Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

ki gaya min mana. Idan baki gaya min damuwar ki ba wa za ki gayamawa?” Na saki sassanyan numfashi na ce, “Ya Faruk idan na tambaye ka za ka gaya min gaskiya tsakanin ka da Allah?” Cikin mamaki ya ce, “Abu, na taba gaya miki abin da daga baya kika bincika kika taras ba haka bane?” Na girgiza kai da karfi, “Baka taba ba Ya Faruk, don haka na san yau din ma gaskiyar ce dai za ka gaya mini. Wani al’amari ne da ya shige mini duhu yake sa ni cikin tunani da neman sani”. Na yi shiru cikin duban yanayinsa da ya zubo kyawawan idanunsa masu sheki yana kallo na. Na sarda kai cikin kunya da matsanancin jin nauyin abin da zan fada, domin duk da ban san ma’anarsa ba, na san ba abu ne mai kyau ba, ba kuma abu ne da ake son a dinga fada ba. Bai nuna kosawa ba har sai da na bara don kaina, na ce, “Shin mene ne ZINA da a kullum Inna Rabi ke gargadi na a kanta?” Na tabbata bai zaci tambayar da zan yi mai ba kenan, mamaki karara ya bayyana a fuskarsa. Ya ce, “Ita Innar ce take miki fada a kan hakan? Ba ta san ke yarinya ce ba? Gaya min gaskiya dai ina kika san wannan kalmar?” Na ce, “Wallahi Allah Inna ce take fada”. Na sake dukar da kai na warware masa wa’azin Rabi gareni a kowanne dare. Na kare da cewa, “Na rasa gane me take nufi, na rasa gane illar shi wannan abu. A da abun baya damuna, amma yanzu ya dame ni. Ba ta bari na in yi barci kullum “Abu, kada ki yi zina”. Shin ZINA shine kadai alkaba’in da Allah ya yi hani da shi?” Ya Faruk ya sunkuyar da kai yana kallon yatsar kafarsa, cikin dabara ya dauke siraran hawayen da suka cika mishi ido. Ya dade bai dago ba, cikin nannauyan tunani. Ya dago bayan wasu mintuna, ni kuwa na tsattsare shi da ido, ya yi murmushi irin mai kwantar da hankali, kamin ya soma yi min magana cikin tattausar murya. “Zina ba shine kadai aikin haramun da Allah baya so ba, sai dai yana cikin su. Kin ga babban haramun shine “shirka”, amma Inna Rabi na miki gargadi a kan zina ne kasancewar ki ‘ya mace, babu wuya an yaudare ku a wannan fannin, kasancewar zuciyar ku (delicate) wato rarrauna ce. Ta san ba za ki yi shirka ba, kasancewar ki rainon musulmi, kin kuma tashi cikin musulunci. Amma za ki iya yin zina, wadda take zigar shaidan ce da rudin zuciya, mai kuma jefa ‘ya’yan da aka haifa ta hanyarta cikin wata irin wahalalliyar rayuwa da bakin ciki tabbatacce. Abin da ake nufi da zina shine, yin rayuwa irin ta ma’aurata alhalin babu aure tsakanin ki da shi wannan namijin. Zina babu wuya an aikatata, amma jin dadin dake cikinta na dan lokaci ne, bakin cikin dake cikinta da abin da take haifarwa har abada ba zai gushe ba. Kamar misali idan wani ya aure ki bayan kin aikata ita zinar a waje, har abada ba zai taba ganin kima da mutuncinki ba. Hatta Bature da ya kawo mana ita, ya kuma yi sanadiyyar yaduwar ta cikin al’ummar mu, a cikin philosophy ya kira ta ‘dynamic pleasure’, wato jin dadi mai wucewa ya barka da bakin ciki mara karshe. Kin ji dalilin da yasa Inna Rabi ke nusarsheki a kanta”. Na ce, “To Ya Faruk me zai sa take tunanin ni din zan aikata Zina? Tunda ita ba ta taba yin zina a rayuwarta ba. Gaba daya rayuwarta tun daga yarinta har girma, ta kare ta ne a cikin bautar aure. Na kuma sha jin Malam na cewa, ‘abin da iyaye suka yi a kuruciyarsu shi ‘ya’yansu suke maimaitawa, wato barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe…..” Ya yi hanzarin katseni ta hanyar girgiza kai da cewa, “A’a, zamani ne ya sauya Abu. ‘Ya’yan yanzu bama koyi da iyayenmu sai da Bature. Da muna koyi dasu da abubuwan da ke faruwa a yau basu faru ba. Kuma Da a yau ka haife shi ne amma halinsa a duniya yake daukar abinsa. Ki kiyaye nasihar Inna Rabi Abu”. To a haka rayuwarmu ke tafiya, cikin rufin asirin Allah da tarbiyya ta gari. Lokacin da Ya Faruk ya zana jarrabawar fita sakandire, lokacin ne ni kuma na zana ta kammala firamare wato (Gwarzo Special) da nake zuwa. Malam mutum mai hanyoyin ma’aikatan gwamnati da dama. Akwai wani almajirinsa wanda ya tashi a gidansa, a yanzun kuma yake Farfesa a Jami’ar Danfodio wato (UDUS). Asalin dangantakar Malam da Proffessor Sa’idu shine, an kawo mai shi almajiranci daga wani kauye a Katsina. Da Dagacin yankin Gwarzo ya nemi da a kai yara makaranta, a wancan lokacin babu waanda Malam ya tuna ya kuma yiwa sha’awar yin boko kamar (Sa’idu-Baki) yadda sauran almajirai ‘yan’uwansa ke kiran sa kenan saboda bakar annakiyar daudar shi. Ya fi kowa datti cikin almajiran, haka ya fi kowa kazanta, inda duk ya wuce warin dauda da zarnin fitsari kawai za ka ji, amma haka nan Malam ke son shi fiye da sauran almajiran, don a cewarsa; Sa’idu duk ya fisu hankali. Kullum ya je makarantar bokon ya dawo abincinshi na nan cikin kwano Rabi ta ajiye mishi, sai kuma yai mata ‘yan aike da ba a rasa ba. A yadda Ya Faruk ya gaya mini, Inna Rabi ma na son Sa’idu, kuma da yake yana da cutar (ulcer) sai ba ta wasa da abincinshi, ko ba ita ce da girki ba in Sa’idu bai samu abinci ba sai ta daura mai tukunya ko ta jika mai garin rogo ta zuba zuma a ciki ta ba shi, haka duk ‘yan tsummokaran yaran gidan da Malam ke riko in sun tsufa ba ta suke ta bawa Sa’idu. Da sallah kuwa babba da karama, sababbi take dinka mishi, haka in zai je kauyen su Bindawa za ta hada mishi tsarabar Gwarzo niki-niki ya kai wa Innarshi da kudin motar zuwa da dawowa. Shima in zai dawo duk tsarabarshi ta Katsina su Aya da sauransu duka na Inna Rabi ne, don haka a bakin jama’ar gidan, Sa’idu dan dakin Inna Rabi ne. To ilimin boko dai babu matsayin da baya kai mutum a rayuwa, don bayan sakandire gaba dayan karatun Sa’idu a waje ya yi shi da taimakon gwamnati da ke daukar dawainiyar karatun dalibai a wancan lokacin. Yau Sa’idu-Baki shine da matsayin V.C watau (Vice-Chancellor) Proffessor Sa’id Salisu Bindawa, na Jami’ar Danfodio baki daya. Kuma anyi sa’a shi Sa’idun irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da aka yi musu komi kankantar shi. Balle shi yana ganin Malam da Rabi, matsayin wani tsaninshi na duk abin da ya zama a rayuwar shi, tunda iyayen da suka haife shi kasa rike shi suka yi saboda talaucin su da rashin dogaro da kai, suka turo shi almajirancin da ya zame mishi gata ba tare da sun kara bi ta kan rayuwar shi ba, sai dai shi ya neme su. [7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: Sai ta sa kuka a hankali tana cewa, “Ni ban ce kada Abu ta yi karatu ba, amma duk makarantun Kano a

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29