Chapter 15
Chapter 15
Duk hakan bai ishe shi ba sai da ya sanya su duka cikin store ya kulle, ya hana masu aiki basu abinci tun safe har yamma. Hajiya Sa’a ba ta san me ake yi ba sai yamma lis ta dawo aiki. Ta yi murna da zuwan Imranan ta da kammaluwar bautar kasar sa, suka barke da hirar yaushe gamo irin na Da da Uwa a babban falon ta. Ta nemi su Hassan ta aika su kawo mai lemu, ya ce, “Ai suna (store) ya kulle su”. Ta ce, “Dalili?” Ya yi kwafa cikin takaicin su da ya ki sakin sa har zuwa lokacin, ya ce, “Sun san yarinyar nan ‘yar Malam ba ta son mage suka watsa mata maguna ta suma, har yanzu ba ta san inda kanta yake ba”. Ga mamakin shi sai ta buga tsaki ta ce, “Shine me? Gidan Uban su ta zo, ban ga dalilin da za ta takura su ba ta hana su yin abin da suke so. In ba ta son magen ta koma gidan Ubanta mana? Sallamamme kawai ka san me ake a cikin gidan ne? A kan Buzuwar nan aurena da ubanka ya kusa mutuwa, da sai dai ka dawo ka nemo ni a kauyenmu, in baka sani ba in gaya maka dalilin cewa da ya yi in tafi kenan kwanakin baya da na gaya maka a waya don sun ce da ita BARAROJI, ko ka bude min yara yanzu-yanzun nan ko in sabar maka wallahi”. Ba musu Imran ya bude su Hassan domin dai shi mutum ne mai biyayya da baya saba umarnin iyayen shi ko ya ya ne. Ya samu Faruq a dakinsu yana cin abinci, ya zauna bakin gado ya dafe kai ya rasa abin da ke mai dadi, anjima kadan ya yi tsaki ya girgiza kai duk sai ya ba Faruq dariya. Ya ce, “Kai Imran ya ya za ka yi when you become a father? (in ka zama uba) baka san sha’anin yara bane?” Imran ya sake yin tsakin ya ce, “Ni ba wannan ke damuna ba, maganganun Hajiya ne ban ji dadinsu ba, ban gane inda ta dosa ba. Ita fa babba ce, da ya dace ta dauki kowa nata ne a gidan nan, duk da dai na san ita mai nuna son ‘ya’yanta ne, amma saboda Allah su Hassan basu yi laifin da suka cancanci a hukunta su ba?” Faruq ya dafa kafadunshi cikin murmushi “Common dear, don’t talk about this matter again, plz…” Shima sai ya share zancen bai kuma yin shi da Faruq din ba, to amma sai ya rika jin nauyin Faruq din ta yadda zai ga mahaifiyarshi a matsayin maras tunani, ga Faruq din shi bai dauki al’amarin wani serious ba ma. Kwana biyu na warware case din mage ya wuce, sai dai cike nake da tunanin mene ne BARAROJI mene ne SADAKA-YALLAH? Wannan tambaya ce da ta dade tana cina a rai, na kuma rasa wanda zan yi mawa, don haka da na ga abin ya fi karfin tunanina, dole na yakice shi karfi da yaji. Imran dogo ne baki kakkaura, sai dai bai kai tsayin Faruq ba, amma ya fishi kauri da fadin kirji (physique), yana da kyakkyawar sura sosai, ya aje zagayayyen gashin baki dan siriri wanda ya tafi ya hade da kauraran zagayayyun lebban shi masu sulbi. Yana da hakora masu haske, jerarru kuma masu sheki. Komai nashi attractive wato mai daukar hankali ya dube su ko da bai yi niyya ba. Kallon yanayin fatar jikinshi kadai ya isheka kimanta irin hutu da jin dadin da yake ciki, haka idanunshi za su nuna maka tsantsar ilimin da ke cikin su. Ba a fiya son mace mai kamun kai ta fiya sanya idanun ta sosai a kan maza irin Imran ba, domin ba wuya za a aikata zinar ido. Wanda kuma shi abin ya zo ne da halittar shi ba wai da gangan yake yi ba. Yana da yawan amfani da karamin gilashi (medicated) ba don lalura ba sai don kara karkon idanu, haka nan Imran baka raba shi da cin biskit din nan na alkama (hob-nobs), yana da fada sosai kamar barkono, amma in ka fahimce shi ya fi ruwan sha saukin sha, raini ne baya so. Shine babban da a ‘ya’yan Farfesa, sun haife shi a kasar England zamanin da shi Farfesa yake karatu, inda ya samu ilimin firamare da sakandire. Don haka ne in yana lallausar Turancin sa ba za ka so ya daina ba. Sai bayan haihuwar shi da kimanin shekaru goma, sannan aka haifi Hassan, Rufa’i ya biyo baya sannan Jauhar da dan karamin su Aliyu da Baban ya sanyawa sunan Malam Ali, suna kiran shi Haidar. Sai da ya fara aiki a UDUS ne ya auri Azumi, wadda take basakkwata usul, kuma diyar wani abokin shi Farfesa a nan Sokoto wai shi Dr. Isma’ila Taura, ya ganta ne ranar ba da shaidar (Degree) ga daliban shekararsu da matsayin da ta fito da shi ne (best overall student in MBBS) na shekarar su baki daya. Yana daukar lasifika abin da ya bude baki ya ce a filin taron shine, “Idan Azumi ba ta da aure shi V.C zai aure ta, wannan kawai shine kyautar da yake jin zai ba ta ya nuna kwazonta a duniya. Ba kuma tare da ya ganta ba, tsohuwa ce ko yarinya ce?” Gaba daya filin taron rudewa ya yi da sowa, masu ihu na yi, masu kabbara na yi da sanyawa abun albarka. Babanta ne ya shige mai gaba ya ba shi auren ta. Ita kanta ta san ba karamar sa’a ta yi a rayuwar ta ba. Imran da Faruk na tare tun daga farkon karatunsu na Jami’a, wato tun dawowar Faruq Sokoto, sun shaku sun kuma amince da juna, domin halayensu duk kusan daya ne, daman an ce wai sai hali ya zo daya ake abuta, wannan haka yake. Halayensu duk kusan daya ne, nutsuwar Imran daban take da ta sauran ‘ya’yan Farfesa, mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, yana adawa sosai da aqidun Malam Bature, yanayin rayuwar shi na Sokkotawan usli ne ziryan, hakan yanayin sutturarshi shadda ne, caftan ko babban riga a kullum, kai ka ce wani magidanci ne, da wuya ka ganshi da wani kaya ba shadda da hula ba, ra’ayinshi kenan. Bayan kammala karatun su sun samu an yi posting din su gari daya yin bautar kasa, wato jahar Abia, duk da ba fanni daya suka yi karatu ba, shi Imran ‘civil engineer’ ne. Sanda na kai aji hudu a sakandire duk wasu alamomin girma na ‘ya mace sun soma bayyana a jikina, da yake ban fara karatun sakandire da wuri ba, ni kaina na san na sauya wane shekarun baya. Abin nufi, halittar jiki da tsarin rayuwa. Zan iya kimanta shekaruna goma sha biyar a lokacin, mun yi sabo sosai da Imran duk da cewa ba zaman gidan suke ba suna fafutukar neman aiki. Ba zan manta da yadda sunan “Abu” ya bace min a shekarar ba, ta dalilin Imran. Ya dauko mu ne daga makaranta yana tuki ina gaban mota, ya ce, “Shin wai ke ya sunan ki ne?” Na dube shi galala! Baki a bude ciki da mamakin wai duk kiran nan da ake Abu-Abu bai san sunana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29