Skip to content

Chapter 12

Chapter 71-72

Afif Book One Complete Hausa Novel 2,531 words 0 views Progress saved
Download Book

""Amin yusrah tace ,

Ammy tace

"Ƴusrah Nusaiba ku tafi ku kwanta nima bacci zanyi kunga tara tayi kee yusrah gobe ki tafi gidan ki kinsan bana son ki dinga zuwa kina kwana yauma afuwar dana yimiki saboda yau kuka dawo gobe nusaiba zata biki ku gidan ki ku gyara abin da kika ga be miki ba tunda na sanki da iyayi cewa zaki yi bayin da sukai miki aiki beyi ba,

"To, mamy Allah ya kai mu suka tashi ,

Washe gari duk wani musilmin da yake birnin zaki ya tashi da azumi

riga ce T-shit black color yar gidan gubbacci anyi rubutu da white color ansa *ALWAYS BE YOURSELF* ya ɗaura agogo rolex sumar kansa sai sheƙi take haka ƙasumbar sa

lips ɗinsa sai sheƙi suki sunyi pink color yawa na jarirai saboda tsabar taushin su mayan sexy eyes ɗinsa masu kama da mai jin bacci ya sanya farin glass cikin nutsuwa da ƙasaita yake taka matattakalal ɗakin da zai sada shi da

Daƙin abbie har ya isa gun gani yayi a lamar da mutane da yawa har yana iya juyo muryar jarababbiyar tsohuwar nan mai kama da matsastsan lemo ƙaramin tsaki ya ja zai juya kenan ta ita kuma ta murda handle ta fito tace

Wanake gani kamar wannan yaron mai baƙar zuciya yawa ta kafuran farko ga subfa yawa bayahude kai abin yayi maka yawa koda yake ka tsotsa a nonan asiya

Cikin murtuke fuska kamar koda yaushe ya juyo saboda tsabar yawan gashin girarsa ya kusan haɗewa baki sidik ya kafeta da manyan idanuwan sa be cewa ta kalama daya ke duk iskancin anni tana shayin sa

"Salati tayi tana tafa hannaye shikkenan asiya ta haifa mana jaraba ace mutum kullum ba fara'a in kaga yayi murmushi to yayi mugunta anya kuwa afif kana so kaga annabi ranar gobe kiyama ?"

A hankali ya matso kusa da ita yabuɗe baki yawa mai ciwan baki ya ce ,

"aa in nazo zangan shi ki rufemin idanuwa kina ta yimin ihu a kaina zaki fasan dodan kunne fa

juyawa yayi ya shiga ɗaki bakin sa dauke da sallama ido hudu sukayi da gimbiya rumaisa da zaliha suna zaune sun gama haɗa kayan da zasu tafi da shi dayake an sallami abbie cije lips ɗinsa yayi cikin isa da izza ya ƙarasa gun abbie kaf cikin su ba wacce ta amsa sallamar sa abie ne ya fito daga toilet yace,.

"aa abbana kazo ?"

Eh abie ya ɗurƙusa ya gyasheshi anni ce ta shigo kamar an wurguta tace mansur

"Sarki mansur yace,

na'am hajiya

"wallahi karabani da wannan ɗan nan na matar ka domin ba jini na bane ,

Rumtsai ido afif yayi domin jin ƙazafin da anni ta yi mai

" abbie kuwa cewa

" yayi dan allah hajiya kiyi haƙuri"

ware idanuwan shi yayi sunkaɗa sunyi ja ya ɗago ya tsura mata idanuwan shi tuni jikin ta ya fara rawa domin har ga Allah yaron nan inyayi wani abu tsoro yake bata cikin haɗewar murya tace

"ni zan tafi Allah ya ƙara sauki a kula ƙarka ƙara cin abincin asiya tunda so take ta kashe ka taci gado ,

""""sandar ta ta dauka ta dauki jaƙarta tafita da alama yau bata tawo da masu tsaranta ba ran su hajiya rumaisa farikal anyi maganin wannan shegen yaron mai taurin kai ,

abie ni zan tafi i nada mara sa lafiya da zanwa aiki

dafa kansa yayi yace

"Allah yayi maka albarka yaraba da duniya lafiya ya kareka da sharrin mutun da aljan ka ruƙe addu'a sannan yau kazo gida muyi shan ruwa tare kai zaka jamu sallah duk maganar nan da yake ba wanda yaji me yake cewa

Kai ya ɗaga mai yace

"insha Allah zan zo amma abie a daga min ƙafa takwas na dare yan jarida zasu yi hira dani ,

Okay ba damuwa Allah ya tsare

Amin abbie ya fuce daga ɗakin

Allah ya jada ran sarki yanzu abinda yaron nan yake ya da aibata ƙarasa ba ta haɗiye zancan ta saboda wani kallo daya jefeta dashi

Wannan kenan

tafiya yake acikin nutsuwa har ya iso tamƙameman asibitin horn yayi gate man ya buɗemai

matashin yayi sauri ya rufa mai baya saboda yana so ya gyashe shi fitowar sa kenan daga mota yace

"barka da zuwa oga andawo lafiya ,

kai ya ɗaga mai yace ,

"Barka de ya aiki ?"

Alhmdllh komai yana tafiya daidai

Masha Allah kuɗi ya ɗauko besan adadin su ba ya miƙa mai ya tafi tasbiyi yake a ransa sai ka tsuramai ido sosai zaka kula cewa bakin sa na motsawa kadan yanzu kowa ya kama aiki wani daki ya shiga ya canza kaya zuwa na fiɗa ya fito

wannan kenan

Kabir yace nurse ki kula da yarinyar nan tunda ansami nasara ta farfaɗo

Nurser farida tace

"Dr bata fa magana tun ɗazu saide ta kalli mu da alama tana jin me ake cewa bansan me ya hanata magana ba ɗazu dr marsut ya ɗauke ta yatafi akai hotan maƙogaranta ba a ga komai ba ina ga gaskiya saide ayi addu'a da alamar kamar sihiri ne a jikin ta ,

Okay ni zan tafi sai in faɗawa dr fita yayi daga ɗakin wani hayene yazubo mata da sauri nurse farida ta share mata gashinta ta tattara gudaya tana tausayin yarinyar batafi sa'ar autar ta ba gashi ta gamu da kaddarar rayuwa ɗaukan ta tayi domin tayi mata wanka suna zuwa banɗakin ta noƙe alamun bata so ta ga jikin ta

"Zaki iya?"

shiru tayi tayi ƙasa da kai domin ko hannunta ba zata iya ɗagawa ba ganin haka yasa ta tuɓe mata kayanta bata shiga tashin hankali ba sai da ta ga duk shatin bulala wani yana kan wani wani ya warke wani kuwa sabone bata yimata wanka da soso ba iya shower gel mai kamshi da tsada tayi mata amfani da shi tayi mamakin girman jiki irin na yarinyar domin ko mace yar shekara talatin baza nuna mata giniwar jiki ba goge mata jikin ta tayi ta daura mata tawel ta dauke ta suka fito kaya ta dauko ta fara samata iya kunya tashiga kunya ganin ta dauko bra ta sa mata sannan wata riga mai siririn hannu ta sa mata ta busar mata da gashi ta sa ribbon ta daure mata gashi

tuni kyahun ta ya fito tea mai kauri ta haɗa mata tana bata tana sha

Wannnan kenan

Afif yaka mata yau yarinyar nan ƙarta ƙara kwana asibitin nan saboda ta sami sauke sai kuma a dinga yi mata addu'a ko allah zaisa ta dawo hayyacin ta ta faɗi inda yan uwanta suke

Kabir ina zan kai ta tunda kai kace mu temaka mata ni nayi nawa sauran naka ka kaita gidan ka dan ni wallahi ba zan ajiye mace a gidana ba

"afif kasan halin madam ko tana da kishi kuma ko da asa misali zan dauketa wazai kula da ita bayan ko ɗaga hannunta bata yi kasan fatisat tana zuwa aiki ko dolle mu sami mafita wallahi dr farida tayi ƙoƙari yau kana huɗu tana ɗaweniya da ita ,

Hannusa ya wanke ya cire hulal kan sa yace

"kaga malam matsamin in huce fito wata daga aiki ka tsareni duk na gaji mutum ukku nayiwa aiki ƙar ka ƙara tarata da maganar nan kai kasan yarda za kai da ita in kana sonta zan baka auran ta har sadaki zanbiya we madam kishine da ita Allah yasa ita ta kawo kishi duniya yama ka mata kai aura ita da take aikin banki sai shida zata dawo ina taga lokacin kula da kai ya ka mata kai aure ,

_Tofa fans shi kenan be kamata yayi aure ba muje zuwa_

hmmm ai wannan maganar da kai ta kamata afif ba dani ba yaka mata kai aure ka manta da rayuwar jiddah ka gina sabuwar rayuwa ka nemawa nur uwa ta gari

wallahi kb zamu iya ɓatawa in ka ƙara yimin zancan in manta da jiddah fuuu ya fita

Kabir sak'ar baki yayi yana kallon sa wannan wane irin kaddarah ce afif ya haɗu da ita shekara shida ana abu ɗaya wayar shice tayi ringing yadawo daga tunanin da yake da sauri ya ɗaga kanin mamy ce ta kirawo yace

"barka da wannan lokaci ya jikin abbie ?,

''da sauki kabir dan Allah kana da lokaci yau k'arfe ukku kazo ?''
insha Allah zanzo

Okay nagode

Bakomai mamy ai haifatace baki ba nine da godiya

*💎KAUYAN GARKUN💎*

wallahi magen juyda ƙahuru ku kiyayeni ko fita daga harka ta in kunki yasin zan farke cikin mutum

"wani banzan kallo ƙahuru ya yimai yace,

Jagwa kake kowa to in kafasa baka haifuba inbada iskanci

ai kafin ya ƙarasa yaga jagwa ya fito da wata sharbebiyar huƙa sai kyalli take aguje ya nufi gida yana ihu haka ma magen juyda

kahu manu yana tsugune yana alwal la'asar yaga suna gudu yarda butar yayi ya mara musu baya dan aciwar sa allah ne yasan kade masifar da tasa su magen juyda gudu

gida ya shiga a guje har babbar rigarsa tana harɗeshi cireta yayi ya wullar ganin ya shigo a guje yasa tsahare da tun da ta dau azuminnan ta fito bakin bishiya ta zauna ashe wata huyar na shafe wata ɗakin jagwa ta shiga tayi maka fa

dagudu manu ya shigo ya shiga makewayi ya rufe yana haki suma haka su magen juyda suka shigo da sauri ƙahuru ya haye kanbishiya domin yasan duk inda ya ɓoya a gidan jagwa zai iya fito da shi ko yayiwa mutanan gidan barazana afito dashi muryar jagwa yaji yana cewa

"Yasin duk inda kake ka fito dan wallahi kowa na gidannan yau bazai sha ruwa ba cikin kwanciyar hankali kai manu ina kuɗin ta kalmina yau zaka bani ko in cire kunnan ka jin haka keda huya manu ya saki gudawa a wando domin yasan jagwa zai iya Allah ya zazzagewa su juyda albarka duk su suka jawomin wannan

tsiyar hawaye ya sharce duk yunwar da yake ji yadena jinta garam jagwa ya buka kofar banɗaki jikake tsuuuu ya saki gudawa ya ƙara lafewa a jikin garu iya tsinuwa yau su ƙahuru sun shata har cewa yayi bashi basu

ji yayi ya ƙara ƙarta huka a ƙasa gumine ya shararo mai yawa anjiƙa shi da ruwa ga kuka da yake da majina Allah yana gani bayasan mutuwa yau gashi ƙannansa sunja maiiii

Daman ni nasan ƙahuru da magen juydah ba sona suke ba Allah sarki duna zaiyi maraicina be tsinke da lamarin jagwaba saida ya tsin ce muryar sa tuni cikin sa ya ƙara murɗewa

"wallahi ƙahuru kafito tun muna shedar juna da kai kun kama ƙaryata kun mata duka nayi magana kace inyi duk abin da na gadama kai kuma manu zaka sani yasin zamu haɗu a way za kai baya ni futa yayi zuciyarsa sai ta fasa take ,

jiiib kake ji ƙarar sauko war mutum daga binshiya wandon sa duk ya jiƙe da futsari k'ar kaɗe jikin sa yayi yana ce wa

"jibi magen juydah duk na ɓaci wallahi yau naga tsiyar anjiye ɗan daba a gida kaga duk yarda nabi na ɓaci,

*KAHU MANU* ne ya fito yarab rab sai ɗoyi yake idonsa duk ya kumbura yana ruke ciki ya sami kan tabarmar da tsahare ta tashi ya zauna shi kuma yana sauke a jiyar zuciya hannu ya ɗago yace

"ai kafin yayi magana suka sheƙe da dariya harda ruke ciki ,

Wallahi bashi kuka ci shegu marasa mutunci ina dan uwan ku kuke yimin a haka shegu da fuska yawa anyi dauryar zunumi .

*wannana kenan*

wata motace ta nufo shashin mamy inda ta yi parking wata matashiyace za tayi shekara ashirin da biyar ta fito sanye da kayan gargajiya na ƙasar ethopia inda tsagar rigar tundaga cin yarta har ƙasa tana taunar cingum jikake kas kas ta saki kwai ta fasa da alama bama ta san yau al'ummar garin birnin zaki sun tashi da a zumi

tasa farce ga make'up fuskarta kamar tayi magana wata dadtijuwar mata ce ba zata huce shekara arba'in da bakwai ba tana sanyi da duguwar riga blue black ta yane kanta da wani ƙaramin mayafi tafiya suke a nutsa har suka isa tam ƙameman floor mamy babu kowa sai haɗiman tani takaici ne ya ma maye zuciyar ta da hassada cikin isa ta sami gu ta zauna ta dubi hadiman ta tace

"Kee jiki ki fadawa wannan ishashshiyar kice mata ni kilishi na zo ,

Cikin girmamawa suka zube suka gaysheta bata amsaba tafiya ɗaya daga cikin su tayi domin ta isar da sa ƙonta ba dawowa tayi tace ,

"tana zuwa,

ita kuwa *HANNAL* tasan ya airpon a kunnan ta tun kafin ta iso kamshinta yayi musu maraba tana sanye da abaya milk color an mata ado da duwatsuna masu hasken Diamon taci jan ƙunshi hannu da ƙafa hannuta sanye da awarwaron gold da zoben sa ta nannaɗe gashinta hannunta ruke da wayarta tace,

Assalamu alaiku kaf cikin su ba wanda ya amsa sai wani cika sukeyi suna batsaiwa bata nuna ko a fuska taji haushi ba sai ma wani shi'umin murmushi cikin isa ta sami ɗaya daga cikin haɗadɗun gujerun floor ta ta zauna ta mike kafa wata bewar ta tana matsa mata sai ga su hajiya rumaisa yawa an hankaɗo su ba gaisuwa suka sami gu suka zauna

"ganin haka mamy ta dauke wayar ta tana dan nawa domin basu ce mata ba bazayi magana ba ,

Kilishi tace

"Amma jiba,

Ko kallon ta ammy batayiba haushine ya kamata tace

" yau na kawo yarinya ta ajiya dan haka ƙar'inji kar in gani abarta ta wala tunda nan gidan ubanta ne ba zaitaɓa can zata ba amma ke zai iya can zaki bare kawe ,

Rumaisa ta ɗora da cewa

"batasan ta kuraba dan haka bama buƙatar ai mata iyayi da sunan tarbiya koda yake rashin tarbiya ya ƙare a kan ki tunda saboda kwai dayun kuɗi kin haifar wa maimar taba shege

murmushi tayi tace

"zan muku uzuri saboda jahilci yana damun ku mai kuka ɗauke kazafi kowa ya dubi ALIYU MANSUR ALIYU jinin mansur ne dan haka ba abin da zan ce muku in lokaci yayi kwai sani wallahi ni Asiya nafi ƙarfin in yi da ku kun ɗauka abin da kuke shi kowa keyi ta meƙe ta tashi tace

"kilishi zaliha baku da bakin magana saboda kunsa zina ta kame jikin ku watama har rabo ta samu wata kuwa ita saidai tayi ko rabon bata samuba wallahi bazan hada gurɓatatcan jini ba saide tsabtatatce ina gab da nuna muku sirikar ku daga haka ta nufu dakin ta

Gabaki dayansu sun sha jinin jikin su

hajiya we uwar ɗakin mu tace in kaiki can ɗakin

Wani banzan kallo hanal ta yi mata alama tayi mata data dauke jakar ta takai mata

"Duk shegiyar da tai miki kira ma kinji hanal,

Okay anty rumaisa zanyi amma anty rumaisa banga yaya afif ba

Dasauri hajiya zaliha ta rufe mata baki tace

baki da hankali ko kinga abin da ke hadani da ke wallahi daddare kizo muyi maganar nan

farin cikin ne ya ma maye ta ta kusan mallakar afif domin saboda shi taki yin aure sai gashi kuma a yanzu tana hasasowa kanta samunsa

Mun tafi ki kula da kanki

"To, bye momcy na

*AFIF*

Oum yasmeen

*My first novel is return black*

_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*____________________________________*

*____________________________________*

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1-6
  2. 2 Chapter 7- 10
  3. 3 Chapter 11-14
  4. 4 Chapter 15-16
  5. 5 Chapter 17-27
  6. 6 Chapter 28-31
  7. 7 Chapter 32-40
  8. 8 Chapter 41-50
  9. 9 Chapter 51-60
  10. 10 Chapter 61-66
  11. 11 Chapter 69-70
  12. 12 Chapter 71-72
  13. 13 Chapter 73-74
  14. 14 Chapter 75-76
  15. 15 Chapter 77-78
  16. 16 Chapter 79-80
  17. 17 Chapter 81-82