Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

ki, koyaushe kuma sai ya yi tafiyarsa. Yau ne da na ji Baba zai zo na ce zan biyo shi tunda Aziza ba ta nan, shine ya taho dani”. Inna Dubu ta wanke min dattin raina da cewa da ita “To ina kika baro Baban?” Ta ce, “Yana zaure tare da Malam din nan gidan, amma ya ce komawa zai yi, nice zan kwana tare da Abu, idan zai koma jibi zai zo mu tafi”. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mafari kenan da wannan ya sayo min tsana mai tsanani a wurin Hajiyar su Hassan da iyalanta, sai da na gwammace dama Abba bai ji al’amarin ba. Tsakanin mace da mijinta sai Allah, bamu san ya a kai suka shirya ba, mun dai gansu kuma sun hade abinsu. Amma Mama ta ce take jin Imran (dan lelen Abba) ne ya yi waya ya ba Abban hakuri. Na sha kimantawa raina ko ya Imran yake? Yadda abin ya bayyana a gareni shine, duk gidan kowa na son Imran, babba da yaro kowa bakin shi baya daina ambaton (Ya Im) kamar yadda na ji suna kiran sunan a takaice. Na san zai zamo mai kyawun sura kamar su Hassan, mai kyan hali kamar Baba Sa’idu. Tun ban ganshi ba na san dole ganinsa ya fi jin sa. Iftihal kan ce; “A duniya ba mutum irin Yayana Abu!”. Na tambayi kaina mai yasa shi din suke son sa, basa son kannensa su Hassan? Me yasa zai kasance na daban din, kamar yadda suke ikirari? Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa. A ganina ni ya dace in fadi cewa ba mutum irin Yayana Faruq amma ba su ba. Na kan so Ya Faruq in kaunace shi, kauna irin ta su Iftihal ga Yayansu, saboda halayensa. Faruq mutum ne mai tsarge gaskiya komi dacinta, ko da hakan na nufin ya bata maka ne, hakan ba zai dame shi ba in har ya gaya maka ita wannan gaskiyar. Ba ya shiga abin da ba ruwan shi, baya da karya, baya da daukar duniya da zafi. Babban abin da yake burge ni da shi shine, addininshi da gudun sabon Allah, a ko da yaushe yana kokarin fin karfin zuciyarshi a kan abinda take so, musamman idan ya fahimci wannan abun ba alhairi bane a gare shi. Idan kuwa aka juya ta bangaren halitta, to su Faruq sune ‘maza’ da za a kira su da wannan sunan suyi gaggawar amsawa a ko ina. Ga tsayi ga zati, irin wadanda kowacce mace za ta yiwa kanta burin mallakar su. Tunda na taso a rayuwata bani da abin tsoro irin MAGE, na tsani mage, ina tsoron mage tun ina mitsitsiyata. Idan na ga mage na kan firgita ne ko in kwalla kara. Idan kuwa ta hada yankwalallen jikinta da nawa, na kan suma ne ko in fita hayyacina, in yi ta firgita a yayin barci. Wannan dalilin ne yasa duk son kiwon mage da Malam ke yi ya hukura. Rannan muna dawowa makaranta a motar yara (school bus), dama kullum sai an fara dauko su Hassan da suke da nisa, sannan a biyo ta makarantar mu a debo mu. Mun dauko hanyar gida Hassan ya ce, “Wai Rufa’i baka san magen gidan su Na’im ta haifi ‘ya’ya har guda goma ba? Suna nan baka gani ba in suna boxing abin sha’awa”. Jauhar ya ce, “To su sammana man ko guda uku ne muyi kiwon su?” Rufa’i ya ce, “Ka ga ko Hajiya na son missa, don da tana da (Laura) da ta mutu ne ba ta sake samun wata ba”. Hassan ya juya ya ce da direba, “Maza kamin mu shiga gida juya kaimu gidan su Na’im”. Tuni Shehu direba ya cika aikinsa. Ban san sanda na fashe da kuka ba na ce, “Don Allah don Annabi Hassan kada ku amso ‘yar mussan nan”. Rufa’i ya ce, “To ‘yar iko da gidan Uban wasu, idan Malam mai almajirai ne ya sayi gidan sai ki hana mu zuba mage”. Hassan ya ce, “Bar ‘yar banza, mai bakin baki irin na karuwai. Tunda an hana mu ce da ke BARAROJI to SADAKA-YALLAH ce??? Suka bude motar da kafa fut! Suka shige gidan mataimakin Abban su. Basu dade ba sai ga kowanne dauke da farar babyn mage, in ban da mazari ba abinda jikina yake. Suna shigowa suka watso su jikina. Da na kwalla wata azababbiyar kara sai da suka razana dukkansu, na mimmike ba ko kwakkwaran motsi balle kyakkyawan numfashi. Iftihal tasa kuka ta ce, “Ai ga shi nan kun kashe ta, wallahi sai na fadi ma Abba”. Shi kansa Shehu direba ya tsorata, ya ja motar da gudu yana cewa, “Ku dai Hassan baku da kirki wallahi”. Yana sanya hancin motar cikin gate din dai-dai lokacin da Faruq ya yi parking karamar Honda Prelude ta Imran, suka fito a tare, dukkaninsu sanye da kanyan NYSC, bakin Abia, zuwan su garin kenan. Azizah ce ta fara fitowa daga motar a rude tana kiran “Ya Im!”. Shi ko Faruq ido yake warawa ya ga bullowar Abun shi, ya ga wane GIRMA da wane irin kyau ta kara, wane irin sauyin rayuwa ta samu a tsayin lokacin da ya yi bai ganta ba? Kullum, cikin sabani suke, sau tari duk sanda suka zo Sokoton daga Abia, wanda kwata-kwata ma zuwan su uku cikin shekara daya, za su tarar su kuma anyi musu hutu suna Gwarzo, sanda suke Gwarzon su kuma sun dawo Sokoto abin dai kamar shiri, amma ya faru ne cikin ikon Allah. Kuma gareni sai ya zamanto rayuwa da su Iftihal ya debe min kewar Faruq din kusan kashi saba’in cikin dari. Azizah ke fadin “Ya Im, su Hassan sun zubawa Anti Abu mage ta sume mana a motar”. Gaba daya Imran da Faruq suka yo motar, Imran ya riga Faruq dauko ni. Wannan shine karo na farko da ya daura idanun shi a kan Abun-Faruq, Abun-Baba Sa’id. Maimakon ya yi sauri, tafiya yake dauke da ita a hannun shi tamkar wanda ya taka kaya, ko ko wanda kwai ya fashewa a ciki. Ganin irin tafiyar da yake yi ne ta marasa kuzari ya sanya Faruq karbe Abun daga hannunshi zuwa dakin Mama. A ransa yana cewa, “Ashe Imran duk wannan physique nashi ragon maza ne, mace wannan kamar ‘yar shilla ya kasa daukar ta”. Mama ce ta yayyafa min ruwa na farfado tana shafa kaina tana zagin su Hassan kaman ta ci babu. Farfadowa na yi ina makyarkyata, hawaye na tsiyaya ta gefen idona, fadi nake ina maimaitawa, “Mage ce fa a cikin jikina Mama”. Ta aza kaina bisa cinyarta ta ce, “Ba wata mage, sai ni sai Ya Faruq, gashi nan ya zo”. Ni ko na dage, “Gata nan fa a hannun su Hassan har guda uku wallahi….” A ranar dai daga ni har Mama da su Imran babu wanda ya kwanta da wuri, don da na rufe ido barcin ya fara fizgana zan farka a firgice ina kiran mage. Washegari Imran ya tattara magen ya sanya a buhu ya ba Shehu direba ya ce ya mai da inda suka karbo. Ai kuwa a ranar su Hassan sun sha tafka da belt, sunyi kuka da majina, daman Imran ba daga nan ba (very-disciplined-brother).

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29