Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

makaranta keda su Ifty. Amma sanin kanki ne wannan ba karamin aiki bane ya hada ni dashi, tunda shima ya buga ya kasa balle ni? Sannan Inna Rabi na ganin mutunci na fiyeda kowa, ina tsoron abinda zai zubar da wannan mutuncin, ya rana na kaunata a zuciyarta. Saidai na gamsu da hujjojin da ya bayar.” Daidai nan Malam ya karaso ya tadda mu, wani almajirin sa Matt ya rikon masa leda, da alama irin tsira da balanghiga gu da ya saba kawo mana ne duk dare, yana murmushi yace “yaya dai? Wa da ‘yar kanwar shi ana shawara ne?” Muka yi murmushi dukkanmu tare da sunkuyar da kai kasa. Yace “ku tashi mu shiga gida, bana son zama cikin hasken farin watannan, yana gadar da ciwo”. Muka mike muka shiga gidan gabadaya, shi da Malam suka shige turakar Mallam din, nikuma nayi daki na kwanta. Inna na bisa sallama tana ta sallah, wannan al’adarta ne na duk daren juma’ah kwana take sallah. Ta kan ce, “wanda ya bari du iya da Kyale-kyalenta ya rudest, ya manta da ambaton Allah da yawa ita tuba a gareshi, haqiqa yana cikin rafkanannu. Don haka nima ta koya min, har yabi jinin jikina. Sau tari na kan bita muyi ta yi, har sai kafafuna sun sare, yawun bakina ya bushe. A can dakin Malam me suka ce – me suka ce oho! Was he gari da asuba hi dai naga fuskar Malam babu annuri. Bayan yayi sallar asubah gari yayi Dan shaawa! Haka, misalin karfe shidda na safe ya shigo dakinmu. Inna na bisa sallaya tana lazumi har zuwa lokacin ba ta mike ba, ni kuma ina kwance bisa gado bayan da na ida sallah ban iya na koma ba. Na dai rufe ido ne kawai cike da tunanin al’amuran rayuwa masu rudarwa, su sanya zuciyar mutum cikin wani hali na rashin sanin tabbas da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya. Ba a rasa ci ba, ba a rasa sha ba, ba a rasa suttura ba amma zukatan al’umma babu dadi. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ke faruwa a cikin gidanmu. Da alama Malam bai san idanuna biyu ba. Ya ce, “Rabi’atu na zo miki da umarni ne ba yardarki nake nema ba. Ki yi duba izuwa rayuwarki, tun daga farkon ta har karshen ta cikin kunci take. Kina nufin a haka za ki kare ta? Wannan hukuncin da kika yanke na tsanar Sa’idu da al’amarinsa ba shi zai sa ba, ba kuma abin da zai rage sai dai ya kara dagula rayuwar Zaynabu. Ki yi hakuri ki ba shi ita ya sanya ta a makarantar, tunda BAKI FISHI IKO DA ITA BA! In kin dauki al’amuran rayuwa da sauki, watarana sai labari, za ki ga kamar ba a yi ba. Ke baki bar zuciyarki ta huta ba, ita yarinya kin hanata amfani da damar da Allah ya bata ta yin ilimi, wanda zai zamo gata ga rayuwar duk da ta tsinci kanta a gaba. Ya gaya mun hujjojinsa cikin takarda, kuma na gamsu. Ya yi alkawarin duk hutu Abu za ta zo nan tare da Faruku, in ta kare hutun sai a zo a tafi da ita. In kin sanyata a daki kin kulle me za ki yi mata itama me za ta yi miki? Ki duba ki ga duk tsararrakin ta sun wuce ta a karatu, shekarunta goma sha biyu, amma har yau ba ta fara sakandire ba sai yaushe? Sai shekarun karatun sun wuce mata? Su Hafsisi duk bana za su shiga aji uku na sakandire, amma ita ki kama kina mummukewa a daki haba Rabi! Ni mijinki ban ji dadin ki ba, abokan zamanki basu ji dadin ki ba, haka ‘yarki hakuri take da ke, duk da ta san babu wata uwa a duniya mai hali irin na tata uwar. Wannan kaunar da kike wa Abu wace iri ce tunda kuwa ita ba ta ganta ba? Wannan ba so bane, kwarar ta kike yi….. in gaya miki gaskiya in baki barta ta bishi ba za ta kullace ki, ko da ba ta gaya miki ba. Kuma IDAN NURATU CE BA HAKA ZA TA YI BA..…!!!.” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Wata irin rayuwa ya yi mai ban tausayi da rashin galihu, amma a komi Malam Ali da mai dakinsa sun tsaya mishi. Ko taron iyaye da ake yi a makaranta Malam ne yake wanke kafa ya je a matsayin mahaifinshi da ya rasu tun bai yi nisa da karatun ba. Haka ranar taron iyayen yara Rabi ke shan lullubi ta je matsayin mahaifiyar shi, duk da idan ka dube ta za ka san a haife ba ta haife shi ba. Don haka a girman Sa’idu, da ci gaban da aya samu a rayuwa, baya da kamar Malam da Inna Rabi. Ka’ida ne duk karshen wata ya zo duba su, ya cika su da abin arziki kamar don su kadai yake nema, baya ga tarin iyalin da yake da shi a can Sokoto. Na taso cike da dokin, ranar zuwan BABA SA’IDU, wadda a kullum take lissafe cikin kaina. Ba don komai ba sai don na san ranar duk da ya zo, to ni ranar take sallah. Sabbin dinkuna da kayan ‘ya’yan gayu da yake kawo mini kamar shago za a bude mini, cakulet da biskit kamar (super-market) din su gare shi, don haka duk hakorana suka cinye da zaki suka gwaigwaye kamin in soma famfara, sabbin littattafai da sabbin uniform wannan duk wata ne sai ya sake mini, don haka nake daban a cikin yaran gidan dama garin Gwarzo baki daya, babu ‘yar gata kuma ‘yar gayu kama na. Ga kuma kyawun sura. Ribbon kuwa Baba Sa’idu dozin-dozin yake saya mani kala daban-daban. Ya Faruk ya zauna ya jera min su reras a kaina, in zamo kamar wata ‘yar Turawa, sai ka rantse da Allah Baba Sa’idu bai san ciwon kudinsa ba in dai a kaina ne. Allah ne ya hada jininmu da wata irin kakkarfar kauna, sai dai babban abin da ke bani mamaki, yake kuma sanyaya min jiki shine, duk wannan hidimar da Baba Sa’idu ke min, ko kadan baya burge Rabi, haka ko sau daya koda wasa bata taba sanya hannu ta taba kayan da suka fito daga hannun Baba Sa’idu ba. Kwankwalatin lemu ne da ni guda talatin, a karkashin gadon Rabi me fameka, kullum sai in ciri daya in jefa a kofi, ranar da suka kare kenan ita ce ranar zuwan Baba Sa’idu. In ina wannan kirgen, Rabi kallona take kawai, sai dai ba ta magana, na san tsabar takaicina ke hana ta magana. A raina sai in ce, “Inna ai ke rayuwarki sai ke, tunda Malam da Ya Faruk ma basa burgeki, shi Baba Sa’idu wane ne da zai maki gwaninta?” Ni dai haka nan nake son Baba Sa’idu saboda kirkinsa, saukin kai da haibarsa, ba shi da girman kai ko kadan, haka yadda yake sonmu ni da Ya Faruk yake kuma janmu a jiki, ko ‘ya’yan cikinsa basa samun hakan. Tun karatun sakandire ya so ya dauki Ya Faruk ya koma gidansa ya yi karatu a can Sokoto, Ya Faruk ya ki don a lokacin babu wani babban da namiji a gidan kusa da Malam sai shi, sai

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29