Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

kullum. Kaduwar da sassan jikina ke yi yanzu, wane na daren jiya. To a haka aka kare cin abincin ba tare da na ci wani abin kirki ba, haka tunda na dukar da kaina kasa ban dago ba. Idan akwai abin da nake son gani, nake kuma gujewa ganin nasa, to Imran ne. ba don komi ba sai don abin da hakan yake haddasa min a cikin gangar jiki da tsokar zuciyana baki daya. Karfe tara na dare ana falo har Abba ana kallon network news amma ni ina uwar dakinmu dukunkune cikin bargo, ga littafin assignment dina a gabana na kasa hassala komi sai fama da abin da ya dameni. Zan so in samu wani ya fassara mun ma’anar wannan abu dake damuna. Abin bakin cikin shine, ni bani da kawa, su Azizah duka yara ne na girme su, ni kaina ban san mene ne ba balle su da na kere sosai a shekaru. Kaduwar da jikina ke yi shi ya haifar mun da zazzabi da sarawar kai, haka abin da na dauka ciwon mara ke karuwa mini. Ga (assignment) din da na tabbatar in ban yi shi na bayar a gobe ba na rasa C.A dina na darasin physics, amma bai dameni ba kamar wannan ciwon Imran da Allah ya dora mini. Hawaye masu zafi suka soma biyo kuncina, na kara kudundunewa tamkar curin alkaki, haka al’amarin yana kara habaka a tare dani. Imran sanye da farar shirt (DKNY) da shudin wandon (Jeans) ya shigo falon, ya zauna ana kallon da shi ba don kallon ne ya kawo shi ba. Ya mike tsaye cikin damuwa ya zura hannunshi cikin aljihun bayan wandon shi kamar mai laluben wani abu, yana kallon su Azizah suna ta shewar su, ya hanga ya duba iyakar ganin shi bai ga mai rikirkita shi ba a ‘yan kwanakin nan. Cikin mamakin rashin ganin ta da yake cikin jama’ar gidan a dan tsukin ya ce, “Azzy ina Zaynab ne?” Iftihal ce ta amsa masa da cewa, “Tana can daki an ba ta assignment ta kasa shine take yi tana kuka”. Ya ce, “To ku baku taimaka mata in kun iya?” Iftihal da Azizah suka dubi juna suka kama baki, can kuma suka hadu suka tintsire masa da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ya shaka, ya kulu, kadan ya rage ya yi kwallo dasu. “Mama ki ji Yaya Im don Allah, mune ma masu koya ma Zaynab karatu?” Mama ta ce, “Zainab ce malamar su Azizah ai, in ta iya su koya a wurin ta, in ba ta iya ba duk haka suke lalacewa”. Hajiya Sa’a ta kyabe baki, saboda neman fitina babu wanda ya sako ta cikin zancen su, amma sai cewa ta yi, “Ai tsiyar ‘ya’ya mata kenan duka tumaki ne, duk ba kwakwalwa sai ta shashanci”. Mama ta wani irin juyo ta dube ta, ta bude baki za ta yi magana Abba ya daga mata hannu ganin yadda yaran suke kallon su, ta yi shiru tana ciccika tana batsewa, kiris take jira ta yi kuka. Wannan dabi’ar Hajiya Sa’a ne, babu yadda za ayi a zauna da ita a tashi ba ta san abin da za ta ce wanda zai bakantawa Azumi ba, ko da kuwa ta cikin ruwan sanyi ne. Ita kuma Azumin ba hakuri, ba ta barin ko ta kwana da an tabo ta za ta hau suyi sama suyi ta yi kamar sa cinye juna. Shi kuma Abban ya zuba ma takarda ido yana rubutu kai ka ce dabbobi ne ya aje ko dagowa baya yi balle ya san suna yi. Ya kan ce cikin zuciyarshi mace daya ce ta ishe shi duba a duniya, mace daya ce ta isa ya daga ido ya dube ta ya ji sanyi a zuciyarsa kuma ta yi mai nisan da har abada ba zai kamo ta ba. Ta tafi da duk wata soyyarshi a kan diya mace. Don haka duk wata mace kallon ta kawai yake a dage, a kaskance, a hagunce, ma’ana ba ta da abin da za ta burge shi da shi har ya bata muhimmin lokacinsa a kanta. Sai zaman aure domin neman lada gami da kariyar kai daga dattin zina, da rainon ‘ya’ya wanda wannan daman dole ne. Ya dago ya dubi Imran idanunshi sun kada sunyi jazur da tunanin wani al’amari mai GIRMA da ya taba zuciyarshi, ya ce da karfi, “Dan Abba! Jeka koyawa Zaynab assignment”. (Kuskuren da iyaye ke yi kenan, musamman iyaye ‘yan boko da attajirai, kan dauki kebantuwar ‘ya’yansu mace da namiji baligai ba a bakin komi ba duk a cikin wayewar ne, wanda ko Annabi (S.A.W) ya fadi mana kebancewar mace da namiji, na ukun su shaidan ne, musamman ga ita Zaynab, da Abban ya yi tunani bai dace ya yi hakan ba, tunda shi da bakinsa ke yi mata nasihar mu’amala ko ya ya da namijin da ba muharraminta ba). Tamkar ya yi mai susa a inda ke yi mai kaikayi, da sassarfa ya nufo dakinmu. Har zuwa lokacin kwance nake kudundune cikin bargo ga littafin a gaban filon da na ta da kai da shi, idanuwana cike da hawaye amma basu kai ga zubowa ba. Daga bakin kofa ya dakata ya tokare a jikin kofar da hannunshi na dama kafafunshi na daga waje ya ce, “Zaynab mene ne haka? Cewa aka yi in baki iya assignment din ba korar ki za ayi daga makarantar?’ Shiru na yi masa tamkar da littafin yake magana, don ban san me zan ce masa ba. Shirun shine mafi alfanu. Ganin haka ya karasa shigowa dakin gaba daya, ya ce, “ki tashi na ce, ki tashi ki zauna Allah tun ban kwaye bargon ba”. Nan ma ba amsa, sai ido da na bishi dasu, luuu! Wadanda suka kankance suka yi jawur, tamkar an gumbuda musu barkono. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ya yi tsai da ransa cikin son karantar me ke damun Zaynab? Ko me Zaynabu ke ciki? Ba tare da tunani ba kuma ya janye bargon ya wancakalar. Subhanallahi! Ba shiri ya mai da mun abuna saboda kananun (minis) da ke jikina. Ya juya mun baya da sauri cikin rawar murya yana fadin, “Ki tashi ki sa kaya in koya miki assignment din. Ki tashi tun baki yi sanadin da na idasa kai hannu gareki ba, wannan hawayen da kike zubarwa Zaynab ba zan iya jurarsu ba. Zaynab ya kike so in yi da raina? Kin hana mun ganin kyakkyawar fuskarki, kin haramta min jin lafuzan ki masu taushi, kin hana mun barci yanzu ma a ido biyun kina so ki mai dani wani zararre, haba Zaynab! Ke wace irin yarinya ce mara tausayi da halin ko in kula……..” Baki na saki galala! Ina jin abin da ko a mafarki ban taba yin na zan ji hakan daga Imran ba, ko a tunani, ban yi na wai Imran zai taba fadin hakan gareni ba even in my imaginations! To ko shima irin ciwon nawa ke damunsa? Bai san halin da nake ciki duk a kansa bane? Bai san duk wannan kukan ba na assignment bane na rashin abin da zuciya da gangar jiki ke so ne, wato shi YA IM, da nake ganin har abada ba zan samu ba. Still

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29