Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

abin da ya karu. Waya ce na basu kowa yana amfani da shi amma ita ta rufe nata, ko kunnawa ba ta yi ta raina kenan?” Ta girgiza kai da sauri ta ce, “A’a, Zaynab ba ta rainuwa, ko kiyashi ka ba ta a matsayin kyauta za ta ce nagode, Allah ya kara budi. Watakila dai akwai dalilinta na rufewar amma ba wannan ba”. Ta juyo ta dube ni tana murmushi, na sarda kaina kasa nima ina murmushi cike da jin dadin yabon da take yi mun. Ta ce, “Ina sauraron dalilin ki na rufe wayar da Imran ya baki Zaynab, don in yi hukuncin adalci a tsakaninku”. Na ce a hankali, “Mama firgita ni take, karar ta na damuna, musamman in ina barci”. Suka kyalkyale da dariya ban da Imran, kallona kawai yake cike da matsanancin so da kauna. A hankali ya ce, “Ai ana canza tune din, ko kuma ki sanya shi a silent ba za ya ke firgita ki ba, ko kuma ki sanya kiran sallah for your own convience”. Ranar litinin Allah-Allah nake mu fito paper in nemi Anti Rose, kuma da yake paper din Islamic Studies ne bana jin wuyar sa, nice farkon fitowa. Gudu-gudu sauri-sauri na bita hanyar fita ganin tana kokarin juya motar ta domin tafiya gida. Na daga murya tun karfina daga nesa ganin cewa duk saurina ba zan iya cimmata ba, na ce, “Anti Rose”. Ta dakata kamar tana nazarin ta inda kiran sunan ya fito, kana ta yi hanzarin juyowa ta dube ni. Lokaci guda ta kashe motar ta fito. Sai murmushi nake ita ma murmushin take min tun daga nesa. Tana karasowa inda nake kuwa ta ce (tana mai nuna ni da dan yatsanta) “Akwai daddadan labarin Imran a bakin Zaynab dina”. Ta kama hannuna har staff-room, babu kowa duk suna dakin jarabawa, muka zauna a kujerun dake fuskantar juna ta ce, “Hurray Zaynab, bani in sha”. Na yi murmushi na zayyane mata dukkan abubuwan da suka yi ta faruwa tun dawowar Ya Im, ban rage kalma daya ba. Ta ce, “Thank God! Na kuma gode miki da baki yi saurin amsawa ba. Hakan ma wani abu ne da zai kara miki matsayi a zuciyarsa. Ki ci gaba da kin amsa bukatar shi har sai kin koma gaban iyayen ki. Idan ya biki ya cika mai kaunar ki Zaynab, sai ki nuna mai matsayin ki na cewa ke talaka ce, kasa da shi. Kina gudun wulakanci. Idan ya ce ya ji ya gani yana son ki haka, Zaynab ki yarda da Imran ku yi auren ku, ina muku fatan alkhairi”. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mun baro Katsina ranar Lahadi, kai tsaye muka zarto Kanon Dabo, yaro ko da me ka zo an fika, mai Dala da Gwauron Dutse, tushen Maguzawa ta Dabo tumbin giwa. Kwanan mu biyu a gidan Baba Sa’idu na Kano dake Sultan Raod sannan muka tattaro muka yo Gwarzo. In ba don idon Abba ba, da Hajiya Sa’a da iyalanta ba za su Gwarzo ba iyakacinta Kano, domin ita a gareta takura ne zaman kauye ai sai dole. Amma shi Abban baya ganin haka. Kar ku yi mamakin jin cewa Hajiya Sa’a ‘yar Gwarzo ce ‘yar kanwar Inna Dubu da aka rike a gidan Malam Ali, domin iyayen Dubu talakawa ne futuk amma duk sun rasu. Don haka Dubu ta daukota ta rike. Shi kuma Abban a rayuwarshi ba shi da kamar Malam Ali, a shirye yake kuma da ya bata da kowa in dai a kanshi ne, daga ‘ya’yan shi har matan shi ya sha gaya masu wannan. Don haka wannan lokacin take taka-tsan-tsan. Ita dama ‘yar dakin Innar Faruq ne, don haka can suka sauka da ‘ya’yanta. Ni da su Mam, ‘yan biyu da Gambo muna dakin Innana dake ta faman makale ni kamar ta maishe ni ciki. Yau abin da sauki tunda kuwa ban ga ta hana su Iftihal shiga dakinta ba, ko don ganin idon uwarsu ne, oho! Ko kuma ‘yan mutuncin ne a kanta? Na danganta hakan da dokin zuwana da take, domin na yi dadewar da ban taba yi ba har watanni shaida ban zo ba. Rabi da Mama sun barke da hirar yaushe gamo wadda duk rabinta labarin rayuwata ne da ke burge kowa, yake kuma baiwa kowa sha’awa a can Sokoto. Ta ce, “Zaynabu-Abu uwar addini ce, ban taba ganin yarinya Abida (mai ibada) irin Zaynabun ki ba”. Inna ta kara janyo ni ta rungume tana murmushi dadi ya cika ta. Don ba abin da take so a rayuwarta irin ta ji ana yabon Abun ta, Kyautar ta, Kyautar Allah (kamar yadda take cewa). Sai na samu kaina da kara godiya ga Allah da ya kare ni daga aikata ZINA, kamar yadda zuciyata da gangar jiki ke so, har suka so su ja ni. Wannan ya samo asali daga addu’ar da Malam yai min a sanda aka haifeni a al’aurata, domin kariya daga aikata zina. Aya ta ( ) cikin Suratul-Maryam. (Don haka iyaye a dage da kula da ita wannan addu’ar a yayin da aka haifi yaro, to insha Allah ba dai ya aikata zina a rayuwarshi ba). Na tabbata da na karya zuciyar Inna Rabi, fiye da wanda ta samu kanta a gaba dayan tsayin rayuwar ta, wanda ni ba zan ce ga shi ba. Da duk wannan kaunar da take mun, ta koma kiyayya, watakila irin kiyayyarta ga BABA SA’IDU. Sai na samu kaina a mai tambayar kaina, wannan na nufin BABA SA’IDU ya aikata ZINA ne shi yasa ta tsane shi? To da WA????? (Wa’iyazubillahi). Wama taufeeqee illa billahil aliyul azeem…. Kada Allah yasa tunanin nawa na banza ya zama gaskiya, kada Allah yasa tunanin nawa na wofi tabbatacce ne. ya Allah ka fitar mun da wannan mugun tunanin a zuciyata…. Allah ka dube ni, kasa tunanina ba gaskiya bane rudin shaidan ne. Ba abin da ke dadadawa Innana kamar ganin yadda nake girma da wani irin murjewa, kai ka ce irin Larabawan nan ne na Lebonon. Duk na fi ‘ya’yan Farfesa daukar ido da kwarjini, haka duk kalar kayan da nasa kyau suke min su kuma amshe ni kasancewata jajur, masu tsada ne ko akasi, kai ka ce don ni aka kirkire su. Ni Zaynabu-Abu shiru-shiru ce, bani da kwaramniya, kuma bana sonta. Da wuya ka ga ina magana in ba a kan abu mai muhimmanci a gareni ba. Sun baro Gwarzo bayan motarsu cike da tsarabobin da suka saba komawa dasu, wato kamar su man shanu, garewanin man gyada, kindirmo, madarar shanu, kwan kaji da na zabbi da sauransu. Wannan karon har kajin gidan gona ishirin Malam ya ba su Hassan, amma an fige an gyara ya kuma ba Haydar takwaransa dan maraki, Abba ya ce a bar shi a nan a kiwata masa. Ni da su Azizah bamu so rabuwa ba, don dai ina son samun lokaci da Innana ne su kuma sun kallafa ran su a son zuwa Porthearcourt, akwai tambayoyi da dama da nake son in yiwa inna, musamman a kan irin gore-goren da su Hassan ke mani a shekarun baya, wanda wancan lokacin karancin shekaru da rashin wadatar hankali bai barni na kuma waiwayarsu ba, sai yanzu da hankali ya zo mini nake ganin hakan

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29