Chapter 6
Chapter 28-31
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
"tuni inna hadiza takara
diriricewa"
tarasa inda zatasa kanta domin inba idon ta kizo yake mata ba gani tayi kan zarah ya dawo baya haka ma hannayanta
"dakin jagwa ta nufa saidai me arufe taji shi"
cikin daga murya tace.
"larai hindatu kofito kucece ni"
jinshiru inna hadiza tace.
"kona jina kukai min jishu..?"
"kahu Manu ne yashigo yana saba babbar riga duk Ta kod'i da alama yadawo daga yawan ba'arsa gawani ta kalmin yafi karfin kafarsa gawata hula yawa yakifa kamar kwano"
kahu Manu yace.
"gafaran kodai masu gida ga shugaban marukan garkun kowa yace bani ba nima ince dashi bashiba saini d'an maitaba ikwon Allah saini waddah yake zuwa gidan mai gari yimai kirari cau cau wllh anjada ni an,barni saini waddah yaje
*MASARAUTAR ZAKI*"
"mai idonshi zai gani zarah yagai akwance kamar matatciya amma hadiza anyi mara imani yanzu marainiyar Allah ta'alah kikai wa haka?"
GA yarda kikai mata walmukalifatu
jinshiru kahu manu yace.
" tsahare tsahare tsahare"
cikin fusatar zuciya yace.
"yau kenan iskancinki ya motsa to wllh kifita a idona in rufe"
"duna ne yashigo yana shan rake"
duna cikin dauki yace.
baba daga gidan su bintalo nake
"cikin jin kunyar karya yajanyo rigasa tazarce fa'ar shadda ce ajikin sa amma takuma milk ya rufe fuskarsa wai yaji kunya,
duna yace.
"babantan yace infito"
cikin kunar rai kahu manu yajuyo yace.
"ashe duna haukan naka har yakai haka bansani ba?"
duna yace.
"baba hauka kuma"
kahu manu yace.
" yo duna inba hauka ba ina kaga kud'in aure ko gona baka zowa ko nayi maka karya ne...?"
duna yace.
"baba tace zata dinga ciyar da ni tunda tana sana'a kuma akwai tuminin takaba na tsohon mijin ta da akaraba akabata"
tuni kahu manu gumin ya wanke mai mutsassiyar fuskarsa
domin yagane shida d'an sa suna son abu daya
"cikin xuciyar sa cewa yake kaga shegen yaro ina jira ta gama takaba inje ya rugani zuwa ashe bana lissafi dai dai"
haku manu yacire hulalsa ya sharce gumi yace yace.
"duna ina kai ina bazzawara duna ba y'ar gidan malam d'an ladi bace tsohon driver?"
tuni duna ya zunb'uru baki yace
"Eh baba itace"
Kafin kahu manu yace.
"wani abu tuni zarah ta kara zuba wani ihu tare da yin kar karwa har anajiyo sautin hakoranta
duna ne ya kalle kahu manu tuni sukayi idu hudu da kahu manu"
kahu manu yace.
"duna me nake gani ?"
cike da tsoro duna yace.
"baba na kaga abinda nagani ko idanu nane suke fad'a min karya ?"
Kahu manu yace.
"Duna zara'u ta kanan nad'a wllh"
Cikin tsoro duna yace.
"Baba ashe ba karya su inna suke fada ba dasu kece wa zarah tahadu da cutar nan ta aljanu wato *farfadiya*
Kahu manu yace.
" hmmm duna mune mi gun tsira tunkafin ta shafa mana domin ni wallahi ban shirya mutuwa ba yasin inta kaina kaima kaita kan ka"
Inna hadiza kuwa tasami makafa dakin tsahare tashiga tahau kan wata a kwaiti ta dakin tsahare
"tsahare kuwa tana cikin akwaiti abin duniya ya isheta domin ta rantsai in komai ya lafa tana fitowa saita bugawa inna hadiza tab'arya"
topa gidan malam Yusif mai taba suna cikin wani hali yaya zata kaya da kahu manu da dansa duna
Cikin ikwan Allah kuwa komai ya lafa itama zara tashi tayi da alama bama tasan tayi ba
cikin dakin ta tsahare kuwa inna hadiza yace ta tashi tana sharce gumi
Inna hadiza tace.
"we yau Allah yayi da kwana na agaba"
mik'ewa tayi aikuwa tsahare ta fito a fusace tana neman inda tasa tab'arya domin tarantsi inbata ludawa hadiza ba yau bata haifuba
Ita kuwa inna hadiza bata luraba can taga nema yayi yawa ta magantu
Inna hadiza tace.
"kedai tsahare ba arabaki da abin haushe yanzu makike nema ne ?
tsahare tace.
" Hmmm kibari inna fito da abinda nake nema kya' gani ganin idonki"
Cikin fusata inna hadiza tace.
"Tsahare ni kike fad'awa haka ko...?"
aikafin ta karasa taji saukar tab'arya agadon bayanta wata ƙara ta saki
Tsahare sauke wani wahallan numfashi tace.
"Ba keba mara hankali baki san da mutum aciki ba kika zauna wato kina so ki kasheni ko?"
Tuni inna hadiza ta dafa bayanta ko magana ta kasa sai dai taci al'washi saita buga tsahare da kasa
Jin bata tanka ba tsahare tace.
"So kike in mutu to ta Allah bataki ba kika wani sh'irgamin duwawunki masu kama da dala saboda girma kina so in mutu ki aurawa manu yar uwarki ko..?"
Karasa warta keda huya inna hadiza ta dagata sama abinka da ba wata mai kiba ba irin siraran matan nan ne zubin taliya yar murji
Jika ke tim ta bugata akasa Allah yasa ta sauka akan gadon k'arfenta
ciken nishin wahala tsahare tace.
"Wllh dani kike zance sai na kara buga miki tirmi"
Inna hadiza tagyara d'aurin zanin ta tace.
"Hhhhhh tsahare kenan kin manta da koni wace ko?"
"to wllh in kin manta bara in tuna miki lokacin muna da jini ajika ni nake miki duka "
tsahare ta saki ajiyar xuciya bawe ta hak'ura bane aa ajiru zuwa rafi wataran tulu zai fashe
kahu manu ne yashigo yana buga kofa yace.
" keeee tsahare wannan wanne irin tsorone kunbi kun k'unshe adaka ina zuwa naga abinda ke faruwa na nad'ai hannun rigata"
"ganin tsahare da hadiza sunyi shiru alamar zancan nasa yasami matsuguni a zuciyar su
kahu manu yace.
" dana nad'ai hannun rigata nafara ce musu
wllh k'arya kuke ni ne dan gidan malam mai taba mai tsittin goma sha biyu zaku nutsu ko saina ko naku ai tuni sukai shiru "
inna hadiza tayi k'arfin halin cewa.
"manu ba'a tab'a mutum inyana farfad'iya wllh mutum dauka yake yanzuma gun datayi sai anzuba toka"
Kahu manu yace.
"Mahaukatan banza waya fad'a muku wannan zance ko kowa zai d'auka banda mu jiniin malamai kakana *MALAM SULE ME TURAK'AR YASIN*
"ganin sun nutsu suna jinsa yana kwararo musu karya domin be bud'i ido yaga kakansa ba koshi kansa mahaifinsu mai taba besan shiba ya mutu
kuma sana'ar sa itace saida tawada ba malami bane"
kahu manu ya kara da cewa har d'aukan aljanu yake ya bugasu da k'asa
har aik'en su yake yasin abin sai waddah yagani
"k'arasa warsa keda huya duna yashigo yayiwa su inna alama da ido suyi shiru ya rufe mai ido da wani farin yadi dayake har ankira sallah magariba to gari yayi duhu abinka da kauye "
duna ya mak'e murya yace.
"nine Shugaban aljanu *ni sarki turk'wa* naji kana anbatar sunan kakana sule lafiya kana ihu yasin saina shanye maka allon kafad'a"
Kahu manu yace.
"kuyi hak'uri Dan Allah wllh bansan sunan kak'an kabane a yimin afuwa"
Duna yace.
"Muba musan wata afuwa ba zab'i daya yarage gareka ko yau ka kwana bak'ai ba bacci ko mutsutsai maka ruwan kwakwalwa "
Duna yamak'e muryah yace.
"wanne ka zab'a?"
Cikin rawar murya kahu manu yace.
in kwana banyi bacci ba
Jika ke duna yasaki wata mahaukaciyar dariya yace.
"ba iya nan yatsa ba kaso auran d'anka da yar gidan malam d'an ladi muga kana so ka hanashi in kak'i zan hadaka da d'an autan aljanu ya cire maka hanji ciki karayu ba hanji "
kahu manu yace.
hakama bazata faruba na aminci zan shig'e mai gaba ayi bik'n
Duna yace.
Hhhhhhhhhhh tsoho kanasan duniya dayawa to rufe idon ka zantafi
Cikin rawar murya kahu manu yace.
"To to to"
" cikin sanda yafuce ad'akin"
Dankin jagwa kuwa koda komai yalafa yand'audo su kace sunga gun zama
suna ciki ba waddah yayi tunanin zuwa yayi sallah sai maida zance suke
"Wani ub'an gangi aka fuga ga ihun karunnuka nan alamun cewa jagwa yashigo cik'in gid'an kai tsaye d'akin sa yanufa sai dai me zai gani ?"
Cikin cije laib'e jagwa yace.
"lalle yau layira zatayi baki Dan wllh yasin ba waddah zan bari yafuta acikin ku"
daya daga cikin yada kata da cin cingum yace .
yo kuma bakace mufita ba ba inda zamu munga gu wllh yana yarfa hannaye sunci zobuna da awarraro yayi fari da idonsa ya saki kwai jikake tush kas
"Bishira ta kama zancan da cewa .
Katambayi d'an uwanka ya muk'ai dashi yasin karo damu badadi
Jinjina k'ai jagwa yayi yafuta daga d'akin yasa muk'ulli ya k'ulle kofarsa ya fita kirawo yaran sa ...........✍🏼
*AFIF*
*Oum yasmeen*
*My first novel is return back*
*The writer of BINTA YAR JAGALIYA*
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
Table of Contents