Chapter 6
Chapter 6
fini. Azizah ce take tambayar Hajiya Azumi wai ni wace ce? Ta ce, “Anti-Abu kenan, Yayar ce Azizah”. Ta kyakkyabe baki kamar za ta yi kuka cike da kishi ta ce, “ita ma ‘yar ki ce?” Ta ce, “Yata ce mana”. Ta sake cewa, “To amma ai ita fara ce mai gashi irin na Indiyawa”. Ta tuntsire da dariya ta ce, “Ke kuma baka ce mai gashi irin na Katsinawa!”. *** Mafari kenan da sunan (Anti Abu) ya bini a bakin su Azizah har yau inda nake. Makarantarmu jeka-ka-dawo ce ta Gwamnatin Tarayya (Federal Govt. College). Alkawarin da Baba Sa’idu ya yiwa Rabi bai karya ba, a hutunmu na farko ko kwanaki biyu bamu yi da hutun ba ya hada mu da direba ya kaimu Gwarzo. Su Iftihal sun fini dokin zuwa Gwarzo, ba don komi ba sai don jin dadin zaman garin da ita Iftihal ta yi a zuwanta na farko, take kuma bai wa ‘yar’uwarta labari, musamman gidan gonar babansu. Inna ta ji dadin yadda ta ganni, har ta kasa boye mamakin ta. Ta ce, “Kyauta ke ce kuwa???” Ni kaina na san na yi kiba, haskena ya kara fitowa, nutsuwar nan da ta sanni da ita tana tare dani ba abinda ya canza ba kamar su Azizah ba, sai ma abinda ya karu. Na ji dadi da ba ta nuna wa su Azizah kyara a kan idona ba, illa dai dakinta ne ta kulle alamun ba za su shiga ba. A cikin kunne na na ji sanda tasa kara tana ture warin takalmin Iftihal da ban san ya a kai ya je kofar dakin ta ba, tana kunkuni tana cewa, “Allah kai mana tsari da ire-iren zuri’ar Sa’idu, ka kare Abuna daga dattin zina”. Gaskiya a zamana tsawon watanni uku kacal gidan Farfesa na yi hankali gami da wayewa fiye da nawa na da, don haka maganar Inna ta tsaya mun a rai. A kullum gidan gonar Baba muke wuni, can ake kai mana abinci. A lokacin su Hafsisi da Indo ma sun zo hutu daga Kabo, duk tare muke yawon. Kauyancinsu da gidadanci na baiwa Aziza matukar dariya, don komi suka gani a jikin su ko suka ji sun fada wanda basu sani ba sai sun tanka. Inna take tambaya ta Faruq kwana biyu bai zo ba. Na ce, “Nima tunda na je gidan ban ganshi ba, an ce karatun ne ya yi masu zafi, shi yana (attachement) ne a Abuja da (Federal Revanue) yayin da Imran ke yi da (Company SIWES) a Kaduna. Da zamu dawo aka hado mana tsarabar Gwarzo rankatakaf! Azizah mai son man shanu ce da madarar shanu sabuwar tatsa, wadda ba ta kai ga zama nono ba. Ita kuwa Iftihal ta fi son a ba ta korai da ludaya na duma masu zane mai kyau, duk haka Inna Dubu da Rakiya suka hado masu, daga Inna Rabi ko a sauka lafiya basu samu ba, sai Abunta ta hadawa shatara ta arziki, don haka cikin dabara na diba cikin tawa tsarabar data hadamin na basu na ce in ji ta, ko don wanke damuwar da Azizah ta shiga kan yadda Innar ta karbe su. Ita ko Iftihal ba ta ma kula da ita ba don ba ta dauke ta cikakkar mai hankali ba. Karfe takwas na daren ranar a Sokoto ta yi mana. A zamana gidan Baba Sa’idu abinda na lura na faruwa cikin gidan shine, Mama mace ce mai kishin jaraba, ita ko Hajiya Sa’a mulki da ganin kyashi ne cike da ranta, ba ta son Abban ya yiwa kowa wani abu sai ita sai ‘ya’yanta wadanda dukkaninsu maza ne su hudu, in ka dauke Imran da yake babba duk yara ne, fitinannu masu dan banzan raini. Kusan duk rabin albashin Farfesa a karatunsu yake karewa. Za ka yi mamaki in ka ji cewa yaro karami kaman Jauhar kudin makarantar shi naira dubu dari da hamsin ne (per-term), amma duk da haka ba ta gani, kullum idonta na kan na Hajiya Azumi da ‘ya’yanta guda uku, sai kuma ni da yanzu aka kara mata. Tun zuwana gidan suke damawa, kowacce tana haba-haba da miji don neman zama mowa. Shi ko Farfesa irin mugayen ‘yan bokon nan ne da biro da takarda ya fi komi muhimmanci a gare su. Ba shi da lokacin ire-iren gutsiri tsoman da ke faruwa a gidan, don haka ko da Hajiya Sa’a ta kawo mai korafin wai Azumi ta zuge ni in zauna a wurin ta, sai cewa ya yi, “Har nawa Abun take da za a zugata? Ki kyaleta ta zauna dasu tunda da su tafi sabawa, ko cikin maza kike so ta zauna?” Faram-faram ta tashi, tun daga ranar Hajiya Sa’a ta kulla ta dani, ‘ya’yanta Jauhar, Hassan da Rufa’i take gaya musu wai ni BARAROJI ce Buzayen Daji su daina zama kusa dani. Daga ranar fa suka diba wai Maman su Iftihal ta zo da Bararoji. In abinci suke ci na zo zan gifta sai Jauhar ya tsartar da miyau ya ce, “Tir! Me za ayi da kazame?” Tun abun baya damuna har na soma share hawaye, musamman ranar da Hassan ya kwararo amai da na wuce shi yana cin abinci. Iftihal ce ta gayawa Mama, ta yi mamaki sosai, ta yi ta lallashina ta ce in yi hakuri za ta fadawa Abba. Su ko su Azizah ganin kwana biyu Maman ba ta dauki wani mataki ba, su Jauhar kuma basu fasa abinda suke ba suma suka shaka. Da daddare an hadu ana cin abinci kaman yadda yake a al’adar gidan, Rufa’i ya faki idon Abba ya tofa mun miyau a cikin plate dina, Jauhar ko ya tsartar gefe, ya ce, “Hassan gaskiya da aka ce Bararoji babu wanda ya kai su kazanta, ka duba ka ga yadda take mixing mayonnaise da margerine cikin farar shinkafa”. Suka tintsire da dariya. Abban ya dube su suna ta dariya, ya ce cikin mamaki, “Ku kuma ina kuka samo Bararoji?” Duk suka yi tsit! Ya buga tebir da karfi ya kara maimaita tambayarsa, kowannen su mara ta cika fam da fitsari. Azizah ta yi kwafa ta ce, “Abba Hassan, Rufa’i da Jauhar ai BARAROJI suke ce da Anti Abu, in sun ganta su tsartar da miyau ko suyi aman abin da suka ci, in tana cin abinci su tofa miyau a ciki”. Farfesa jikinsa har tsuma yake, muryarsa na rawa ya ce, “Ai ban ga laifinsu ba, ga inda suka samu daurin gindi nan”. Ya nuna Hajiya Sa’a da ta sunkuyar da kai. Ya koma mazauninsa yana kaduwa kamar mazari kamin ya yi murmushi ya ce, “Sai ki nemi wani gidan kuwa, amma ba gidan Sa’idun Malam Ali ba!”. Ba ita kadai ba hatta Mama ta kadu da wannan hukuncin na Abba. Hajiya Sa’a saboda takaici ba ta san sanda ta ce, “Ban gane ba, Abu ta fimu iko da gidan nan kenan?” Ya girgiza kai don tabbatar mata tambayar ta ita ce amsar ta. Ta ce, “Aikin banza! Su da gidan ubansu? Ba Bararojin ba ce karya suke? Da dai ba a san asalin balbelar bane….” Kamin ta karasa ya soma kwallo da su Hassan a cikin falon, cewa yake, “Fice min a gida, Hajiya Sa’a, sai na neme ki”. Idanun Hajiya Sa’a suka firfito kuru-kuru,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29