Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

mara gaskiya kuma munafuka, ban san sanda hawaye ya zubo min ba, nasa bayan hannuna ina sharewa duk da haka Imran na nan like a zuciyata, haka komi da yake yi bayan bani haushi illa wannan abu da ya yi mun cikin su Azizah da ya hanani kurbar ruwa cikin gidan gaba daya, duk da na san ba halayyarsu ba ce fadar abin da ba a tambaye su ba. Shi din ne dai ya shigo Iftihal na biye da shi, ya ce, “Kin gani ko abin da na gaya miki, saboda na ce ina sonta a gabanku ta bi ta kuntatawa kanta ta hana kanta sakat, nima ta hana mini. Tunda na zo gidan nan Iftihal Antin nan naki ba ta barni na huta ba, sai garani take kamar gare-gare ko kuwa juyani ya waina a tanda. Ban san me take nufi ba, ban san me take so in mata ba da zai nuna ni Imran mai so da kaunar ta ne. na yi duk iya kokari na ta saurare ni ta kiya, wayar da na kawo dominta ta rufe ta toshe duk wata kafa da zan bi in nuna mata manufata ta alkhairi ce a tare da ita”. Ya samu gefen gadon da nake zaune ya zauna, ya kai hannu ya dago habana ya ga yadda hawaye ke ta gudu, ya ce, “Jibi ki ga Iftihal, shin dama kaunar da kuke wa Anti-Abun na karya ne, da take shakkar ku? Saboda ni dai na san in dai so ne Zaynab na sona, ba tun yau ba, tun sanda ta fara kirgen dangi take sona balle yanzun? Dama so nake ku yi karatu kuma an kare, ba sai aure ba Iftihal? Yau shekaru dai-dai har uku ina rainon Zaynab a cikin raina, ina addu’ar Allah ya bani tsawon ran da zan ga karewar karatun ku, in fiddo burin zuciyata na son mallakar ta. Ki taya ni rokon Zaynab ta amshi kokon bara ta ko na samu nutsuwa, ita ma ta samu damar karasa jarrabawar ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Amma meye amfanin wannan hali da take neman jefa kanta?” Na matsa can gefe na takure cike da wata sabuwar kunyar, kamar in daura hannu aka in ce “Wayyo Allah!” Iftihal ta yi tsaki ta ce, “Kema dai don Allah Anti Abu meye haka kike yi sai ka ce wata Illiterate (jahila), mu fa ba tun yau ba mun san Ya Im na son ki, har amanarki yake bamu in zai tafi to meye wannan mummuken da kike mana sai ka ce baki yarda damu ba? Kina tsammanin zamu so Ya Im ya auri wata fiye da ke ne? Kin yi kuskure. Ko ita Azizah da take yawan yi miki zancen Mami ina tabbatar miki don kawai ta ga hawayen ki ne da kukan da kike mana cikin dare, kin dauka barci muke?” Ta fita tana dariya. Na juya na harari Ya Im da idanuwana da suka kada suka yi jawur, ya rausayar da kai cikin yi min wani lallausan kallo mai nuna yes, abin da yake fadi da wanda ‘yar’uwarshi ke fadi haka yake har zuciyarsu. Cikin kuka na ce, “Don Allah mai yasa ka yi mun haka? Ni da bakina kataba jin na ce ina son ka? Wannan ma ai sharri ne kuma wallahi sai Allah ya saka mini…..” Dariya na ba shi sosai. Ya ce, “Kina bani mamaki Zaynab, abin da baki sani ba shine, duk wani motsinki a tafin hannuna yake. Kuma tun baki da wayo nake da wayo. Maganar kina sona ko bakya sona duk a barta, na ji ni nake son ki, kuma a yau na furta. Amincewar ki kawai nake nema ba wani abu daban ba, ina fatan ranar da kuka kare jarrabawa ranar ne za a daura mana aure, don ba zan koma ko ina ba Zaynab sai tare da ke a matsayin matata (by my side) Insha Allahu. Abin da ya wuce a bar shi a matsayin wanda ya wuce a fuskanci na gaba…..” Na dago cikin murmushin takaici na katse shi da cewa, “Kana manta da wa kake magana Ya Im, ba da Mami bane da Zaynab ne. Ka shirya shiga uku ne da kake marmarin auren jarababbiya kamana?” Da sauri kuma cikin murmushi ya ce, “Na shirya Zaynab, in ma sau goma-goma ne a rana duk za ayi miki, me ake da ‘yan mazan? Ke irin ki hudu ma idan ana ciki a rana a kuma haife za ku haife goma-goma a rana daya, in dai Imran ne mijin”. Ya kanne min idonshi daya cikin zolaya yana murmushin sa mai girgiza zuciyana, na kyabe baki na ce, “Ban ga alama ba, wai Liman babu Mamu…” Da sauri ya mike ya nufo ni yana kokarin cire riga ya ce, “Eye! Me kika ce Zaynab sake fadi ban ji sosai ba, bari in nuna miki ko waye Imranan nan da kike rainawa… wayon ki kadan ne haka maganganunki ko daya babu respect a cikin su. Ko da yake mantawa na yi ke din babbar mace ce ba karama ba, tunda tun kina karama babba ce, to babu laifi yau kin samu babban namijin da zai sa ki raina kanki….” Na ga da gaske yake tubewar zai yi, sai ‘ya’yan hanjina suka hautsine, na koma lallashi na ce, “Haba don Allah Ya Im, idan Mama ta zo fa? Allah ni wasa nake….” Ya ce (yana kara dosoni) “Wannan ne kuma baki isa ba, tunda ba matse bakin ki na yi kika fadi abin da kika fada ba”. Ya wancakalar da shirt din da ke jikinsa ya rage singileti fara sol. Na dauka da wasa yake ba cirewar zai ba, na cira kai a hankali na hango wani irin ingarman kirji lullube da muscles baibaye da lallausar gashi baki sidik nannade da gurayen karfi ta ko ina. Ban taba ganin babban mutun irin Imran ba, ban taba ganin Da namiji mai halittar GIRMA irin Imran ba. Na tabbata duk abin da ya fadi babu kuskure a ciki, zai iya yin abin da ya fi hakan. Ubangiji da ya halicce shi ya iya halitta, ya kyautata halittarsa yadda ta zamo mabambanciya da ta sauran maza kwatankwacin sa. Kenan tsarki da GIRMA sun tabbata gare shi. Ganin ya nufo ni gadan-gadan yana shirin cafka ta, na ce, kafa! Me na ci ban baki ba! Zuwa cikin toilet na murza key sai karkarwa nake saboda tsabar kaduwa. Ina jiyo shi yana cewa, “Karyar banza cika bakin wofi, da ki tsaya mana ki ga aiki da cikawa, ki ga in ana haihuwa a gobe baki haifewa Abba dan jika a gidan nan gobe ba!” A raina na ce, “Allah ya tsare ni da haihuwar SHEGE!” Ashe har ya fito ya shiga kunnensa, ya ce, “Na ji abin da kika ce Zaynab, ina mai tabbatar miki in baki amince da bukatata ba wato daura auren mu bayan kammala jarrabawar ki, za kuwa ki haifi SHEGEN! In yaso daga baya ayi mana auren mu rike abin mu ko ya kika gani?” Zaynabu dai baki ya mutu, sai Uban mazari da jikina ke ta yi kamar wadda ta yi gamo. Ya yi dariya shi kadai yana fita daga dakin yana cewa, “Yarinya baki san Imrana ba, watakila sai a (foot-ball

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29