Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

tamkar wani barazana ne ga mutuncina a nan gaba. Mun kwanta ne da daddare, sauro ya gallabe mu, duk kuwa da maganin sauron da muka kunna da (Rambo) da na fesa, amma ni ko jin cizon suron bana yi balle in sosa, abubuwa ne da yawa ke damuna a zuci. Wurin karfe daya na dare na ja tsuka “Tsut!” don tuno shekarun baya. Ashe Inna Rabi barcinta ba wani nisa ya yi ba, ta ce, “Ke in wani abu ne ya dame ki, ba kya gaya mun? Haka kawai ki bi ki isheni da tsaki cikin dare”. Maimakon in amsa mata sai tsakin ne (by mistake) ya sake subutowa daga bakina, na ce, “Kai abin ne ma Inna na kasa ganewa wallahi”. Ta ce, “Can gidan Baba Sa’idun naki, fi sauran-Babanni ne kike da matsala ko-ko satittikan da za ki yi mana ne kike ganin kyashin su, kin baro A/C sauro na cizon ki? Abin da na guda kenan ai tun farko Kyauta na hana tafiyar ki hannun su Azumi, amma Malam bai saurare ni ba, saboda dukkanku baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba sai SA’IDU. Sa’idu ya fini GIRMA a idanun ku, komi Sa’idu ya ce shine dai-dai, amma Rabi ai MAHAUKACIYA ce…..” Wasu hawaye suka balle min, na ce cikin rishin kuka, “Ki daina gaya min haka Inna, wallahi-wallahi a kowanne hali, a kowanne matsayi babu inda ya fiye mun dakin nan naki kwanciyar hankali. Babu inda nake ji na sake, freely, cikin walwala da kwanciyar hankali tamkar nan. Bani da wanda ya fiki, bani da wanda nake so fiye dake. Baba Sa’idu bai taba daukar ki matsayin maras hankali ba, ke ce dai kike zaton haka. Ya sha cewa inda mai hankali a duniya to ke ce, in da wanda zan dage wurin bin maganarsa to ke ce, in da wanda ta san ciwon kanta a duniya to ke ce. Abin da ke damuna kwata-kwata bai shafi abin da ke kike tunani ba. So nake in tambaye ki ashe mu ba Fulanin Gwarzo bane? Kuma meye BARAROJI? Mene ne SADAKA-YALLAH?????” Inna Rabi ta mike zaune a nutse ta yi murmushi. Ta mika hannu ta latsa makunun wutar lantarki dakin ya gauraye da haske, iare-iren wadannan gorarrakin ita ma ta sha su wurin kishiyoyinta a zamanin kuruciyar ta, ta kuma tabbata watan-watarana za a yiwa Abun ta. To amma ba ta zaci tun yanzu ba, ta dauka sai a gidan aure ko lokacin aure. Ba ta san daga inda ya fara fitowa ba, don haka ta ce, “Shin wa ke ce da ke hakan a gidan Sa’idu?” Na ce, “Maganar fa ba ta yau ba, tun farkon zamana dasu ne. kuma tun lokacin Baba ya saba musu basu sake ba. Ita Hajiyar ma yanzu ba ta shiga harkata kowa zaman kansa yake a gidan, babu mai shiga shirgin wani. Ita Hajiya Sa’a ta gayawa su Hassan suka samin kahon zuka a wancan lokacin, wai suna kyankyami na saboda mu BUZAYE ne, kazame. Su tofar da miyau, suyi amai wai BARAROJI babu wanda ya kaimu kazanta. Sai nake jin tsoron ko wani ciwo ne hakan abin kyama”. Inna Rabi ta hasala ta ce, “Ita Sa’ar har tana da bakin gaya mun haka? Tana da bakin ce dake SADAKA-YALLAH ba ta fadin babban? Koma meye ta ce a yanzu ai duniya ce, ita din kuma makaranta ce babu abin da ba za ka gani a cikin ta ba. Wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran, kuma tarihi MAIMAITA KANSA yake, sannan kowa ya kwana lafiya shi ya so. Idan a yau na ga dama wallahi ba za ta kara jin dadi a rayuwarta ba, daga ita har Sa’idun da take takama da shi, domin GIRMANSU YANA HANNUNA, yau ne ko gobe in na ga dama sai in FADAR DA SHI, in ga karshen kudi da boko, wadanda basu da amfani idan babu mutunci a idon duniya. To amma ba zan yi hakan ba saboda wasu manyan dalilai, akwai ranar da dubunta za ta cika. Tara su nake daga ita har Sa’idun ina jiran ranar da wani a cikinsu zai wulakantaki, ina jiran ranar da zai nuna fifiko tsakaninki da ‘ya’yansa….” Sai kuma ta razana da ta fuskanci ko da wa take magana, Zaynabu ce ba Au ba, da cikakkar budurwa mai hankali take magana ba Kyauta-Abun d ata sani a baya ba ce,. Ta yi hanzarin gyara zancenta da cewar, “Zaynab mu ba Bararoji bane. Sune ‘yan kasarmu dake daji, mu ‘yan kasar Niger ne ‘yan uslin wani gari DAMAGARAM, amma iyayenmu da ‘yan’uwanmu duk a babban birnin Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can. Mahaifinmu fitaccen dan kasuwar fata ne da ya yi fice a Niger, kuma mashahurin dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama a gwamnatin Damagaram, wanda gab da rasuwarshi yake dan takara mafi rinjayen magoya baya da suka tsaya neman kujerar gwamnatin Damaragam. Duk dangina suna Niamey, ba fakiri ko daya, bamu taba yin talauci a rayuwarmu ba, bamu san shi ba ni da iyaye da dangi na gaba daya. Kaddarar aure da rabon haihuwar ki ya kawo mu Najeriya mu da mahaifinmu da kanwata NURATU da ta bata a hanuna. Batan Nuratu ne ya hanani komawa gida, ya hanani neman dangina har yau don ban san me zan ce musu a kanta ba, kuma rashinta ne ya tsomani a halin da har yau kike ganina a ciki ake min kallon MAHAUKACIYA ko TABABBIYA. Su kuma danginmu basu san inda muke ba, don mahaifinmu rasuwa ya yi a sanadiyyar hadarin jirgi a kan hanyarshi ta komawa gida, ya gaya masu cewar ya aurar dani ba da saninsu ba. Ki taya ni addu’a Allah ya bayyana min Nuratu, ni kuma na yi miki alkawarin a ranar da na ganta a ranar ne zan sadaki da danginki na wurin uwa. Sai kin raina zamanki da su Sa’ar da ke ce dake SADAKA-YALLAH, sai dai ki basu SADAKAR ki wuce. Idan kika shiga Niamey ko Damagaram kika ce kina neman wani da ya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan. Ki yi hakuri ki kyale ta, akwai dalilin da yasa ba ta son ki, ba kuma za ta so kin ba har abada, illa ta boye hakan a ranta don amfanin kanta, amma ai……” Ta sunkuyar da kanta. Ta dade tana kallon kyawawan yatsun hannunta, can ta dago ta ce, “Ke Zaynab kada ki damu kanki a banza, da dangin Uba ai ake tutiya ba na Uwa ba, ko ta isa ta ce da Malam SADAKA-YALLAH? Ni ta fada ta more, akwai ranar da GIRMA ZAI FADI!” Na yi shiru ko kwakkwaran motsi bana yi, sauraron Innana nake da dukkan hankalina. Ta ga akwai alamun rashin fahimtar wasu abubuwa cikin kalamanta a tattare dani, sai ta ce, “Ke yi kwanciyar ki don Allah kada ki kara sa wannan shirmen a ranki, na ce dake da dangin Uba ake tutiya ba na Uwa ba. Kuma ni nan da kike gani, zaman jiran Nuratu nake, amma ba zaman soyayyar Malam Ali ba, ko zaman jiran Sa’idu ya dauko ya bani. Domin har yau Sa’idu bai yi arzikin da zai bani in mance takaicin da ya tusa mini ba, da rayuwarmu

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29