Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Girma Ya Fadi Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Sai nake tambayar kaina dama akwai wadanda Allah ya halitta da kamshin baki ne? Ko da yake in ban manta ba ai Iftihal ta ce Yayanta daban yake a cikin al’umma. A haka su Azizah suka shigo kwanciya suka tadda mu, karfe goma sha daya da rabi na dare, don su tuni har sun yi barci a falon taso su aka yi. Suka saki baki galala! Suna kallon mu don basu zaci har lokacin yana nan ba. To shi kuma sai ya bi duk ya daure fuska, ya buga musu tsawa ya ce duk su dauko nasu littafin. A take kowacce ta shiga taitayinta barci ya nemi inda ya fito. Karatu ya dawo sabo, ya hadamu gaba daya yana koya mana, bai kyale mu ba sai da ya tabbatar mun gane, ya bamu aiki muka gwada mai a kan idonshi ya gani, sannan ya fita ya ja mana kofa, ko kallon mu bai kara yi ba. Azizah tana ta korafin ita dai da Abba bai ce Imran ya koya min karatu ba, gashi nan yanzu ya jawo mana masifa sai ya mai damu wasu alhuda-huda, su kam sun shiga uku kenan. Iftihal dake ta fi kowa son Ya Im cikin gidan ta ce, “Ai ba zama zai yi ba, baki ji Abba ya samo masu aiki ba? Yanzu haka next week in ya tafi duk da fadan shi ke da kanki za ki yi kewar shi”. Sai na ji duk hankalina ya tashi, Imran zai tafi aiki, ina? Ni kuma ina zan sanya rayuwata? Kasancewana tare da shi a yau na wani lokaci mai tsawo, ya kawo sauki 50% cikin ciwon zuciya da gangar jikina, ya wanke wani babban kaso na ciwon shi dake damuna, ya kuma kara gina wani makeken al’amarin da ya wuce na jin shi a gangar jiki kadai, maimakon haka, sai ya shigo har cikin bargo da kasusuwana. Ni kaina na san yau idan na ce idanuwana sun ga barci, to wannan karya ne. cikin kowanne juyina IMRAN ne, cikin kowanne kiftawar ido IMRAN ne, cikin kowanne zama da tashi IMRAN ne, cikin kowanne kwanciya da mikewar kafa IMRAN ne, cikin kowanne mafarki da ido biyuna shi din ne dai kadai ya mamaye, ya babbake yayi babakere a ko ina, bai barni da ko sako daya da zan sanya tunanin kaina ba. Da safe na sanya (uniform) dina cikin sauri ne saboda makarar da na yi, su Azizah tuni sun gama suna diniing suna karyawa, wannan ya samo asali ne da rashin isasshen barcin da na samu daren jiya, bayan sallar asubahi kuma wani nannauyan wahalallen barci ya yi awon gaba dani mai cike da mafarkai na ni da Y Im cikin wata irin rayuwa mai dadi, da kyar Mama ta tashe ni. Na ja cambas na daura na juya a hankali ina kallon kaina a mudubi. Ban yi mamakin ‘yar zabgewar da na yi ba cikin ‘yan kwanakin nan da duniyar Imran ta sanya ni gaba. Banda su Azizah shiriritattu ne ya dace su fahimto sauyuka da dama a tare dani, to ita kanta Mamar su haka take, ko cikin dare ba ta rabo da call na emergency case, don haka ba ta samun nutsuwar da har za ta fuskanci kananun abubuwa kamar wannan. Na ci gaba da kallon kaina cikin mudubin, ba wata kwalliya na yi ba ban da mai da farar powder da na shafa, amma ni kaina ina alfahari da ‘yar zagayayyar kayatattar fuskata, wadda in ba son kai irin na dan adam ba, zan iya cewa alhamdulillahi, babu abin da Allah subhana bai kawatata da shi ba. Fararen idanu, giran ido kakkaura, dogon hanci da tsararren baki mai daukar hankali. Idan kuma aka yi maganar zubin halitta abin sai shukrah ga Maqagina, domin ko yaro dan shekaru biyar ba zai iya yi min kallo daya bai maimaita ba. Farina kuwa ba fari ne sol ba, ja ce ni kalar uslin Abzinawa na Damagaram. Ko a farce ba za ka ce na hada jini da Bahaushe ba, domin komi nawa har yatsun kafata irin na Inna na Rabi ne. Na dauki jakata (school bag) na rataya a kafadar hagu, nasa kai zan fita, Imran na sawo kai zai shigo sai muka yi karo garam, da goshinmu, kasancewar nima ba baya ba ce wurin tsawo zamu yi kafada da Imran, illa ya nuna min kaurin jiki. Na yi saurin ja da baya ina ta faman ba shi hakuri don ni har ga Allah ban ji tahowar shi ba, kasancewar shi mutum mai nutsatstsen taku, duk na gigice saboda yadda ya yi min jiya na dan fara shakkun sa, da alama dariya na ba shi. Ya ce, “Ni ne mai ba da hakuri Zaynab, kin kwana lafiya?” Kalaman shi sun matukar bani haushi, wannan rainin hankali ne, kuma kamar son jin halin da mutum ke ciki ne, wanda shi din ba zai maganta mini ba, ba sai ya kyale ni in ji da ciwona ni kadai ba? “Don haka maganar na kwana lafiya ko ban kwana lafiya ba, ba damuwar ka bane….” Magana nake a zuci, ban san cewa har ta fito fili ya ji ba. Ya yi murmushi kamar bai ji ni ba, ya sake matsowa gareni ya russuna ya dauko min jakata da ta fadi a dalilin karon mu ya miko mani, ya sake cewa, “Kin kwana lafiya Zaynab?” Wannan mugun mutum ne, bani da zabi ban da na daga mishi kai domin ya gama kashe mun jiki da fitinanniyar muryarshi. Ya ce, “Amma ni kin ga ban kwana lafiya ba, Zaynab saboda ke!” Ya ci gaba da mugun murmushin, yana magana ne kasa-kasa yanda in har akwai wani cikin dakin bayan ni dake kusa da shi, duk kasa kunnen shi ba zai ji abin da yake fadi ba. Na kyabe baki na ce, “Allah yai maka magani”. Dariya ya yi ya ce, “Ya yi mana magani baki dayanmu za ki ce Zaynab. Ba gara ni ba, amma ke maganin naki ai mai GIRMA ne, wanda ni kadai ke iya maganta miki, kuma ba zan yin ba, saboda ni mai hankali ne sabanin ke da kuruciya ke dawainiya dake”. Ya sake jifana da mugun murmushin, sannan ya miko min ledar da ke hannunshi, tuni na yi suman tsaye. Wani takaici ya zo ya tokareni a kahon zuci kamar in yi aman zuciya don bakin cikin maganganun da ya yaba mani. Bai kuma bani damar in yi magana ba ya juya yana cewa, “Ki yi maza ki tafi makaranta kin zauna nan kina shirme, tun baki tafasa ba kenan wannan in kika kara shekaru uku a gida ban san me za ki zama ba, gara Abba ya tattaraku da zarar kun kare makarantar nan ya ba wani mai tsautsayin sadakar ku. Balle ke Zaynab irin jarababbun matan nan ne wallahi (nympho), duk wanda ya aure ki ya shiga uku”. Ya juya zai fita yana mun dariyar keta, na ga idan na bari ya fice ban yi wani abu ba na fadi ba nauyi. Idanuna suka ciko da kwalla, bayan kadawa da suka yi suka yi jawur na ce, “IMRAN!” Tunda yake yaran gidan baki dayansu babu wanda ya taba gigin kiran shi da Ya Imran ma balle IMRANAN gabagadi. Iyakacin kowa YA EM,

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29