Skip to content

Chapter 3

Chapter 11-14

Afif Book One Complete Hausa Novel 509 words 0 views Progress saved
Download Book

Cikin hanzari yake tafiya bai damu da jinin da kafar sa keyi ba, ringing wayar keyi yana ji amma sai yayi kamar ma bai san tana yiba dan yasan kiran yana da nasaba da MASARAUTAR MAI ZAKI, shiyan zu duk kallon muna fukai yake musu maciya amana

bedroom ɗin shi ya nufa still ƙafar shi bata daina zubar da jini ba

masha Allah na faɗa yayin da nayi arba da bedroom ɗin, ashe parlor ba komai bane, dakin fari ne tas da alama Afif ma'abocin son white color ne gawasu labulaye masu kyau farare cikin hanzari ya karasa gaban wani tamfatsaesan hoto matar jiki kamar kai mata magana ta amsa saboda kyan da hotan yayi tana sanye da leshi baki da adon flower golden da yarfin pink colour hannu ta ruke da yarinyah a kallah yarinyar xatayi kimanin shekara biyar ko hudu, yarinyar tana sanye da baby gown pink colour da adon flower blue ansa mata haed band blue

yayin da afif ya na ruke a hannu jiddah ya sakar mata tausassan murmushin sa mae tsada har ana iya gano hushiryar sa fadan kyawun pic din bata baki ne duguwar riga ce a jikin ta dinkin dai dai da zamani haka daurin kanta baza akira jiddah me kyau ba saidai tsakatsaki saide kwalliya da huto ya zauna ajikin ta,

a hankali yake shafa hotan yana zubar da hawaye tabbas yasan lokaci zaizo da halin kowa zai bayyah a masaurautar zaki munafukai zasu bayyana jin alamar inuwar mutum akan sa yasan bazai wuce kabir ba, dan idan ba shi ba babu wanda zai shigo mai kai tsaye

" ya Allah" kabir ya furta cikin daga muryah yace

" Afif ya kamata kamanta da jiddah kashiga sabuwar rayuwa , hakan da kake kana bawa makiyanka da masu san ganin ba yanka damar jindadi jiya ina garkun naga jaridar NCB ta wallahfa hotan ka we katafi kasar america domin duba kwakwalwar ka wai, tunda matar ka ta mutu kasami lalu'ar kwakwalwa suna kira da arufe maka asibitocin ka domin gudun kar ka cutar da al'umma , we a sibitin da kake aiki su daka tar dakai , sai dai nayi binkice emir's yace kana nan ba inda kaje , da alama makiya ne suka biya suka wallafa har gidan TV NBC sun dora inda ake Jin ra'ayin mutane akan haka sai dae cikin hundred percent 85% basu yarda ba wasu nace wa aeba Kai ke duba marasa lafiya ba, tun da ma baka kasar koda kana nan sai wadda cutar shi ta munana zaka duba Alhmdllh hakan samun nasara ne "

AFiF a hankali ya buɗe bakin sa cikin zazzakar murya mai dadin sau raro yace

" kabir ko kowa ya yarda ina da cutar ƙwaƙwalwa kai nasan bazaka yarda ba , kabir inajin ciwo narashin kulawar mahaifiya tun ina yaro kabir bansan dadin uwa ba , tsakani na da ita sai kallo daga nesa kabir abubuwa sun minyawa wallahi muddin na gano waddah ya kashe jiddah koda mamy ce sai na hukunta ta kabir bazan koma birnin zaki ba in har bangano ba ...........

*AFIF*

Oum yasmeen

*My first novel is return*

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1-6
  2. 2 Chapter 7- 10
  3. 3 Chapter 11-14
  4. 4 Chapter 15-16
  5. 5 Chapter 17-27
  6. 6 Chapter 28-31
  7. 7 Chapter 32-40
  8. 8 Chapter 41-50
  9. 9 Chapter 51-60
  10. 10 Chapter 61-66
  11. 11 Chapter 69-70
  12. 12 Chapter 71-72
  13. 13 Chapter 73-74
  14. 14 Chapter 75-76
  15. 15 Chapter 77-78
  16. 16 Chapter 79-80
  17. 17 Chapter 81-82