Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Gimbiya Nafeesat Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

field) watau filin saka kwallo, ranar Innar taki, Abban naki da Ya Faruq din naki basu isa su kwace ki ba. Kuma in gaya miki ke karamar jarababbiya ce, su manyan jarababbun tsayawa suke a doka kwallon don a ga hazakar kowa, in ya so mai sa’a ya dauka, ba gudu suke suna neman mafaka ba alamar weakness (ragonta) kenan”. Bani na fito ba sai da na ji muryoyin su Iftihal suna cigiyata a dakin za su kwanta, na kasa ko da shakar kwakkawaran numfashi don yanzu su Iftihal sun zame min surukai, na rasa yadda zan yi in iya hada ido da su. Sai na jiyo Iftihal na dariya tana gulmatawa Azizah, “Allah sarki Anti Abu! Ya Im ya takurata a gidan nan, Allah ni har tausayi take bani, dazu da muka shigo baki gani ba tana ta kuka abin tausayi, yanzu zaman falo ya gagareta tana tsoron ko zamu gayawa Mama ne”. Azizah ta ce, “Ke rabu da ita, gulma ce ita ma tana son sa, baki san duk ranar da na yi zancen Mami da kuka take kwana ba? Gaskiya in suka yi sa’ar yin aure, they’ll make a perpect couple, domin sun dace da juna. Sai dai kin san ba karamin abu bane a ce Hajiya ta amince, yadda take son Ya Im da auren Mami, amma daga Abba ba za su samu matsala ba”. Na ga dai in zan kwana cikin bayin nan su ba abin da ya dame su, ba kuma fita za suyi daga dakin ba hirarsu kawai suke. Karewa ma tare zamu kwana cikin dakin, to boyon har na yaushe zan yi? Sai na share ido na murje kunyar na fito, duk suka juyo suka dube ni kamin su kyalkyale min da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ban ce musu komai ba na bi lafiyar gado na ja bargo har kaina. A sannan ne kowacce ta bi gadon ta suka kwanta suma. Dakin nau gadaje ne na ‘silver’ kanana guda uku, nawa ne a farko sai na Iftihal sannan na Azizah. Can anjima Iftihal da ta fi makotaka dani ta kwaye bargon da ta rufe kanta iya wuyanta ta ce cikin rada yadda Azizah ba za ta ji ta ba, “Anti Abu don Allah in ce wani abu?’ Na dauka tsokanata za ta yi sai na sha mur na ce, “Ki rike abunki bana son ji”. Ta yi shiru, can ta ce, “Am serious, don Allah ya ya so yake? Ina nufin ya ya za ki iya kwatanta son Ya Im a zuciyarki?” (Tana murmushi mara amo). Na lumshe ido na a hankali ina jin wata sabuwar kauna na ratsa zuciyata. Ni kaina na san son da nake ma Imran ba za ya kwatantu ba, ba shi da iyaka, kwakwalwata ba ta yi kaifin da za ta fahimce shi ba, harshena ba zai iya bayyna shi ba, domin ya fi yawan silin gashin kaina. Ta tabbatar ba za ta ji kalma ko daya daga baki na ba, (shiru ma amsa ce, amma ga mai hankali), sai ta hakura ta juya ta kwanta. Washegari ya kama asabar din karshen wata, kuma rana ce da muke sanitary watau kakkabe komi na dakin mu, mu fidda kaya masu datti mu cire yana, mu kintsa sif din mu. Wannan wani aiki ne da muka sanya kanmu bama son masu aiki suyi mana saboda baya gamsar damu. Imran yayi sallama a dakin ya shigo, turaren da ya fesa na (Gucci-Rush) ya bakunci hancinmu. Na lumshe ido zuciyana na girgiza domin ba karamin kyau ya yi ba, cikin bakar shadda ghalila. Mu kuwa ko wanka ba muyi ba. Ni sanye nake da doguwar rigar barci fara sol mai gajeran hannu, sai dai na daura zanen atamfa a kai, kaina babu kallabi, don haka murdaden gashin kaina ke dunkule cikin tufka guda a gadon bayana, rike da abin sharo yana ina sharowa. Su Azizah duk suka russuna suna gayas da shi, ya amsa yana cewa, “Zance na zo Azizah, ina fatan ban yi sammako ba?” Kunya ta kama su duka, suka dukar da kai suna dariya kasa-kasa, ta ce, “Gaskiya ka yi sammako, Anti Abu ko wanka ba ta yi ba”. Ya ce (idanun shi a kaina), “Kin san meye ne Azizah? In da kin san kyan da ta yi min a haka, da na ce ta daina wanka. Wannan Zaynabun dake tsaye gabana, ta fi mun duk matan duniya. Idan na daga ido na dubi wata mace, komi wankanta da kwalliyar ta sai in ganta kodaddiya a kan Zaynab dina. Wanka da kwalliya ba su ke sawa a so mace ba, wannan daga Allah ne. Don haka in kina tunanin hakan ki daina. Ina tabbatar miki in Zaynab za ta shekara ba ta yi wanka ba, ba zan daina sonta ba, ba zan daina ganin ta a matsayin wadda ta fi kowacce mace a idanuna ba….” Dariya suka yi suna kokarin ficewa saboda su dai basu saba jin irin wadannan maganganun ba, balle kuma daga bakin da suke matukar girmamawa. Ya ce, “Ku yi zaman ku ayi hirar da ku, watakila in ci arzikinku ta amshi kokon bara na, in kun tafi ko kallo na ba za ta yi ba. Ku taimaka ku tambaya min Zaynab, shin kalamanta masu tsada na sayarwa ne? Ko-ko kwalliyar da na yo mata ne bai burge ta ba in koma in sako?” Suka sa dariya gaba dayansu, nima kaina ban san sanda na murmusa ba, still ban juyo ba na ci gaba da abin da nake, kamar in ce da shi shin ba yanzu ka gama cewa ba kwalliya ke sawa a so mutum ba? Ya karaso ya amshi abin sharar a hannuna yana cewa, “Kawo nan in karasa miki ko kya zauna mu yi zance?” Ya dubeni cikin idanun shi cike da abubuwa da dama, na yi hanzarin zama a gefen gado saboda kafafuna dake neman kayas dani. Iftihal ta ce, “Hala baka taba zuwa zance wurin Mami ba?” Ya ce, “Eh, yes, ban taba ba, ita ne take zuwa”. Ta girgiza kai ta ce, “Ko da na ji”. Ya dube ta bayan ya aje sandar ya ce, “Me kike nufi?” Ta ce, “Na ga baka iya bane, duk da ban taba yi ba na san ba haka samari ke gayawa ‘yammatan wai sun zo zance gatse-gatse ba, abin babu ko dadin ji”. Ta zura da gudu Azizah ta rufa mata baya ita ma ta ce, “Gaskiya idan baka koyo zance ba, ba za a karbe ka ba”. Ya zauna a gefena na yi saurin rufe fuska da tafukana ina dariyar su, ya ce, “Da gaske ne ban iya ba Zaynab?” Na girgiza kai ba tare da na bude fuskar ba. Ya ce, “Wallahi ko ki bude fuskar nan ko in sumbaci hannun ki”. Da sauri na bude. Ya ce, “Ashe dai yanzu an san ni wane ne, da kar ki bude mana”. Na tsuke fuska gami da baki gaba daya, ya yi dariya ya ce, “Yi hakuri don Allah saki bakin kada fushin ki ya lahanta ni, ya jawo min asara ya dai-daita zuciyata”. Na yi wani irin murmushi a raina na ce, “Ni kuma fa? Da ka sanya tawa zuciyar cikin wata irin wahalalliyar rayuwa da

Table of Contents

Chapters

29 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29