Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

ba? Wannan ai rainin hankali ne, don haka na juyar da kai ban amsa ba. Daga bayanmu Iftihal ta ce, “Kai Ya Im, da gaske baka san sunan ta ba?” Ya ce, “Gaskiya ban sani ba, na ji dai kuna cewa wani abu wai “ABU”, ni ko na san kyakkyawar yarinyar kamar wannan kallo daya za ayi mata a san ba sunanta Abu ba”. Gaba daya suka tintsire da dariya, ni ko na yi murmushi kawai. Ya kafa mun ido kamin ya mai da hankalin shi a titi cikin son karantar karbar da na yiwa zancensa. Na kalli can wani gefen daban, cikin raina ina cewa, gaskiyan Iftihal ne, gaskiya ne ba mutun irin Yayan ta! Komi nashi mai ban sha’awa ne, hatta furucinsa. Azizah ta ce, “A school ma ba a ce da ita Abu sai Zainab”. Ya ce, “That is good, ZAYNAB, daga yau cikin ku kada wanda ya sake ce da ZAYNAB (ABU)”. Wannan shine mafarin al’amarin. (Takori). **** Na kwanta a daren nan ina maimaita kalmar “ZAYANB” da Imran ya ambata, na fadi ya fi cikin carbi, amma ban ji na fadi dai-dai ba irin yadda shi ya furta. Na yi tunanin abubuwan da suka faru a ranar tare da Imran na kasa mantawa. Idanuwanshi suka sanya zuciyata cikin wani sabon al’amari da ban taba tsintar kaina ciki ba. Na yi kokarin in yakice Imran a zuciyata na kasa, inda duk na juya shi ke zuwa cikin idanuna. Na ji wasu sassa na jikina suna wani irin kaduwa da ban san na mene ne ba. Marana ya kulle tamau kamar zan yi fitsari, don haka na rarrafa zuwa (toilet) na yi ta kakalen fitsarin amma bai zubo ba. Na dawo daki na kwanta a dandaryar carpet, na ware fanka da A.C amma ban daina zufa ba. Wannan al’amari ya tsoratani, domin wani al’amari ne sabo a gareni da ban taba tsintar kaina a ciki ba, ban kuma san ko mene ne ba. Hawaye ya zubo min ina kallon su Azizah dake ta barcinsu cikin kwanciyar hankali, na rasa abin da ke min dadi, na rasa mene ne shi wannan abun, haka na rasa me zan yi ya gusar min da wannan sabon abu da nake ji cikin jikina har kuma cikin kwakwalwata. Wannan shine mafarin shigar rayuwata cikin gararin da har yau take ciki, cikin halin bakin ciki da dakacen ina ma ba a haifeni ba. Da ban hadu da Imran ba, watakila da rayuwata ta ci gaba da garawa a yadda take. Wato ba bakin ciki ba kuma farin ciki, sai godiyar Allah. Haduwata da Imran shine silar warwarewar al’amuran rayuwata da na Innana da suka shige min duhu, suke damun zuciyata tun ina kankanuwa. Har ila yau, Imran din ne sanadiyyar rushewar farin cikin rayuwata. Wata zuciyar ta ce dani, wannan al’amari da ke neman samuna ba alheri bane a tare dani, don haka in nemi tsarin Allah. Wannan ita ce tarbiyyar da iyayena suka dora ni a kai, wato duk wani abu da ya fi karfin iyawa ta, ya fi karfin sani na, ya fi karfin kariyata to in nemi tsari da kariyar Allah, domin shine mai iko a kan komi. Sai na mike ina layi na yi bayan gida, na dauro cikakkar alwala na yi (brush) na fito na suturce jikina na fara sallah, a cikin sujjada ta ina rokon Allah cikin yi masa kirari da ya yaye min wannan matsala da ya daura min a kan Imran, ya kawo sanadin da Imran din zai bar gidan gaba daya in huta. Washegari na tashi da azumin tadauwa’i a bakina, kasancewar ranar Alhamis ce dama na kan yi azumi litinin da alhamis. Wallahi sai na ji ni sawai, kaman an yaye mani. Na yi ta yiwa Imran boyo cikin gidan har aka sha ruwa, gani nake kamar idan ya kalli kwayar idona zai karanto abin da ke damuna game da shi, wanda ya hana mani barci daren jiya. Wannan ya faru ne tun ina da shekaru sha biyar a duniya. A daren Imran da Faruq na zaga gari cikin motar Imran din, Faruq ya ce, “Yau tun safe ban ga Abu na ba, na shiga sassan Mama ya fi sau biyar ban ganta ba, ina cikin damuwa wallahi”. Imran ya yi murmushin da shi kadai ya san dalili yin abin shi, amma bai ce komai ba. Ya yi parking a wani katafaren shopping complex suka shiga tare, shi Faruq ya dauka biskit din nashi zai saya da baya rabo da saye. Don haka shi ya yi wani barin can daban yana saye-sayen shi. Kafin ya zagayo inda Imran yake, ya ganshi ya cika kwando taf da kayan shafa na mata (designers) yana jujjuya kwalbar turaren cool-water watau (Davidoff) a hannun shi, turare ne mai sanyin kamshi na ‘ya macen da ta san sirrin da ke cikin turare. Sai daga baya ne ya dauki kayan shaving din shi da biskit din nashi na (Hob-Nobs) ya yi gaba ya bar Faruq da baki bude. Mamakin Faruq yaushe Imran ya yi budurwa bai sani ba? Ina ya je shi kadai ba tare da shi ba har suka hadun? Imran S. Bindawa, tamkar ya san me Faruq din ke sakawa a ranshi, sai ya yi murmushi ya kanne mai idon shi daya cikin tsokana, ya ciza lebbanshi masu sulbi, ya matso dai-dai kunnenshi ya ce, “Don’t be nervous mana (kada ka ji tsoro) ba kowa na sayawa ba face kanwata, ZAYNAB”. Ya yi gaba ya barshi nan yana mai son convincing zuciyarshi ta yarda da abin da take ji, amma zuciyar ta ki yarda, karyatawa take da cewa, ba ZAINAB ya ce ba ZUBAIDA. Da Imran din bai yi gaba ya barshi ba, da ya ji irin hautsinawar da ‘ya’yan hanjin shi ke yi, da kukan da akuyar cikinsa ke yi. Ya kuma ga kallon firgicin da ya bishi da shi da gumin da ke ta yankowa daga kowanne sako a jikinshi. Ya shiga gyada kai tamkar kadangare yana girgizawa, yana gayawa kanshi cikin lallashi cewa, ba da wani nufi Imran ya fadi kalaman shi ba, ba da wani nufi Imran zai yiwa Zainab kyauta ba, abin da yake kokarin fahimta ba shine ba. Zumunci ne kawai da alkhairi irin nasa, domin shi mutum ne mai alheri ga kowa ma ba Zaynab kadai ba. Abinci ake ci bisa makeken dining din gidan, to amma me? Imran idanun shi kyar bisa kyakkyawar fuskar Zainab, tana kai lomar ta a nutse ba irin su Aziza ba hannu baka hannu kwarya. Idan tana tauna kumatunta duka biyu da tsakiyar habarta lotsawa suke ciki sosai. Komi nata a yangace amma naturally ba wai tana sane take yi ba, yana tafiya ne da halittar Ubangiji. Sanye take da doguwar riga fara sol, ta matse dogon gashin kanta daga tsakiya da farin ribon ya sakko ya kwanta lamban bisa dogon wuyan ta kamar na barewa. Zainab a mike take sosai ga kuma alamun ‘mace’ dake neman bayyanuwa a jikin ta daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya kasa cin abincin sai ko juya cokali cikin farfesu? A bangarena, nima ba cin abincin nake yi ba, bugun da zuciyata ke yi a duk lokacin da na ga Ya Im, na yau har ya fi na

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29