Skip to content

Chapter 11

Chapter 69-70

Afif Book One Complete Hausa Novel 1,579 words 0 views Progress saved
Download Book

TUNI suka naɗa wanna zai magana tashi yayi yace,

Sunana SaM dawud ina aiki a asibitin nan bangaran masu cutar ƙoda na dauke tsawon shekara goma ina tare da asibitin nan sai dai gaskiya tun lokacin tafiyar ka muka fara samin matsala saboda zaka ga

wasu ma aikatan sun ajiye aikin su saboda duk wata sai an kwashe mana albashi wani bifi ya tashi da dubu dari ba mun kai korafi ance za a gyara ƙar shema yau watan mu goma ba albashi da ya gama jawabin sa zauna ,

tuni idon Am yayi ja saboda ɓacin rai cikin hacking voice ɗin sa yace

" MD MANAGER ACCOUNTER GENERAL na baku sati daya ku dawo min da kuɗina sanin kan kune kunsan ni *YAƊIN MAGE NE* duk wanda ya cini sai yayi amai na sannan ina mai bawa ma aikatan a sibitin nan haƙuri insha allahu yanzu zan sawa kowa albashin sa,

addu'ar rufe taro yayi kowa ya yashi wasu na farin ciki wasu na baƙin ciki
tashi yayi agajiye kai tsaye gida ya nufa sai yaga kiran kabir dole yaje in da yake katsai kiran yayi ya tafi ɗakin da yake sallama yayi ya shiga yace,

"lafiya ka kirani gida nake son zuwa kaga dare yayi ?"

Kabir yace

"yarinyar nan ce tun ɗazu nake kanta amma ko motsi ba tayi ba ,

Dasauri ya ƙarsa gunta temaƙon gaggawa yashiga bata sannan ya sa mata oxygen gumi ya asharce yace ,,

"ga inda matsalar take ka tafi yimata dressing in drip ɗin hannun ta ya ƙare ka cire ma sannan fa tana buƙatar jini kuma naka zan ɗauka in yayi mata shikkenan ,

Okay yanzu muje lab a gwda dauki samfirin nata dauka yayi suka tafi lab sai de kash nasa beba sai na Am nashi ne yayi dole ya kwanta aka dibi leda biyu sosai kabir yake dariyar ƙeta yace,

"gaskiya Wannam beauty ɗin ta sami nasara we jini har lida biyu koda yake batai ƙƴan banza ba ni wallahi dama ka aureta zaku dace wallahi ,

kai kabir kasan me kake faɗa me zanyi da wannan yarinyar inda ace nayi aure da huri na tabbata zan haifi ka marta ni manyam mata ma basa ga bana balle wannan bata huce yar cikina ba Allah yaa ki yaye,

Dariya kabir yayi yace

" haba mutumina ba asan inda rana zata waɗi ba ƙar kace min madam ta haihu,

duka ya kai mai ya kauce yana dariya kai Am ya girgiza ya fita

motar sa ya dauka ya nufi hanyar gida horn yayi mai gadi ya buɗe fitowa yayi sai da yayi tafiya mai dan nisa tukunna ya xo kufar da zata sada shi da shashinsa wani kati ya fito dashi mai kama da ATM ya zura a kofar nan da nan kuwa ta buɗe

sallama yayi ya shiga ma kunnin futula ya kunna nan da nan haske ya gauraye ɗakin

masha Allah iya haɗuwa ya haɗo kasan ɗakin an malale shi da epoxy mai kalar blue da wasu flowers pink ga wani carpet mai laushi kamar auduga kana takawa kafafuwan ka suna nutsaiwa

ga wasu hadaddun luxury sofa royal dark blue da adon teal color

zama yayi yana fiddah wani wahallan numfashi ya lumshe idon sa ya daɗe a haka tukunna ya buɗe ya zubawa pop ido yawa mai shirin ganin wani abu wayar shice tayi ringing

banza yayi da ita ji ana shirin da marsa da kira ya ɗauke wayar a fusace zai kashe sai yaga sunan da yayi save wanda iya tsayin rayuwar sa kiran be taɓa shigowa wayar sa ba tsayawa yayi ya ƙarewa sunan kallo first love sannan ya dauka yayi shiru jiya ance

"ya jikin naka kaje gida lafiya ?"

Numfashi ya sauke daman yasan ba de mamy bace iya rayuwar sa be taɓa ganin mamy ta bashi kulawa ba cikin gaji yace,

"Alhmdllh lafiya qalow nusaiba jin muryar mamy yayi tana cewa nusaiba wakika kiramin da wayata ke ina take wayar bani abata ita kuma ta bata amsa dacewa ya AM nakira ,

"wane AM kuma nusaiba bana son rakice rakice ?,

Haba mamy yaya AFIF ne fa shinake nufi nayi mai ya jiki kitta ya kashe wayar fridge ya nufa ya dauko rowa mai sanyi

ya buɗe baƙin gorar ruwan ya sa abakin sa duk ya shanye ya hullar da robar

a jiyar zuciya ya dinga saki ajire ajire ya wanda yayi tsaire fresh yogurt ya dauko ya buɗe ya fara sha ɗakin baccin sa ya nufa

masha allah komai nasa tsabtsab ba dadti gaba ki ɗaya komai na ɗaki farine toilet ya shiga

wow yawa ka zauna ka ci abinci wanka yayi yai alwala ya goge bakinsa ya fito cikin wasu hadaddan pajamas parare tas bakin gado ya zauna ya zura glass sai ya fito balarabe sak lapton ɗinsa ya ɗauka ya kunna datar sa saƙonan nin email ɗinsa ya buɗe yana bada amsa wani saƙone ya shi gomai kamar haka,

_me ka dauki kan ka aliyu mansur zaki ka mar yarda na kashe matar ka kai ma saina kashe ka sannan a kwai ajiyar mu a gunka saide kash kafi muzo mu dauka kariga mu ɗauka yau ɗinnan zan kaita lahira hhhhhhhh wwwzzzz_

glass din idonsa ya zare wannan wacce ajiya ce ko de ya bugawa nusaiba waya ya tambayi ina princess take wayar shi ce ta shiga ruri da sauri ya dauka cikin muryar kuka nusaiba ta ce,

Ya yan fashi sun tare mu a hanya sun tafi da nurr

"Amma Allah be basu nasaraba da suka ga jami'an tsaro zasu kama su shine suka yarda ita suka gudo ta ƙurje a kafa da hannu ya lamir yayi duba ta ya bata magani yanzu muna gida ,

"ajiyar zuciya ya sauke yayi hamdalah aran sa cikin yar sassayar muryar mai cike da haiba nitsuwa da kamala ba zaka taɓa gane halin da yake ciki ba yace,

Nusaiba ku ƙara kula mutanan nan da gaske suke sai sunga baya na dan haka ku ƙala kula ƙar kudinga fita yawo

"TO, yaya zamu kiyaye insha Allah yaya anty yusrah ta zo ga su afnan ,

Kice mata ina yimata sannu da zuwa

kit ya kashe wayar shiru tayi tana kallon wayar muryar mamy ce ta dawo da ita cikin hayaiyacin ta wato sai da kika faɗamai ko shima yaji da abin da ke da munsa yusrah ce ta shigo afnan na kafaɗar ta tace ,

"Mamy we ina yaya ance ya dawo ban gan sa ba yanzu daga bangaran sa nake ?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace,

"Yusrah kamar yarda kika sani ta miƙe ta shiga ɗaki kan gado ta waɗa ta saki wani irin kuka sai da tayi mai isar ta

sannan miƙewa shi ga toilet ɗin dake bedroom ɗinta tayi alwala tana fitowa ta ɗauki hijabin sallah ta ta shinfiɗa praymate ta ɗauki qur'ani ta fara karantawa ko tasami sauki a zuciyar domin abubuwa dayawa yayi mata yawa wayarta ce ta fara ringing bata ɗaga ba ganin ana ta kira ba kaukautawa yasa ta yi sallama gaban tane ya waɗi ganin mai kira da sauri ta ɗaga tace

" brk da harwaka Anni ina huni barka da dare,

Cikin fada anni tace

"yimin shiru da ban huni ƙya ganni za kiwa mutane daɗin bakin da ki ka saba sanin kanki ne ni nafi ƙarfinki da tsafetsafen ki kurwata kur aniyarki ta biki,

"to kibu ɗe kunne ki jini yau hanal zata dawo daga Dubai a shashin ki zata sauka saboda tsabar rashin mutunci sai yanzu ki kaga damar ɗauka wayata wallahi ASIYA kike yayeni

Muryar ta narawa tace

"Wallahi anni ina banɗaki ne shiyasa domin tasan ta ce mata tana karatune to tashin hankalin da zata fuskanta yafi haka Allah ya kawo ta lafiya ,

kee we yaron nan mai zuciya yawa ta kafiran farko yazo dan haka auran su zan haɗa da hanal bawe ina faɗa miki dan kin isa aa dan inuna miki isata da ƙarfen ikona akan danki bawe na yarda jika nane ba domin baya kama da ahalin mai zaki tun huri ki nema me uban sa kafin indawo kan ki ke da shi kitt ta kashe waya ,

"Wayar ta ciro da ga kunnan ta ta dafe kirji bata son wannan haɗi kaf ahalin xaki ba wanda be san halin hanal da mahaifiyar ta yanzu ma haka ance fa da saurayin ta ta tafi dubai hawene ki zarya afuskar ta yawa an buɗe fanfo

ahaka su yusrah da nusaiba suka sa me ta mamy lafiya dan Allah me yasaki kuka ?"

Nusaiba tace,

"mamymeke faruwa murmushi tayi ta goge hawayan tace,

Abune ya fadamin ido na

Yusrah tace,

haba mamy in baki faɗamana ba zamu shiga wani hali mamy mai zaisa ki ɓoyemana ko dan saboda ciwanki ki faɗa mana kyaji sauki in kika bar abu a ranki zai dameki

ajiyar xuciya tayi ta fara faɗa musu duk abin da ya faru

Mamy ga shawara awanna karon ki nunawa anni iya kacin ta inaha Allahu ba zatai nasaraba kiyiwa yaya aure bayarda zatai da ke tunda ba ita ta haifa miki ɗan ba yaka mata su daka ta da cutar da yaya gobe ki kira abdulraman da lamir mu shawarta sanna tunda abbie ya sami sauki ana ganin gobe za a sallamo shi a gobe a haɗa su waziri da wani ba kusantan shi a daura aure haka shine mafita

"TO, yusrah Allah ya bamu sa'a sannan kinga zamu faɗawa kabir ayi komai cikin sirri sai lokaci yayi sai kowa yasani *……………✍🏼*
*AFIF*

Oum yasmeen

*My first novel is return black*

_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_

https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

*____________________________________*

*____________________________________*

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1-6
  2. 2 Chapter 7- 10
  3. 3 Chapter 11-14
  4. 4 Chapter 15-16
  5. 5 Chapter 17-27
  6. 6 Chapter 28-31
  7. 7 Chapter 32-40
  8. 8 Chapter 41-50
  9. 9 Chapter 51-60
  10. 10 Chapter 61-66
  11. 11 Chapter 69-70
  12. 12 Chapter 71-72
  13. 13 Chapter 73-74
  14. 14 Chapter 75-76
  15. 15 Chapter 77-78
  16. 16 Chapter 79-80
  17. 17 Chapter 81-82