Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

so ci gaba da zama da shi muddin rayuwarki”. Yawan labarin Imran da Ya Faruk ke bani, na irin rayuwar shi da yadda yake tafiyar da ita, sai na samu kaina da son ganin sa. Bayan wata guda jarrabawarmu ta fito, inda na ci makarantar ‘yammata ta gwamnati dake garin Gashuwa ba inda na so in samu ba. Muka yi ta kuka ni da Hafsisi, sai Malam ya ce, “Me ya yi zafi? Bari Sa’idu ya zo gobe in da abin da zai iya a kai, a maida ke Kabon”. Baba Sa’idu bai zo ba sai a sati na sama, saboda ya yi tafiya zuwa Brunei. Muna bakin motarshi ya miko min wata ‘yar akwati kankanuwa mai tsananin kyau, ya ce, “Ga tsarabarki Zaynabu”. Na karba cikin mamaki ina juyata a hannuna, cikin raina ina raina ‘yar tsarabar a zuciyata, tunda kuwa akwatu ya saba ciko min da kaya a duk sanda yai tafiya irin wannan. Da kyar na bude akwatin cikin gidadanci. Wani haske ne ya dallare min ido, musamman da yake a cikin rana ne. Duk da karancin shekaruna a lokacin jikina ya yi sanyi, na san ko yaya ne wadannan zobba guda biyu ba karamin abu bane. Kuma a matsayina na ‘yar Malaminsa kawai, ban kai matsayin da zai mallaka min wannan abu mai daraja ba. Ya lura da rashin kuzarina, ya kamo hannuna muka shigo soron gidan, almajiran Malam na ta gaishe shi yana yi musu kyautar shi da baya gajiya. Sai da suka dauke kafa ya ce dani cikin murya kasa-kasa “Ko me Inna za ta yi dake, kada ki bari ta yi kyauta da zobban nan naki. Ba gwal bane, ya fi zinare daraja, kusan rabin abin da na mallaka ne. Ki kula dasu sosai, a nan gaba za su yi miki amfani”. Sun dade suna magana da Malam, inda ya yi mishi zancen makarantata. Kai tsaye ya ce, “Ai tuni ya yanke shawarar tafiya dani Sokoto, ya sanyani makaranta tare da su Aziza in ba haka ba, ba zamu taba shakuwa ba”. Malam ya shiga girgiza kai yana cewa, “Ba zai yiwu ba, Sa’idu, na ce ba zai yiwu ba. To a barshi a hakan!”. Ya tashi ya karkade babbar rigarsa ya barshi a nan a duke a kan buzu. Ya fi awa daya a hakan kamin ya mike ya shigo gidan. A lokacin Rabi na bakacen masara a fai-fai, ko kallon shi ba ta yi ba, ya russuna a gabanta ya ce, “Barkan ku da yamma Inna”. Ba ta fasa abin da take ba, haka ba ta dago ido ta dube shi ba sai bakacenta take cikin kwarewa, tana huro mai dusar masara a fuska, kai ka ce da sassaken dutse yake magana. Ina tsugunne a gefe abin yana mun ciwo a rai, na kasa daurewa sai na sa kuka. Na yi niyyar in je in kama hannunshi in mikar da shi daga wannan durkuson da ya yi kamar na mai neman gafara a gareta, kada gwiyoyinsa suyi ciwo, amma tsoron abin da za ta ce dani ya hanani. Daman a daren jiya ta ce mun, “Idan abin duniyar da Sa’idu ke kawo mana ne yasa nake neman juya mata baya, to za ta mika ni gare shi mu tafi, kuma ko a lahira kada in ce na santa”. Wannan tunani da na yi ne yasa nayi hanzarin shiga daki na kwanta a dandaryar kasa, nayi ta kukan tausayin Baba Sa’idu. A ganina duk wulakancin da Inna ke masa shi yake jawowa kansa da yake shiga sabgarta, tunda ta nuna ba ta ra’ayi meye dole zumuncin? Ko bashi da uwa a duniya ya dace ya fita sabgar Inna Rabi, tunda ba ita ke raba wuta da aljanna ba. Haka na yi ta faman mummuke ‘yar akwatun zobunana cikin bante na (dinkakken siket mai hade da shimi da ake dinkawa a kauye). Don na tabbata muddin Innata ta ga wannan akwatu, to sunan ta badaddiya, koda kuwa a ce za ta sayi duniyar ne da abinda ke cikinta. Na matsu matuka da zuwan Ya Faruk, na yi matukar damuwa da zuwansa. Abubuwan nan sun addabe ni, na kuma tabbatar babu mai amsa mini duk duniya in ba Faruk ba. Shi kadai ne zai tsaya ya fidda ni duhu, ya ganar dani al’amuran Innana da suka fi karfin hankalina. Ina zaune bisa kujera ‘yar tsugunne ina cin magarya, yayin da Innana ke kiciniyar daura sanwar dare bayan ta sauke rogon da ta dafa. A gefe Innar Faruk ke surfen gero, Inna Rakiya da Zulkiflu wani yaro da take riko suna tuyar gyada marau-marau da take sayarwa. Daga zaure almajiran Malam ne suka rude da karatu kamar sa tsaga gidan, cikin muryoyin su daban-daban, da surorin su daban-daban, ba mai jin na wani. Inna ta dan juyo ta dube ni ta ce, “Yau ba a zuwa karatun ne Kyauta-Abu?” Na ce, “Rubutun da na yi nake jira ya bushe Inna”. Wata yarinya da ba ta kai ni ba, ta yi sallama cikin sassanyar muryarta ta shigo, hannuwanta duka biyu rike da ledoji, jikinta da fuskarta kamar an wanke a inji sumul-sumul da ita kamar tarwada abin sha’awa. Gaba daya muka amsa mata banda Inna da ta juyo ta kalle ta, ta juya ta ci gaba da abinda take. Na mike da sauri na amshi ledojin hannunta ina yi mata sannu da zuwa, muka zauna bisa tabarma, sai zare ido take na rashin sabo. Inna Rakiya ta ce, “Kamar Azizan Sa’idu, ‘yar wajen Hajiya Azumi, ina abokiyar tagwaitakar taki?” Ta ce, “Ba Aziza ba ce Iftihal ce, Aziza tana Porthearcourt”. Inna Dubu ta ce, “Ikon Allah, kamar taku ce har ta baci, wa zai iya banbance ku banda iyayen ku?” Ta yi murmushi da dan bakinta mai kyau. Jin an ce diyar Baba Sa’idu ne sai na yi ta kallonta, nan da nan na ji ina kaunarta. Dan mai kaunarka, ai abin kaunar ka ne. da gani babu tambaya, ko daga yanayin fatar jikinta da irin kayan da take sanye dasu, tana kuma yanayi da Baba Sa’idu da irin Hausarshi ta Sokkotawa. Cikin murmushi na ce, “Dama ke ce Iftihal?” Ta gyada kai tareda cewa, “Wa ce ce Anti-Abu?” Na kai duba na ga Innana wadda ko juyowa bata kara yi ba. Inna Rakiya ta zuba gyada da ruwan sha a babban kwano ta kawo mata tana nuna ni, “Ita ce Zaynabu Abu, ‘yar’uwarki gata nan”. Wani uban kallo da Inna ta juyo ta yarfa mata kadai ta san ta yi laifi, ta yi karambani, ta yi ba dai-dai ba. Amma ita din sai ta yi murmushi cikin bagararwa ta kara da cewa, “Ga Innar Abu nan tsugunna ki gaishe ta Iftihal”. Ta kai gwiwoyinta kasa ta ce, “Inna ina wuni?” Sai da ta yi kamar ba za ta amsa ba, can dai ko me ta tuna? Ta daga mata hannunta na dama ba tare da ta juyo ba. Banda dai ina tsoron Inna, da na tambayi Iftihal ina Baban yake? Sai na buge da ce da ita, “Ya Faruk yaushe ya ce zai zo ne?” Ta ce, “Ai sun tafi Bindawa shi da Ya Im, amma ina jin ya ce daga can nan zai taho, kullum yana zancen ki, yana cewa zai kawo mu wurin

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29