Skip to content

Chapter 13

Chapter 73-74

Afif Book One Complete Hausa Novel 2,013 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin fitar sirri bawan da yalura da fitar ta tanufi shashin inna domin a can su kabir za su same ta da sallama ta shiga ɗakin tsohuwar matar tace inna barka sa wannan lokaci

"yauwa uwar masu gida ,

numfashi ta fesar tace inna nazo ne akan wata shawara da zaki bani

Uwar masu gida ina jinki

"hajiya anni ce take so ta haɗa aliyu da hanal a gaskiya hankalina ba zai kwantaba kinsa bakin su ɗaya da su rumaisa ina tsoron in rasa ɗana a karo na biyu domin nasan da manufa za suyi haka kina ganin waziri zai yarda ya bawa afif yar sa bare da wata manufa ba ?

kinsan fa sawa mai martaba gubar nan inna rantsai bazanyi kaffara ba da sa hannun su tunda tsoyake yayi mulkin birnin zaki kinsa kuma a jiya dadtawan masarauta sun aiko da taƙarda cewa inhar sarki be sami sauƙiba zasu naɗa waziri ruƙan kwarya kwallace ta taru daga idonta ta share tacigaba da cewa

"inna we yaushe mutanan nan zasu bar mu ne ashe daman mulki baƙar inuwa ne kowa babban burinsa yazamo shike juyaka wallahi dana san haka yake bazanyi kwaɗayin sa ba da yanzu yana zaune a matsayinsa na ma aikacin gwamnati koba komai duk wata zamu sami abin da zamu sa abakin mu ga dukiya iya dukiya amma ba kwanciyar hankalincin ta inaso intafi Qatar amma ba dama saida masu tsarona badama inyi sirri saina baki numfashin mutane kinaga ina zargin jakadiya tanayiwa su rumaisa aiki aboye

Uwar masu gida zancan ki hakane kinyi tsinkayi mai kyau tabbas

domin yana auran ta sai yarda sukai da shi kuma sun shirya su hallaka shi nima yau na tashi da damuwa yarinyar da kanwata ta mutu tabari kwana biyu ina mafarkinta acikin mugun hali dole gobe inje kauyan garƙun anan tayi aure data mutu nane mijin ta yabani ita in ruƙe yaƙi shekara goma shaɗa kenan yawa anmin asiri ban ƙara biyawa takanta ba za zamemin dole inje inga halin data ke ciki

"To, Allah isa lafiya

hmmm amin amma zuciyata bata min daɗi ina ganin ba lafiya akwai wani abu da ubangiji yakeso yasanar dani shiyasa nake mafarkinta Allah isa ba mutuwa tayi ba

Amin ya Allah

Asalamu alaiku

Walaikassam aa babana yau kaine a gari daman tare da mai gari nake ganin ku in yana ƙasar

ina hinin ku barkan ku da wannan lokaci na sameku lafiya

"lafiya lau kabir ina mai gari yake ?,

inna sai addu'a yana nan yarda kika sanshi kowa ya raɓe shi gani yake cutar sa zaiyi ko yaushe afif zai koma kamar da yaushe komai zai daidaita Allah yakawo mana ƙarshan wannan lamari

Amin kabir

Kabir anni tana so ta haɗa auran afif da hanal

What wallahi ƙarku yarda da idona na ganta awani asibiti an zubar mata da ciki ni nayi mai sha'awar auran wata yarinya tuni ya basu labarinta yanzu haka tana a sibitin mu ko za kuje ku ganta ayi auran a sirri in zata iya yin magana musan gidan su ayi binkice

"Mamy tace,

yauwa kabir in ansha ruwa zamu je a sirrin

a'a uwar masu gida yanzu mu tafi

"To, shikkenan bara mu tafi kira min abduraman da lamir su same mu a can ,

okay bara in kirawo su

aa uwar masu gida muje mu gani sai mu zauna ayi shawara

"To, inna.

wannan kenan

cikin manyan kaya ɗanyar shaddah ce fara kal sai kamshi yake zubawa yayi wani irin kyau yawa ka sace ka gudu wayar sa ya dauka ya fito motarsa ya dauka

ya nufi masarauta kamar ance ya dubi glass din motar sa ya ga wata mota baƙa tana binsa shi'umin murmushi yayi we yaushe su dr uzairu za zu barsa gudu yafara yi har ya isa masarauta kai tsaye yasan yanzu abbie yana fada da sallama ya shiga cikin fadar ta haɗu iya haɗuwa hannun dama galadima ke zaune na hagu waziri sai sauran manyan masarautar

gaidasu yayi kowa yayi mamakin ganin sa a yanzu sauram awa daya a sharuwa

*Su inna a madubi*

tafiya suke cikin nutsuwa harsuka isa asibitin kainuwa kabir ya bi dasu ta ƙofar sirrin saboda in aka gansu zai zamo abin magana cikin har suka isa kofar ɗakin da take ciki mamy ce sahun gaba ta buɗe handle ɗin ɗakin sallama tayi ta shiga sai kabir sai inna me zata gani suman tsaye tayi ta fara cewa

wallahi itace ɗiyar yar uwata fa'iza da ta mutu duk inda jinin fa'iza yake ba zan ƙi gane saba

'''da sauri inna ta ƙarasa gun ta ta ruƙe mata hannu tace,

"ya akai ki kazo nan ina su hadiza da baban naki ?"

Hawayene ya zubo fusƙarta ba baƙin magana ko nuni ma baza iya ba

"itama hawayene ya zubo mata Allah sarki jinin fa'iza ne na bari rayuwar ta ta zamo haka ya a ƙai na manta dake har shekara goma sha daya ban waiwayeta ba anya kuwa lafiya su hadiza mai mugun hali suka barri bana boka bana mallam su hadiza ne suka saki a wannan halin da kike ciki anya kuwa hadiza zata gama da duniya lafiya tunda ran fa'iza take cutar ta rungumai ta tayi tana kuka mai tsuma zuciya duk wanda ya gansa su a haka sai ya tausaya musu

"mamy ce ta matso ta dafa ta tace,

ayanzu ba kukan ki take buƙata ba addu'ar ki take buƙata kiyi haƙuri inna insha Allah komai yazo ƙarshe

Zancan mamy gaskiya ne mu ɗauke ta mu tafi sai ta zauna a ɓamgaran inna har zuwa ta sami lafiya ko

"Eh tu yanzu ya za kai da uban masu gida?"

hmmm inna kenan ai yanzu ya manta da ita domin cewa yayi insan ƴar da zanyi da ita shi yayi nasa

wannan kenan

cikin girmamawa ya gaida su mamaki ya kusan ƙar da waziri

Tuni annurin fusƙar waziri ya dauke

"har ta su yarima suhal sun haɗe fuska faisal ne kaɗe yake walwala domin sai lamir da abdulraman da suka gan shi farin cikin su ya daɗu

Alhaji adam ma yana farinciki alhaji ibrahim kuwa da suke ciki ɗaya da shi wani irin tsana yayi mai saboda ashi ya so yayi sarki a ka bashi tun daga lokacin suka fara takunsaƙa da shi duk shi yake zuga anni akan lamarin Afif tuni kowa ya bar abin da ƙe saƙawa a zuciyar sa domin jin gyaran muryar da mai martaba yayi

" martaba yayi yace"

Alhmdllh bayan doguwar rashin lafiyar da nayi na sami sauƙi shekaruna ta tafiya ya kamata in matsa in bawa wanda zai iya dauƙar nauyin masarautar nan mai albarka ina yin godiya ga duk wani mai muƙami dake masarautar nan da yabani haɗin kai na gudanar da mulkina lafiya tuni yan jaridu suka sai tashi da camera domin dauƙar shirin kai tsaye al'umma zasu gani wato LIVE program

sannan yace

Ina bawa al'ummar kasar nan haƙuri ba dan na gaza da daukan nauyin ku bane kuyi haƙuri zan zaɓa muku shugaba mai a dalci wanda yafini zai ja jirce a kan mulkin wannan ƙasa sanin al'umma ne abubuwa sun faro da yawa ya kamata in matsa kafin rai yayi halinsa ina neman afuwar ku ga duk wanda na cuta ba da sanina ba

Tuni mutane suka fara kuka domin iya adalci yana yi musu ba su san waku ma zai dora ba

"daya ga watan babbar sallah zan naɗa wanda zai maye gurbi na wanda ya daci da mulkin garinnan mai zuciya irin tawa wanda na ke farin cikin kasan cewar shi ahalina

tuni fadawa suka rufeshi domin zai tashi daga zaman fada har ya fita kaf cikin su alhaji ibrahim ba wanda yayi motsi sai galadima da su faisal da lamir da abdulraman sai uban gayyar domin yana ganin dama abie be wahalal da kan shiba gun kiran shi dan shi tsarin mulkin masarautar baya burge ashiba suka fita

da ƙƴar alhaji ibrahim ya iya buɗe bakin sa yace

Waziri kaga abin da tsohon nan yayi mana ya samu a duhu ya faɗi wanda ya bawa in zamu bujire tun yanzu mu bijire shekaran jiya ya aikawa da sarkin musulmi na kasar ethopia taƙarda ya bawa wannan munafikin nan galadima ba musan mene aciki ba

Hmmm alhaji ibrahim sarkin fada dana kofa sun faɗamin harda sarkin shela nan ba gun magana bane kai sahal bayan shan ruwa akwai zama domin mu mu kai hidimar masarauta ba zamu tashi abanza ba wallahi ba za'a naɗa wani mahaukaci ba domin duk mai hankali yasan wayake nufi wallahi mahaukaci bazai mulke muba ato

Yarima suhal yace

nima a bin da nagani kenan tashi sukai suka fita

cikin sauri ya nufi shashin sa dake gidan domin an kusa shan ruwa gashi shi zayyi kiran sallah yana isowa kata faran shashin nasa zuciyar shi tayi wani irin bugawa ya tuno da sahibar sa sai yake ganin tana mai gizo

barka da zuwa mijina nasan ka sha hanya sannu da zuwu uban ƴa'ƴa na

" ya ka tsaya kana kallo na shigo gidan ka cikin aminci ,

"Kamar raƙumi da akala yana binta ,

Mijina kai min magana yau na dafa maka abincin da kafi so

Murmushi yayi yace

ni yanzu bana muƙatar komai ki dawo gareni mai yasa ki ka tafi kika bar mu kinsan irin ɗacin zuciyar da na shiga ni da yar mu kin tafi nur tana tsananin buƙatar ki

Dariya tayi tace

Na tafi gidan gaskiya inda kowa zashi

Dan Allah jidda ƙarki ɓacewa ganina muna buƙatarki

Shish tasa hannu a bakin ta ta ɗaga mai hannu tana mai bye bye

Dasauri ya ƙarasa cikin hamshakin floor nasu wanda iya tsaruwa ya tsaru ga kayan alatu iri iri yawa da mace agidan dan kullum amintatcan yaron sa sai ya gyara komai duk wani abu na jidda yana nan

" duk inda ka ratsa photo tane katu yawa kai mata magana ta amsa gawani glasa ƙato da kifaye kala kala gaban sa taja ta tsaya tace

Habibty kalli ina son yellon kifin nan da baƙi zan so ko da yaushe in buɗe ido ingan sa

Da gudu ya ƙaraso gun ya sa hannu zai ta ɓata ɓatt ta ɓace duk zuciya irinta Afif durƙusawa yayi ya rushe da marayan kuka mai nayi muku kuka kasheta me tayi muku wallahi ko iya nan kuka tsaya iya bakantamin arayuwa kunyi dama kun haɗa dani mun mutu tare

" jiddddddah jidddddah daman ana mai da hannun agogo baya da na gudo dake basu kashe kiba,

ta shiyayi yawa mashayi ya shiga toilet iya tsaruwa ya tsaru komai farine yawa kayi bacci anan saboda kyansa wanka yayi yayi alwala ya fito wata jallahbiya yasa milk color da hula tashi kafiye naci

yasa slippers ya dauki carbi turare ya fesa tuni sassanyan ƙamshi ya fara tashi ya haɗu da turaran wankan da yayi amfani dashi ya bada wani irin kamshe ba zaka so ka dena sha ƙarsa ba fita yayi kai tsaye babban masallaci yanufa dake fadar masarauta ya fara kiran sallah duk wani dake cikin masarautar ba zai manta zazzaƙar muryar sa

"dede da bugawar zuciyar wata tsohuwa dafe girjin ta domin iya kidima ta demauta tuni hawaye ya fara zarya a idon ta idonta yayi ja ƙarya kake aliyu wallahi sai na shafe tarihin ka dole inkoma gun boka domin yayi min ƙarya ya cemin bazai taɓa dawowaba ya akai ya dawo ta fara jifa duk wani kayan dake kusa data

" na shiga ukku da raina aliyu ya dawo ƙasar nan ba zata saɓo ba wallahi tuni gumi ya wanke mata fuska saboda tunowa da tayi shekara shiddda baya boka ya ce mata duk lokacin da aliyu ya dawo topa komai yana gab da zuwa ƙarshe kuma a kwai yarinyar da zai aura kuma ba acikin masarautar take ba ina hakan baza faruba ina yau dole aliyu ya je lahira ,

dole sarauta ta dawo gidan mu wallahi kai ɗana waziri dole ka zage dan tsai domin bazan dau asara a wannann karan ba wannan shegiyar uwar tasa ce ta warware min shirina dole aliyu ka mutu keee moma kiramim sarkin yaƙiii
*……………✍🏼*

*AFIF*

Oum yasmeen

*My first novel is return black*

_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*____________________________________*

*____________________________________*

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1-6
  2. 2 Chapter 7- 10
  3. 3 Chapter 11-14
  4. 4 Chapter 15-16
  5. 5 Chapter 17-27
  6. 6 Chapter 28-31
  7. 7 Chapter 32-40
  8. 8 Chapter 41-50
  9. 9 Chapter 51-60
  10. 10 Chapter 61-66
  11. 11 Chapter 69-70
  12. 12 Chapter 71-72
  13. 13 Chapter 73-74
  14. 14 Chapter 75-76
  15. 15 Chapter 77-78
  16. 16 Chapter 79-80
  17. 17 Chapter 81-82