Chapter 28
Chapter 28
ji na tsane su bana son ganin su kamar yadda na tsani wadda ta bani. Na ji haushin kaina da har na tsaya na kula Mami, wani kululu ya zo ya tokare min a makogaro ko miyau na kasa hadiya. Su Azizah sun dauka wai mamakin ita ‘yar waye ne ya kamani, don son kara burge ni da tabbatar min da Mami wace ce, Azizah ta zura da gudu dakin Mama ta zo da mujallar ‘OVASION’ da bama gajiya da kallo ta auren Aishah Babangida tana nuna min Mami cikin ‘yammatan Aishah, dama kuma na so in tuno inda na ga fuskar Allah ne ya mantar dani. Irin rudewar da Azizah ta yi a kan Mami sai na ji ina tausayin kaina, da burin da na daura a kan Ya Im. Yanzu idan ta san ni din ina son dan’uwanta ko ya ya za ta karbi al’amarin? Ni Zaynabu-Abu ‘yar Malam Ali, jikar Mamman Gwarzo, da bamu da komi sai tumaki, sai tsintsaye. Na fara fidda rai da Imran a karo na farko a rayuwata. Na san Imran ya fi karfina nesa ba kusa ba, wai wan ce ‘kwarya ta bi kwarya…..’ Anya maganganun Anti Rose za su taba zama gaskiya kamar yadda take ikirari? Kwana na yi a ranar nan cike da kishin Mami, ko rintsa ido na kasa, gami da wani azababben son Imran dake kara daidaita zuciyata. Sai dai wannan karon kam kauna ce ta hakika, da har nake jin ko ya ya ne, ko ya nake ba zan iya barwa Mami shi ba. Amma a dole washegari na shiga tirsasa zuciyar da ta fidda Imran da duk wani al’amarin shi a cikin ta. Ina nuna mata beke da illar dake cikin hakan, ina nuna mata Imran ba alkhairi bane a tare da ita, ina nusarsheta da cewa a kul, Zaynabu! Igiyar rakumi… ta yi nesa da kasa, tsira da mutunci…. ya fi tsira da kudi, abu mai yiwuwa shi ake yi ba mara yiwuwa ba, yaro tsaya matsayinka…. kada zancen ‘yan duniya ya rude ka, kai zai kai nya baro. Amma wallahi zuciyar nan mai laushi da kafiya (delicate but strong) ta ki amincewa, ita dai Imranan nan shi kadai take so by all means. Babu abin da ya dame ta da hujjoji na, ba ta san su ba, IMRAN kawai ta sani. Cewa take Zaynabu-Abu luv, have no boundaries….. A kwanakin biyun da suka biyo baya, duk rabin hirar su ta Mami ce da kirkin ta. Idan na ji ba zan iya jurewa ba, sai in tafi daki na ci kuka na ya isheni, in sa sabulu in wanke fuska. Kamar wata zautacciya, in saka wannan in kunce da wancan. Daga karshe na alkawarta ma raina ko Imran din nan ne autan maza na hakura da shi, don tsira da mutuncina da na iyayena. Duk wanda ka ga Hajiya Sa’a ta tashi ta rako gate da kafafunta, to tabbata ya isa, ta san shi din wani ne, za kuma ta samu wani abu a jikinsa, duk da babu abun da Allah bai mata ba ita da mijinta da ‘ya’yanta, ba ta da godiyar Allah ko kadan. Ko a jiya Imran ya aiko mata da sabuwar mota (Hummer Jeep) da gaba dayan albashinsa na wata da watanni, dama ya ci alwashin ita ne za ta fara cin gajiyar iliminsa, amma a yadda take nan-nan da Mami, sai ka rantse ba ta taba mallakar kwandalar kanta ba. A kwanakin da suka biyo baya ban kara yardarma zuciyata ta tuna Imran ba, na tattarasu shi da Mamin da al’amarinsu na zuba a kwandon shara. A yau muka fara zana WAEC da practical Biology, bamu muka fito ba sai karfe hudu na yamma. Kwakwalwata ta yi zafi, kaina ya yi zafi rau, ga yunwa, gajiya da nannauyan barci a kaina, wanda ban samu na yi ba a daren jiya muna ta karatu. Don haka mun shigo gida a gajiye lis, muna tafe muna hada hanya, ban lura da bakuwar motar da muka samu ba a harabar gidan. Muka isa falo kowacce na ‘wash-wash’, ni ko dafe nake da goshina, idanuwana a rufe nake tafiya a cikin falon. Ban ankara ba na ji na yi karo da mutum, kamin wani lafiyayyen kamshin turaren nan na (Boss-Intense) ya bakunci hancina. Na yi hanzarin bude idanuna da suka yi ciki sosai saboda yunwa da wahala, na dube shi yana murmushin nan nasa mai cike da ginshira, a hankali ya ce, “Ya… ‘yan makaranta ba a gani ne?” Wallahi sauran kadan in fadi a tsakiyar falon sakamakon kafafuna da suka kasa daukar nauyin jikina, saboda yadda Imran ya koma, in da dare ne ba za ki gane shi ba. Ya zama kato, ya zama ‘giant’ ya kara kyau na ban mamaki. Tsayayyun kafadun nan nashi ‘pysique’ na barazanar gabje maza biyar a lokaci daya saboda yadda suka kara habaka har da doro na musamman, na kasaitattun maza. Ya kara haske ba can ba ‘chocolate’, ya kuma kara murjewa, da gani za ka san naira ce ta zauna da gindinta. Lafiyayyen agogon ‘switch-blustery’ sai walkiya yake cikin lallausar fatar hannun shi, yana sanye da farar shadda kal kamar takarda, dinkin mazan Maiduguri. Na yi gaggawar ba shi hanya, ya yin da shawarar Anti Rose ta zo min cikin kaina kamar karatun sallah. Cikin halin ko in kula na ce, “Sorry plz, ban ganka bane na gaji ne sosai. Muna barka da zuwa”. Da daddare muna falo muna ta hirar pepermu ta yau, ya shigo yana balle links din hannun shi yana tambayar Mama ina abincinsa. Gaba daya muka rude mai da labarin zuwan Mami, muryata ta fi ta kowa karadi, ina kara kuranta kyawun Mami da kurzanta kirkin ta, duk sai ya sha kunu ya bi ya daure lallausar fuskar nan tam, alamun ba wargi. Amma bamu fasa ba, kamar ma zuga mu yake. Hajiya na gefe tana ta murmushin jin dadi, ta ce, “To kai ka ji ‘yan kannen naka ma sun yaba da ita”. Ya dago fuskar nan a murtuke kamar hadari, ya kulu iyaka. Ya hade giran sama da na kasa a take ya koma (previous IMRAN) mai gigita kannensa. Na yi mamaki da bai daka mana tsawa ba. Ya zube min manyan idanun shi a mamakance, ya ce cikin gatse da wata murya mai kama da ta mai ciwon makogaro, “Har da ke Zaynab, kema kin yaba da Mami?” Da sauri na gyada kai ina dariyar nan da Malam Bahaushe ke kira (yake), na ce, “Wallahi kuwa Ya Im na yaba, a very simple lady, ba ta da girman kai”. Ya sakar min hararar da ta kada min ‘ya’yan hanji, ya ce, “Tunda haka ne ki hadata da Faruq man, kin ga shima baya da girman kan, amma ni ta yi mun tsufa sai yarinya (sweet 16) zan dauka, yadda nake (fresh) din nan in na auri kaman Mami ‘yar (28) ai na ci baya……” Iftihal ta toshe baki kada dariyar da ta zo mata ta fito, Azizah da Hajiya suka daure fuska wato sun ga samu suna neman ganin rashi. Ni ko na yi tsuru-tsuru don duk maganar nan da yake idanunshi a kaina yake yin su, kamar da ni kadai yake magana a falon. Ya ci gaba da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29