Skip to content

Chapter 17

Chapter 81-82

Afif Book One Complete Hausa Novel 1,681 words 0 views Progress saved
Download Book

*☆☆︎*

*☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆*

*AFIF*

*🅃🄰🄺🅄🄽 🄺🄰🅁🅂🄷🄴*

""Amma wallahi ba ni na kasheta ba abin da nasan inayi safarar yara ƙanana shine abin da nake ,

"shiru gun yayi domin jin mai sarkin zace ,

Saida ya nisa sannan yace

"a cikin ku wa ya kashe min mahaifi ?"

tuni su waziri da uwantale babar waziri suka fara muzurai

"wannan kuma uzairu ya fini sanin komain domin da shi aka haɗa baki saboda shine likita me kula da mai martaba Allah ya jiƙanshi da rahama ,

"Uzairu we hakane ?"

eh amma wallahi ni abin da san na aikata nayi koƙari in mai allura bata yuhuba hajja ce ta bashi guba abincin da ta kawo sannan sanƙira da uwantale su sukai kaiwa aliyu guba sha shin sa ana zatan mamy ce ta bashi

"tuni aka tuso ƙiyar uwan tale da sanƙira da waziri ,

Haɗa baki sukai suka ce sun aika ta sai aka dawo kan hajiya zaliha tuni daman tana ta tonawa kanta asiri da abin da ta aikata ganin basu wahalal da shari'a ba aka yankewa su uwan tale huƙuncin rataya ranar sallah a idon

mutane domin izina ga al'umma hajiya rumaisa kuma da zaliha huƙuncin ashekara ashirin agidan yari har su mai dala duba da irin ɓarnar da suka aikata suma ratayesu za ai shi kuma za abada gawar gwamna abinne ta saboda an gano ba wanda ya kashe shi doka guduma akai fadawa suka kare sarki domin antashi da shari'a

da gudu faisal ya rungumai afif yana kuka yace

"Dan allah ka yafewa mama ko zata sami salama arayuwar ta,.

Wllh ban ruƙe mama ba Allah ya yafe mana

"ameen,

Wanann kenan

Tuni su anty aisha da rabi suka hallara sai kuka suke jin abin da malam yake ce musu

Malam yace

" a yau zaki barmin gida tunda bana ku bane ,

sosai take rawa tana juyi su kuwa rufa'i tun da a ka fasa randa suka shiryu yanzu haka suna zuwa daukan karatu

a guje inna hadiza ta fita yayin da suka kusa karo da Duna a ƙofar gida

''shima ya shigo a guje domin ya faɗa musu wani albishir tuni ƙiɗan algaita ya fara ra tsosu da kuma jiniya bigeta yayi ya shige ,

yayi da ta dakata domin ganin wasu masu kayan sarauta

"inna inna wallahi dan sarkine ya shigo garin nan kuma nan gidan suke nema yanxunnan lawandi yake faɗamin ,

dafa girji tayi tace

Mun shiga ukku allah isa ba ƙarangiya aka biyo ba

"uhmmm ni menayi da za abiyoni bayan sun tabbatar bani da laifi har yanzu dai wannan cutar taki tana nan baki ga abin da ya sami yar uwarki ba ,

"Bana son rashin mutunci wllh kakiyaye ni manu kana jinsa ko ?"

Ya isa dan allah ku dakata yawa wasu yara ni yanxu wallahi na shiryu barar da nake na a dena sana'a zan nema

Malam yace

"Alhamdullahi na jidaɗi daka shiryu manu yanzu in anjima kai wanka kazo mutafi gun yansanda kai ƙara domin wallahi ba zan yarda ba sai anne momin ya'ta kasa ƙara sawa yayi dukansu suka tashi domin ganin wacce ta ke shugowa duk da hutu da jin daɗi ya game jikin ta ta koma yawa balarabiya cikin tantama malam yace

"zara keece?"

Eh nice malam sai ta rushe da kuka da sauri hindatu da larai suka matso kusa da ita wani sassanyan ƙamshi ke fitowa a jikin ta ga suttura ta alfarma

"Zara ke kika zama haka hindatu ɗauko min ta barma ,

"TO, to yaya da sauri ta tafi dauko ta barma da wowa tayi ta shinfiɗa misu suka zana ,

duka sun sandare cikin kuka ta fara basu labari ba wanda beji tausayin taba

"dan girman Allah zara ki yafe mini

Wallahi malam ba abin da kaimin inma akwai na yafe tuni suka nemi afuwar juna basma kuwa saboda kunya kasa motsi tayi inama ita aka tura aikatau

"malam tare dashi muke ,

To to shigo da shi

To tace ta tashi a sanyaye ta daɗe a soro domin bata san yarda zata faɗamai ba candai tayi kundunbala ta nufi inda motarsa take yana cikin ya zuba mata

"idanuwa Allah yana gani besan irin son da yakewa zara ba yana jinta a jinin jikina ,

Cikin sanyin murya mai daɗi tace

Yace ka shigo

"okay muje tayi haka zata fara tafiya ya ruƙo hannunta sosai ta fara ƙoƙarin ƙwacewa amma ina ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba,

Haka ta haƙura suka jera tare sai suka zama taurari tuni kowa ya fito domin gida gida duna yake bi yana zara ta dawo tana auran dan gidan sarki

"da sukaje cikin shagwaɓa da bata santayi ba tace

Dan Allah ka sakini

banza yayi mata tabbas mamy uwace ta gari haka ya aiyana a zuciyarsa

"har suka shiga cikin gida har ƙasa ya durƙuwa ya gaidasu ,

a tabarma ya zauna sunyi mamaki yana jikan sarki dan gidan sarki amma ba ƙemƙƴami ya zauna a wannan gidan nasa

"hindatu jeki ki gyara ɗakin iya su zauna domin dare ya kusayi basa koma a yauba ga inaso ta zaga dangin mahaifiyar ta ,

to malam

Saurin kallon sa tayi irin hutu da jindaɗi da yatashi da shi bata tunanin zai iya zama anan

na gama malam

Zara kaishi ɗakin kafin ku tafi

To tace iya gyara ya sha gyara ga yar katifa ansa sai ƙamshin turaran huta yake ajiye wayoyinsa yayi ya zauna janyo ta yayi yace

"zauna muyi jira ki bani labarin garin nan,

Lamgwabar dakai tayi kamar baby tace

to ka bari sai ansha ruwa sai inbaka yanzu nagaji

uhm mijinki kike cewa kin gaji

wata kunya ce ta rufeta ta rufe fusƙarta da ta fukan hannayan ta sun sha jan lalle

Zuba mata ido yayi yace

"au kinyi lalle ko ki nunamin mugani ?"

ta shi tayi zata gudu domin bazata iya wannan sabuwar rayuwar da daddy nur ya tsuro mata da ita

ƙafa yasa aikuwa ta harɗe ta waɗo jikin sa cikin soyayya wacce bata ɓoyuwa a fusƙar sa yace

"au ni kike gudu ? hmmm yarinya dan dai azumi muke da yau na cire miki kunyar ki "

Ƙasa tayi da kyakkyawan idanuwan ta ta fara wasa da hannun ta cikin siririyar muryarta kamar sarewa tace

"Dan Allah daddy nur kai haƙuri kaga a gidan mu nake ,

Tabbas yarda tayi tasiri a jikin sa kallo ta yake yawa wata yar baby lalle aure ni'ima ce da shi

cikin salon tsokana ya ja mata kumatu yace

"uhmm daddy nur sauran ƴa'ƴan da zamu haifa fa kinsan fa ina so muhaifi ƴaƴa masu yawa kinsa nifa ba rago bane ?"

da sauri ta ɗago ta kalle shi

ɗaga mata gira yayi yace

ta shi kije nima akwai aikin da zanyi a garin nan

cikin sauri ta tashi tace

"To, daddy nurr

uhmm momy ɗin nur

Rufe fuska tayi

Tana dariya ta futa

da sauri saude ta sha gaban ta tace

"iyee ahe daman gaskia duna yake faɗamin kin koma balarabiya ''

Cikin mamaki ganin irin ramar da saude tayi ga wani uban goyo da tayi duk ta fita hayyacinta ta ce

Saude

"Zarah kin ga yarda na koma ko ?…… "

kamar ƙadangaruwa ta gyaɗa mata kai tace

"zo muje mu zauna "

cikin yaƙe duk fusƙar ta ta muzan ta tace

"to,

duk da irin tsamin da take bugawa haka zara ta haƙura suka shiga ɗakin inna hindatu tuni hira ta ɓarke tsakanin su

Zara bayan tafiyar ki mama tayi min auran dole bana sonshi haka na haƙura kinga dan mu

Dasauri zara ta kunto shi a baya tace

masha Allah kuna kama saude

dariya tayi tace

"dan Allah ki roƙar mana mijin ki ya bashi aiki a company ɗin sa "

a jiyar zuciya ta saki tace

"To, saude zan tambaye shi
tare da saude suka zaga dangin mahaifiyar ta domin aliyu yace bashi da lokaci bayan ta dawo daga zaga dangi ta huce taga ana ta gine gine

tuni suka shiga mamaki suda saude wata mahaukaciya ce ta taso tana rawa tace

La kamar zarah malam

Kuka zara tasa tace

"eh inna nice haka kika koma ?"

Hhhh haka boka ya mayarda ni

Ganin tana nema ta dukesu yasa suka ruga aguje sai da suka zo wajan gida suka nutsu zara ta kalli saude tace

"saude rayuwa ba tabbas ,

alla ka samu dace

"Amin saude"

to bayan sun koma masarauta ranar sallah aka kai zara gidan ta tasha kuka dangin mahaifiyarta sun nuna mata so

Zarah da afif sun shinfiɗa rayuwa mai kyau abin sha'awa tuni ta matsamai sai ya dawo da nur duk da mamy taƙi

haka ta matsa mata saida ta basu domin ita tayi alƙawarin baza wahalal da dan wani ba domin taga izina duk da tana fama da laulahi haka ta jure zarah ta haifi dan ta namiji yaci sunan yusif ana cemai Imam sosai anni tayi dana sani haka su hanal yanzu hanal ta aure kabir suna zaune cikin kwanciyar hankali tare da matarsa da ya'yansa ita dai likitoci sunyi binkice bazata taɓa haihuwa ba saboda mahaifarta ta lalace haka take kula da ya'yansa saboda matarsa aikitake...

*Bayan shekara hudu*

zara ta ƙara haifan yan biyu duka mata aka sa sunan mahaifiyar ta da anni ana ce musu

afura da afreen bayan su tace hutawa zatayi

"nikuwa nace banga laifin kiba ƴa'ƴa har ukku a shekara hudu"

tuni rayuwar su ta canza ya samawa kauyan garkun abubuwan jin daɗi har da makarantu yayi musu ya gyara gidan su zara ya koma na bulo ya samarwa su duna aiki

Yanzu shine sarkin garin abdul gwamna sosai suka samarwa da birnin zaki ci gaba zara ta zama yar boko ga ilimin addini

Cikin takunsa na izza ya matso bakin kofa ya dubi zara cikin so da kauna yace

"hayaty mu rufe ƙofar mu nagaji da oum yasmeen ta ɗibar mana labari tana bazawa a duniya "

rugumai shi tayi tayi mai kiss a kumatu tace

"gaskiya kama daddy nur mungaji ,

duka yaran suka matso suka rumgumai su suna dariya

Alhmdllh Alhmdllh

Ya ubangiji duk kan wasu kura kuraina ka yafe min a yau na kawo karshan littafin AFIF

Ina godiya ga kungiyar

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*

Sai

*AMINCIN WRITING ASSOCIATION*

Mu haɗo a littafina na gamaba

Zaku iya samin audio na wannan littafin akan wannan number 09061890481

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1-6
  2. 2 Chapter 7- 10
  3. 3 Chapter 11-14
  4. 4 Chapter 15-16
  5. 5 Chapter 17-27
  6. 6 Chapter 28-31
  7. 7 Chapter 32-40
  8. 8 Chapter 41-50
  9. 9 Chapter 51-60
  10. 10 Chapter 61-66
  11. 11 Chapter 69-70
  12. 12 Chapter 71-72
  13. 13 Chapter 73-74
  14. 14 Chapter 75-76
  15. 15 Chapter 77-78
  16. 16 Chapter 79-80
  17. 17 Chapter 81-82