu. Na yi kewar Ya Faruk ba kadan ba, na yi kewar kulawa da kaunar sa, na yi kewar komai nashi, domin shi Yaya ne mai karamci da nuna kauna, mai muhimmanta zumunci da kyautata shi, mai gudun duk wani abu da zai zubar da mutuncina da na mahaifinmu. To amma ni kaina ina son ya yi karatun, kasancewar sa babban burin rayuwarshi. Ya kan ce yana so ya zamo mutun irin Baba Sa’idu, yana sha’awar duk wasu halayen shi banda abu daya, yana son ya zama mai hidima da iyayenmu da al’umma kwatankwacin Baba Sa’idu. Kwaikwayon halayen Alhaji Sa’idu dole ne ga duk wani mutum da ya san ciwon kansa, mutum ne wanda ilimi, daukaka, da duniyar da Allah ya ba shi basu sa ya manta alkhairin da wasu tsirarun mutane su kai mishi ba, he’s really a model! Kullum cikin hidima yake da Malam da almajiransa, da lafiyar shi, aljihunsa da karfinsa a gwamnati, amma ko kadan wannan baya burge Inna Rabi. Kai ni sai da na fara wayo ma na lura inda wanda Innana ta tsana da gani a duniya, take kuma kyamatar abin hannunshi, to Baba Sa’idu ne. Daga sanda ta ji rurin motarshi a kofar gida, kasancewar karar motar shi daban take da ta duk sauran motoci masu zuwa wurin Malam, domin ba ta da kwaramniya sai dai ka ji wani irin suuuuu! Kawai, to za ta shige dakinta ta bame da sakata, har ni ba ta kara nema na sai ya tafi, don ta san inda duk yake cikin garin to ina nanike da shi yana ta haba-haba dani. Yau da dare har mun kwanta na tuna ban saka kwankwalatin zuwan Baba Sa’idu a kofi ba. Sadaf-sadaf na sauko daga gadon, kada motsina ya tada ita. To amma duhun dare bai sa na ga kwankwalatin ba, don haka na kunna aci bal-bal na zarosu daga kasan gado. Abin takaici abin bakin ciki, sai na taras baki daya an hade min su wuri guda baki dayansu, bayan sun kusa karewa. Na tabbatar Inna ce da ta zo shara dazu ta sharo su daga kasan gadon ta hade su waje guda. Kenan wannan watan ban san takamaiman ranar zuwan BABA SA’IDU ba. Sai nasa kuka, ina yi ina karawa har da shessheka. Gunjin kukana ya ta da Inna Rabi, ta zuro fararen kafafunta kasa daga gadon ta ce, “Kyautar Allah me ya faru?’ Cikin kuka na ce “Bayan kece kika hade mun kwankwalatan ZUWAN BABA SA’IDU???”. Ta yi shiru na lokaci mai tsawo, na dauka zagina za ta yi ko ta rufeni da duka, ko me ta tuna? Sai ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, “Ki yi hakuri Kyauta, ban sani ba na hade miki, amma gobe ba zan kuma ba”. Muka koma barci, amma har garin Allah ya waye idanuna basu rintsa ba, zuciyata ba ta bar tukuki ba, haka ban bar yin nannauyar ajiyar zuciya ba, yadda na ga rana haka na ga dare, na kuma tabbata ita ma Innar ba ta yi baccin ba sai juyi a kan gado. Kwanaki biyar da yin hakan, ina durkushe a bakin ramin da na haka don wanke allona a ciki, misalin karfe biyar na yamma, allo na nake wankewa don shiga sabuwar sura. A gefe toka ce a cikin dan kokon ludayin duma da zan shafe allon da ita kamin in sake yarfa wani sabon rubutun. Ina diban ruwa daga cikin kwarya ina wanke allon a hankali tamkar mai wanke jariri, na tallabeshi da hannuna na hagu cike da tunanin Ya Faruk dake Sokoto, kowacce wainar yake toyawa? Na yi murmushi ni kadai a raina ina kwatanta Ya Faruk a cikin babbar makaranta, na tabbata nan ba da jimawa ba zai bada mamaki. Domin ko da nike yarinya kankanuwa ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu, na san samun maza irin Yayana, ba abu ne mai sauki ba. Faruk ko a cikin tsararrakin shi daban ne a komai, haka yake da aji na musamman, sannan jarumi ne ko ta yawan kunyaryakin da yake nomewa Malam, wanda aiki ne da almajirai goma majiya karfi ke yi. Shi ba wani mugun kyakkyawa bane amma namiji ne ta kowanne fanni, kuma baiwarwakin da Allah yai mishi suna da yawa, har ba zan iya lissafasu ba. Kasancewar shi da namiji guda daya amma Malam bai taba takaicin rashin ‘ya’ya ba. Ya kan ce, “Faruk daya ne tamkar da goma! Da haihuwar yuyuyu, gara daya kwakkwara, ta kowanne fanni yana alfahari da Umar-Faruk….!! Ban ji karar (horn) din mota ba ko kadan, nayi nisa a cikin tunanina, illa takun Baba Sa’idu na GIRMA da nutsuwa, da ya bakunci kunnuwana. Yana kwarara mana sallama da wankakkiyar muryarsa tamkar wani balaraben Madina, saboda yadda muryar shi ke fita tar-tar. Ita kanta Inna Rabi na san ba ta zaci zuwansa a wannan lokacin ba, kasancewar ranar Juma’a ce ba Asabar din karshen wata da ya saba zuwa ba, wannan tabbas ne, da tun kan ya shigo ta shige dakinta ta rufe. Da na wulwula allon na yar sai a kan gadon bayan Inna Rabi dake gefe tana barar gyadar miya, ji kake tim! Ba kuma tare da na san aika-aikar da na aikata ba na yi tsalle na rikeshi ina “Oyoyo Babana!” Mikewa daya Inna Rabi ta yi sai ji na yi tana fizgata tana cewa, “Gafara ki bawa mutane wuri”. Shi kuma cikin ladabi ya russuna rike dani tamau yana “Allah ya baku hakuri Inna, Inna Allah ya huci zuciyarku”. Ta ce, “Sakar min ‘yata na ce Sa’idu, na yi ma kama da wadanda kudi ke rudinsu, a yaudare su? Da zuciyar ba ta huce ba da na kawo yau ne?” Kanshi a duke, cikin tsananin girmamawa da kaskantar da kai, ya ce, “Bani da kudin da za na yaudareku dasu Inna!!! Har gobe ni almajirinku ne dake neman albarkarku, dake neman abin da za ya sanya a bakin salatinshi daga tukunyarku. Hakurin nan nake dada badawa, wanda har abada ba zan daina ba, ko da yawun bakina zai kare. Dukkanmu ‘yan Adam ne da bama sama da aikata KUSKURE, ‘yan adam ne da shaidan ya yi alkawarin janmu ga ba dai-dai ba, kamar yadda ya ja Ubanmu Annabi Adamu Alaihis Salamu. Amma da ya roki Ubangijinsa, sai ya yafe mishi bai barshi ya rafkana ba. To Ubangiji ma kenan yana afuwa a garemu balle ku mutane?” Ta fiddo fararen idanunta ta zube su a kanshi za ta fara lailayo ire-iren ashariyar da ta ke narka mishi kenan Malam ya shigo gidan rike da tazbaha yana ja, ya ce, “Subhanallahi! Rabi’atu meye haka? Me zan gani haka? Saketa mana, karyata za ku yi?” Ni kam sai kuka nake ganin Baba Sa’idu yana kuka, abinda ban taba gani

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29