Chapter 5
Chapter 5
Uwar ta ba. Malam Ali ya dubi wadannan kasaitattun mutane, basu kyamaci nashi ba sai shi? Ba wannan yake ji ba, illa tattalin mutunci da martabar Zaynabu Abu, wanda muddin ta gusa daga kusa da shi da Rabi, ba mamaki ya FADI a nan gaba. Abin da suke ta mummukin sa a tsakanin su shekara da shekaru ya fito duniya ta sani; GIRMA YA FADI! To amma shi kansa zai so Abu ta yi ilimin da watarana zai ganta haka a kasaice kamar su Hajiya Azumi, ko ko ta rika taimakon al’umma kamar yadda Sa’idu ke yi ta fannoni da dama, ba wai ta hanyar kudi ba kadai. A yau matasan da ke neman aiki a garin Gwarzo in dai har suna da takardun nasara masu kyau (graduates) na diploma ne ko NCE, ko ko babban digiri, wurin shi suke zuwa ya hada su da Sa’idu, kamin dan lokaci za su zo suna gode masa, suna sanar da shi an samar musu aiki da albashi mai tsoka. Haka masu neman gurbi a jami’o’i saboda yadda gurbin karatun jami’a ya zama a wannan kasa tamu, sai ga masu iyaye a gindin murhun. Almajiran Malam da Sa’idu ya ya samarwa gurbi a jami’o’i ba za su kidayu ba, don haka al’ummar Gwarzo kullum cikin amfana da Sa’idu suke, tare da shiwa Malam Ali albarka saboda ci gaban da ‘ya’yansu ke samu a dalilin sa. Haka matasa wadanda Allah bai basu daman yin karatun ba, yana hadasu da gwamnati su samu taimakon sana’o’i na dogaro da kai. Wannan dalilin da wasu da yawa da ba zasu fadu ba, ya karfafa shi da ya barsu su je da Abu, to amma bai yarda a yiwa Abu aure nan kusa ba, sai ta mallaki hankalin kanta, ta san WACE CE ITA? To ga ‘yan bokon, wannan ai ba wani abu bane da har sai Malam din ya fada, su dama basu da burin da ya wuce ayi ta bokon har a kure shi in ana kurewa. Da wannan ZAINABU-ABU ta koma Sokoto, gidan Baba Sa’idunta. *** ZAYNABU-ABU MAI TAGWAYEN SUNA! A duk yadda dan Adam ya samu sauyin rayuwa ko y ya ne, imma ta fannin abinci, suttura ko muhalli, ya kan samu sauyin zuciya dana surar gangar jiki gaba daya. To hakan ce ta faru dani a gidan Baba Sa’idu. Duk da irin sabuwar rayuwar da na budi ido na samu kaina a ciki, hakan bai hana ni tuno gida ba da wadannan mutane guda biyu; Malam da Inna Rabi. Sai kuma na samu kaina da jin haushin kaina mai tsanani na wautar da na yi na amince da zaman gidan Baba Sa’idu, bayan a da shine babban burin rayuwata, wato na ganni kusa da Baba Sa’idu. Dalilin kuwa shine, kwata-kwata tsarin rayuwarsu ya sha banban da tawa, da irin rayuwar da na taso a cikinta. A ganina irin wannan rayuwar bata dace dani ba; ‘yar mallam jikar mallam. Rayuwa wadda babu Allah ko daya a cikin ta sai rayuwar tsurar ta. Sai a kwana a wuni ba a ambaci Allah ba, balle a ja carbi, sallah ma ba kowa ke yi a kan lokaci ba, balle ayi maganar jam’i, don shi Baban ma kwata-kwata baya zaman gidan. Idan ya tafi cikin makaranta tun karfe takwas na safe sai shida na yamma yake dawowa cikin gidan, haka nan kullum yana bisa hanyar meeting ko seminar a Abuja ko Lagos da sauran manyan birane. Ban taba ganin mutum (busy) irin Baba Sa’idu ba, bautawa bokon yake da karfinsa, lafiyarsa, lokacinsa da aljihunsa, yayin da jami’ar Danfodiyo ke kara bunkasa da samun ci gaba (inaudiably) a dalilin kwazo da sadaukarwa irin nasa. Rayuwar gidan rayuwa ce da ke sawa mutum ya manta da Allah, da irin tarbiyyar da ya taso a cikin ta saboda jin dadin da ke cikin ta, sakaci da rashin kwaba ga ‘ya’yan su, abin har ya so yayi yawa. Duk da haka ina kokari naga cewa ban kaucewa tarbiyyar Rabi ba da koyarwar Mallam. Hakika duk wanda yasan rayuwar Malam Ali da iyalansa, itace rayuwa a bar koyi. Babu abinda suke bari ya shagaltar dasu daga bautar Allah da kiyaye sallah. Kuma babu shakka shima Baba Sa’idu a wurin su ya samu wannan tubalin na kiyaye sallah, domin ya kan ce mun tana hani daga aikata alfasha da aikin munkari. Irin yadda su Iftihal suka ga bana wasa da sallah, ko me muke yi da zarar lokacin sallah yayi zan tsame kaina har sai na bada farali, shine sanadiyyar da suma suka dage, duk sanda nayo alwala suma zasu mike su dauro alwala, wannan ba karamin fa ranta ran Haj. Azumi yake ba. A ranar dana zo Aziza bata nan tana porthercort hutu gidan Antinta Isaita kanwar Haj. Azumi, Iftihal kuma tana makaranta. Bazan manta ba zugum nayi, na zubawa akwatun kifaye da ban taba gani ba ido (aquarium) kifaye nata gudu a ciki masu ruwan kumfar zinare cikin mamakin ilmi da fasaha na bature, wanda yayi tunanin ya zabo kyawawan kifi masu rai, ya zuba cikin wannan gilashi. Haj. Azumi ta umarci Gaddafi (Gambon su Aziza) kuma autan ta, da ya rakani dakin su Aziza, in yi sallah inyi wanka in kwanta in huta, don kuwa ba karamar tafiya muka kwaso ba ta yini guda cur. Da nayi wanka na canza zuwa doguwar rigar shadda ruwan makuba, da aka yiwa dinkin babban riga. Haj. Azumi ta kira ni muka ci abinci tare, ni da ita da Ghaddafi, tana mun hiran shirmen Gaddafi cikin sugar Jan ra’ayi na da sake dasu, ga yadda na lura ta fi son Gaddafi fiye da su Aziza, ko don shi kadai ne namiji ban sani ba. Cikin murmushi kuma ta ce, “Abu ya ya? Za ki zauna dani ne ko ko wajen Hajiya Sa’a za ki zauna wurin su Faruq?” Ni kam cikin dan lokaci Hajiya Azumi ta saye ni kaf da kirkin ta, ganin ta nake tamkar Inna ta, gata dai ba wata babba ba sosai, ga kuma kissar zama da mutane, komi nata da na ‘ya’yanta burge ni yake, yadda take nan-nan da ni sai ka ce ba ta taba haihuwa ba. Ban san sanda na ce, “Ni dai da ku zan zauna, waccan matar bata dariya”. Ta yi dariyar jin dadi ta ce “Ni kuwa zan gwada miki kauna Abu, ba za ki yi kewar Inna ba insha Allahu. Tuni an sanya ki makarantar su mutuniyar ki, da zarar Azzy ta dawo jibi da yardar Allah za ku fara zuwa”. Cikin kwanaki biyun shakuwa mai tsanani ke shiga tsakanina da Mama (yadda ake kiran ta a gidan) hatta abinci tare muke ci, in za ta tafi aiki sai ta sanyamu a gaban motar muje in an sauke ta sai direban ya dawo damu. Fadin murnar da Iftihal ta yi da zuwana ma ba zai fadu ba. Ranar lahadi da Mama ba ta da aiki daukarmu ta yi ta kai mu wajen wankin kai, ta yi mun sayayya mai yawa. A ranar ne kuma Aziza ta dawo. Farkon ganina da Aziza ban san cewa ba Iftihal ba ce, saboda kamannin su (identical twins). Yara bula-bula dasu kamar hura su ake sai ka ce balloon, da gani duk na girme su sosai, cikar hutu suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29