Chapter 6
chapter5
jama‘ar wurin 'da suka' taru_ suna kallonsa. Ya
dinga Zaginsu da Turanci. " ' Wasu ko a
jikinsu,"don ba suma fahimci me yake fadi ba,
Ibrahim ne ya jashi suka shiga Mota da idonsa
jawur kamar zai zub da hawaye. Ibrahim ya
kalleSa’ ya ce, "Sabeer a dinga haquri, ba ,kullum“
za ka 'sami yadda'kake 'soba, “ Dama
tsautsayine ya sa Motarmu' tsayaWa anan
ya kalli Nura. ""‘tuqa mana mu ‘lallaba mu koma
Gida, fitar dai tayautafasu
Sabeer ya harari Ibrahim cikin fishi‘ ’yacé "Tunda.
bayanta kake bi da alama ka' ji dadin abin da ya
faru dani in kaje ka hada party Yayi wannan’
murmushin nasa ya ce "Sabeer ke nan.
Tabbas 'naji dadin abin ba don". komai ba sabo
da darasi ne na farko ga
rayuwarka.
Sai dai ba zanyi Party ba sabo da ina da abin yi
da yawa , kaine keda lokacin Party ba ni ba". '
Sabeer ya , qara qulewa yaji- tamkar ya kamashi
,da duka, sai dai ba ‘zai iya hakan .ba sabo da
matsayinsa‘ da girmansa da'yake da shi
Bai sake furta: komai ba, sai dai kallo daya za
kayi masa kasan yana cikin ,bacin rai da zafin
zuciya.
Ganin haka yasa‘ “Ibrahim . ya soma lallashinsa
amma bai kulashi ba.. '
" Haka su Nura k0 kallo ba su ishe shi ba.
Haka .suka haqura suka Kyaleshi, har suka isa
Gida, 'ya fita ya nufi Dakinsa k0 Marfin Motar
bairufe ba.
Ibrahim ya bi shi da. Ido yana tunanin ta ina zai
shawo kansa.‘ Fatansa dai kar ya yiwa sister
Waya ya daga mata hankali
*.*i ’,*.*. _*.* -
_ DEEDATA ISA gida Itama rai bace Inna mai fura
tace Deeda lafiya! Magana fa nake kinaji , meya
faru na ganki haka, na ga kwanon furan a Bace?"
' "Inna don Allah ni ki kyaleni". Tayi Tsaki. “
' "Daman haka 'yan BIRNIN su ke wulakanta
Talaka k0 mara karfi shi ne wayewa?"
' "Ke Deeda ba dai fada ki ka yi. da 'wadanda
suka fi qarfinki ba k0? ' ,Kin ga fa nan Birni ne ki
rufa mana asiri kar ki musu halin da ki ke mana a
Kauye muna lallaba rayuwannu ki jawo mam
masifa. ‘ ‘ Ni kam ki fito ki kai min daya
Furan..." , "Ni fa Inna ki kyalemi, bazan."Iya
daukan wani furaba"
Garam!! “Ta. ,_,rufe ,Kofa- —ta bar Inna da
budadden Baki tana mamakin al’amarin Deeda. :-
" "Tomeya faru kumahaka?” ‘ Ta sungumi
Kwanon Furan ta fita. , ‘ A can ta ji ‘labarin abin
da ya faru. Nan ta godewa Allah ,daba
wanda'yanuna 'Gidan da» Deeda ta ke da sun
shiga wani tashin hankalin.
“ KARFE SHA BIYUN DARE
amma Sabeer‘ya‘kasa nutsuwa, k0 Abinci a:
wannari yammacin har zuwa dare bai iya ciba,
tsabar tafasar zuCiya, sai ka ce wanda akai masa
wani mummunan illa. K0da yake abin da bai saba
ba kuma baizataba. " duk lokacin da ya tuna
furkar deeda sai Ranshi ya Baci, yayi Tsaki
Banza»Mummuna Yar kauye Yar gidan matsiyata
Abin da yake’fadi kenan a harshen Turanci.Abin
da ya f1 kona masa‘zuciya shi ne, Mace ‘ce ta
ma‘sa wannan wulaqancin, waccé ba koman-
komai ba. '
"Shin Ina zai ganta ya rama wulaqancin datai
masa?" : ‘ ’
"Shin inya gantama ta'ya ya zai some rama
wannan wulaqancin datai masa?”
Lokaci guda Sabeer ya ji burinsa shi ne neman
yarinyar nan da 'kuma_ rama wulakancin da tai
masa wanda ya kasa samun irin wulakancin da
zai ma ta ya qona mata zuciya, Wanda ba zata
taba mantawa da shi ba har qarshen rayuwarta
Ibrahim yana hangosa ’yana ta. kaiwa da
komowa da alama har yanzu bai huce ba, abin na
damunsa. ‘
yayi qoqarin lallashinsa yaci abinci koda kadanne
amma ina wannan dare. Abincin
ma daci yake yiwa sabeer. Da kyar ya sha rabin
Kofin juice
' " Ibrahim tare ya kwana da‘ shi, ‘kowanne
juyi yayi sai yaga Sabeer na zaune ido biyu. ‘
‘ Shi dai tun da .ya ke bai taBa ganin abin da ya
hana Sabeer Barciba a rayuwarsa sai yau. K0
Jarrabawa bai taBa hanasa bacci
' Haka baitaba ganin Sabeer yadauki wani abu da
muhimmanci haka ba. A wannan dare ya kira
Farida. '
Ta dauka a gigice. ‘
‘Lafiya‘ Kanina, Waya yanzun nan?" 7‘
yi haquri Yayata
"Kanina ai ni ba ni da, matsala a kowanne: lokaci
zaka iya kirana damuwata. dai shi ne naga dare.
ne_,yanxu a naija lokacin da kowa ke baCci, dole
inji tsoron ,~ ganin Wayarka a wannan
lokaciHaka ne Yayata, kasa haquri nayi gari ya
waye, na ‘ga ,abin da ban taba ‘gani ba a tare da.
‘sabeer daga ni har ke har Daddy 'abin 'da mu ke
so mu gani a tare da shi kenan.“ -
"Kanina fada min mene ne don Allah?" "
Ta fada cikin zumudi da dokin sonjin mene ne
"Yayata‘ yau lokaci‘ na farko da naga Sabee‘r .ya
zama (Serious) akan abu, ya dauki wani abu da=
muhimmanci da gaske har ma ya kasa bacci‘
yana ta (Planing) ta‘ yadda zai bullowa'
al'amarin, 'yana ta ‘ Kullawa da kwancewa. Kin
tuna Yayata ko Jarrabawa‘ k0 Ciwo ba ya hana
Sabeer Bacci?"
Haka ne Kanina. Amma na ji dadi ba ka ji wani
farinciki ‘da ya mamaye niba. Akan (Business) ne
ko Asibiti?"
Ibrahim ya dan yi shiru sannan yace "Karki damu
zan fada miki in kin zo k0 ma akan mene ne dai
shi ne yadda ya zama (Seriou) ya bada
muhimmanci akan abin
"Haka _ne qanina, ina mana addu'a‘ Allah Ya
mana jagora, ya kawo sanadin kimtsuwar
Sabeer".
"Haka ne Yayata, da alama Allah Ya kawo sanadi.
Ke dai ki ci gaba da addu'a da fatan samun
nasara ga abin da na yi niyyah
"Zan ci gaba da addu'a qanina, Allah Ya
taimaka". .
"Amin". Ya amsa.
Bayan tambayarta lafiyarta ’ :da wasu al'amura
suka yi sallama.
Ya dawo ya samu har yanzu Sabeer na kaiwa da
kawowa. -
Ya isa gareshi ya jawo hannunsa ya ce "Sabeer
20 ka kwanta dare ya yi".
Ya Bata fuska. _ , ‘
"Uncle IB ya ,zan yi in iya bacci?" ‘ '
Idonsa ya kada.
"Ka ga wulaqancin da yarinyar nan ta min.
Please'Uncle IB ka taimaka min in nemo ta, ka
san ni yanZu k0 Unguwar ba zan iya sake
ganewa ba".
"Zan taimaka maka. Ina dai yarinyar ka
ke son sake gani?" ’
"Sosai don, ba zan iya kyaleta ba", ‘
"To kar ka damu za ta 20 har inda ka ke ta
sameka..amma dai yanzu ka kwanta gobe muna
da fita Asibiti". ’
Da kyar ya lallaBashi ya kwanta ya dinga juye-
juye ya kasa baccin har sai dab da Asuba - Bacci
ya sace shi. ~
Juyin duniya kuwa Ibrahim ya yi Sabeer ya tashi
su je Sallah amma yaqi, haka ya hakura dole ya
barshi.
Bai tashi ba sai wurin sha biyun rana. Nan ma sai
da Ibrahim ya je Asibiti ya dawo ya tashesa suka
fita tare.
*.* *.* *9*
tun qarfe shida na safe deeda da lnna mai Fura
ke layin ganin Likita, duk kuwa sammakonsu bai
sa sun ga Likita da, wuri ba Saboda wani Tiyata
na gaggawa da ya Shiga, sai da ya fito sannan
ya soma ganin marasa lafiya
Deeda ta bata fuska cikin Kosawa ta ce, "Dama ai
duk abin da aka ce ma kyauta ne sai. ka ga
wulaqanci. . ,
Ni dama tunda na ji Tabawa ta ce mu zo wannan
Asibitin kyauta ake ganin marasa lafiya na san za
a wahala.
Aik0 Asibitin gwamnati ana dai siyan Kati..."
"Wai me ya sa kin fiye gajen hakurine?" Kakarta
ta fada a hasale. .
' "Ke da ki ke neman lafiya k0 ma kwana za ki yi
ai sai ki hakura ki jira su ba mutane ba ne? Haba
kin fiye mitan tsiya.
Duba Asibitin nan da kyau kin san ya sha
karfinmu ba don alfarma muka samu ba"
' ‘ Deeda ta yi tsit! don ba ta son musu k0 wani
sa'insa da Kakarta.
Nan ta canja maganar da cewa, "Inna duba
hannuna fa ya wartsake, jikina ya mike ba kamar
da ba, sai ina ganin kamar yanzu ba ni da
bukatar ganin Likita".
"Kina da buKata". Kakar ta katseta.
"Ki ka san ko ya sake dawowa? Ai gara ki yiwa
Likita bayani in da Magani a ba ki da zai hanashi
dawowa.
Kama ma ai ba duka jikinki ne ya wartsake ba,
har yanzu ta ciki, ta wani wurin akwai inda ya ke
yamutse". . ' ‘
"Shima a hankali ai zan washe kamar sauran
"Ki min shiru tunda har munyi haqurin jira har
wannan lokaci kuma mun20 to ba'abin da zaisa
mu koma...” 7
Kafin Inna ta rufe Baki wacce ta shiga din ta fito
ta ce Deeda ta shiga. Ba ta Bata lokaci ba ta
kutsa kai ya yin da Inna ke jiranta a waje.
Zaune ya ke akan (Table) Tebur din da ke cikin
OfIice din, da alama shi ne Table din Likita.
SABEER NE! !!
Hannunsa riqe da Game yana ta bugawa, gefensa
kuma Fruts ne da Juice yana ci yana Game
hankalinsa kwance. Hakan ba karamin nishadi ya
ke sa shi ba.
Deeda ta turo. Kofar ta shigo tare da
sallama. '
K0 daga kai bai yi ba daga Game din da ya ke ba
balle ya amsa ma ta sallamar
Nan ta je ta tSaya a gefe gami da cewa, "Ina
wuni Likita?"
Har yanzu bai dago kai ba sai dai ya amsa mata
da cewa, "Likita na (Washing room) Bayi, ki jira
ya fito
Nan ya ci gaba da game dinsa. Ita k0 _taja
kujera ta zauna tana kallon yadda’ ya bawa
game"‘ din muhimmanci. ‘ ’ "Lallai wannan bai da
matsala a rayuwa "ta fada a ranta. ‘ ' Sai ihu
yake yana dariya shi daya yana buga game yana
morewa abinsa. 'Mutum babba dashi qaton
Saurayi kamar Wannan' yana abin Yara Kai Allah
Ya 3“ kyauta. - ‘ - T 0 ma wai shi ba Likita bane
me ya keyi a nan?
Wai a gabansa zan ga likitan? KO shima Likitan
ya 20 gani? Bari dai in tambayesa'
Ta mai da hankalinta gareshi ta ce, "Mallam
kaima Likitan za ka gani ko in fita sai ka gansa
in shigo?"
Har yanzun bai kulata ba. Haushinsa ya kamata.
Ta ce, "Wai kai ba ka jin kunya Kato da kai kana
abin Yara?" '
Nan da nan ko Sabeer ya fusata, ya dago kai
.gami da juyowa da sauri don ci. mata mutumci. ‘
Carab k0 suka yi ido biyu da juna. Ya mike tsaye
cikin mamaki kuma a fusace, itama ta mike, ta
lura da haushinta da ya ji amma ita ba ta ' ma
gane shi ba. .
"Na lura yarinyar. nan ba ki da kunya, ba ki da
mutunci! Uban wa ya kawo ki Asibitin nan?"
Ta kalleshi sama da kasa ta buga mai Tsaki tare
da Harara ta ce, "Sa'a ka yi ban iya
Zagi ba da na ma ka wadanda ya fi naka ciwo.
Kuma karka'yarda ka sake zan min Uba".
Sai an Zaga me ki ka isa ki yi? Dama nemanki na
ke, yau sai na miki rashin mutuncin da ba za ki
manta da shi ba".
"Banyi tsammani ba".
‘ Ta ba shi amsa kai tsaye.
"’Me kike nufi?"
Ta kada mai Idanunta wanda sai da ya sa yaji
gabansa ya fadi. '
Wannan ne lokaci na farko da bama Mace ba,
lokaci na farko da aka taBa kallonsa ido cikin ido
ba tare da shakka k0 tsoro ba.
nace, "Ban tsammanin zaka iya ba. Ina nufin
yanayinka da alamunka bana zaton ka Iya rashin
mutunci , sabo da a yadda na ga alamarka girman
jiki ne kawai kayi, amma har yanzu tunaninka da
ayyukanka har kwakwalwarka ta yara ce ba su
girma ba.
Yaro k0 ban tsammanin ya san meye rashin
mutunci balle ya iya, sunansa kawai ka sani, don
haka ka bari in Kwakwalwarka da tunaninka
sun gama girma sai Ka zo mu kara rashin
mutunci, in ka gwada min na 'YAN BIRNI ni .kuma
sai in gwada ma ka na 'YAN KAUYE":
Tuni Sabeer ya kara harzuka, idonsa ya kada ya
yi ja ya kasa furta ma ta komai, kuma ya kasa
ma ta komai, sai azabar zuciya kamar za ta
kashe shi. .
Tun-tuni Ibrahim ya ji hayaniyarsu ya fifo ya
tsaya a kofar ya -harde hannu yana kallonsu
yana murmushi. . -’
Cikin qunar zuciya Sabeer ya Ce ma ta, "Fita
Asibitin nan tun da ba na Ubanki ba ne, ba zakiga
Likitan ba, kuma yau sai na nuna miki halin yarint
Ya- zaro- Belt dinsa da karfin tsiya ya kai ma ta
duka, ta yi saurin sa hannu kuwa ta tisge.
Mamakinta ya‘sa shi bude Baki.
_ "Bi a hankali Yaro kar (Body bulding) din da
kayi ya yaudareka; kar ka ganni Mace ka raina
min Wayo daga Kauye na ke, na ci Tuwon Dusa
na ci na Dawa, kar ka nemi raina ni.
Kuma da na san Asibitin nan na Mahaifinka ne da
ban soma takoshi ba."
Ta ja mai dogon Tsaki ta juya za ta fita, wani
kololon Bakinciki ya. tokare masa zuciya, ya rasa
me zai ma ta.
Ba ta ankara ba ko ta taka Sunul ta fadi qasa ta
daku. . -
"Wash Allah". Ta fada
"Wayyo! Bayana".
Sabeer ya Kyalkyale da. dariyar mugunta
yace,"Su Budurwar Kauye masu karfi an sha
Kasa".
Ya matsa dab da ita yasa kafa ya' takéta .sai da
tayi Kara yace"Duk karfin Budurwar Kauye ba ta
isa ta kai Namiji ba, musamman na Birni, BIRNIN
ma na GAYU Ya Kara taketa da Karfinshi ya ce,
"Dama neman‘ki na ke tun rashin mutuncin da ki
ka min ban manta ba, kin hanani sukuni kin
hanani
Bacci' kin hanani cin Abinci, kin sani yawan
tunanin wannan mummunar fuskar taki, har ta
zauna a kwakwalwata.
Yau wannan hannun da ya watsa min Nono sai
na Balleshi".
Nan ya kai daya Kafar ya danne Yatsun da qarfi"
‘
Ta sa ihun Azaba, sai da hannun yayi jini sabo da
irin takalman da yasa ba na wasa ba ne.
"Wayyo Inna zai kasheni
Ibrahim ne ya matso wurin da sauri ya janyesa.
"Kai- Sabeer ba ka da hankali za ka kashe- 'yar
mutane?"
"Kyaleni in ma ta illa, gobe idan ta. ganni za ta
canja hanya. Kuma wannan kadan ma ta gani." ‘
Ibrahim ne ya taimaka ma ta ta tashi gami da
dressing din hannun cikin . gaggawa ya samu
jinin ya tsaya, amma bai yi nasarar tsayar da
jinin ba.
Hankalinsa ya tashi, gaba daya ya rude, bai taBa
tsammanin abin nasu zai yi tsanani haka ba da
bai bari hakan ya faru ba. '
Nan ya sa hannun cikin qankara ya sa ma ta
Magani sannan ya daure da Bandeji ya nufi ciki
don dauko Allura ya mata.
Bayan fitarsa Sabeer ya harareta ya ce, "Kalli
'yanda ki ka zama abin tausayi...azaba kadai ta
canjaki."
"Allah Ya isa Ta fada cikin zafin zuciya.
- "Kuma kai ne abin tausayi ba ni ba, don ni kam
ban iya bin 'yan fage in yiwa mutum illa ba sai
‘dai in fuskance "shi. Ka ji kunya da ka nuna
qarlinka akan Mace".
Ta ja Tsaki gami da matsawa dab da shi, bai
ankara ba ta ja farar Rigarsa ta goge Jinin da ke
zuba a hannunta gaba daya ta bata masa Rigar. '
‘
Ya daga hannu zai Mareta, tuni ‘ta manta ciwon
da ke hannunta ta cafke Hannun ta gantsara
masa Cizo ta fita da gudu. " i
. Inna dai ba ta ankara ba sai ganin Deeda tayi ta
fito da gudu a rude ta bita. "Ke Deeda!!!”. ' Can
kuma sai ga Sabeer ya biyota da gudunsa. ‘ ‘
Inna fa hankalinta ya tashi, ta bisu tana,"Deeda!
Deeda!! Deeda! ! !" Daga qarshe dai ta gaji ta
hakura don ba‘ za ta iya gudunsu ba. ‘ - Sai da
suka yi nisa sosai har suka fita Asibitin sannan
Sabeer ya yi nasarar kamata ‘ Ba ta saurara
masa ba' ta yi na ‘maza turesa da qarfinta. ' Sai
da ya fada cikin wani ruwan dake a bakin hanya.
. Tana' ganin ya' kai qasa kuwa ta arta ana Kare,
ba ta tsaya k0 ina'ba sai da ta kai Gida, ta nufi
daki ta rufe tana haki gami da tuno abin da ya
faru kamar a wani Mafarki k0 Almara. . lnna dai
hankalinta a tashe ta nemi abin hawa ta kOma
bayan ta gama neman Deeda ba ta
ganta ba, ta tafi tana addu'ar Allah Yasa ta koma
Gida.
Sabeer ya mike cikin takaici da bakin ciki da
Bacin rai, duk’ Kunya ta kamashi da ya ga Yara
da wasu Mutane suna kallonsa.
Wasu 'yan Mata kuwa har dariya suke suna mai
da‘ yadda abin ya faru, da alama a idonsu aka yi.
Da kyar ya iya daga kafa ya miqe ya wuce kai
sunkuye takaici da kunya sun lulluBesa, ya rasa
ma ina za shi.
Shi 'dai bai gane hanyoyin ba, don haka dolensa
ya koma cikin Asibitin, ga‘ shi 'ba Waya a
hannunsa, haka' dolensa ya sunkuyar da kai yana
Boye fuska ya koma cikin Asibitin yana kaucewa
jama'a yana kulla tsiyar da zai ma ta Ibrahim
yana ganinsa ya fashe da dariya
ya ja shi wani Office da ba kowa ya ce, "Sabeer
kai ne haka k0 Ido na ne?"
Cikin zafin rai ya ce, "Wannan Aljanar Yarinyar in
na kamata k0 sai na harbe yar banza! Ni zata
yiwa haka?"
"Ya isa haka Sabeer. Yanzu dai abin da ya faru
ya faru ba yadda ka iya, ka koma Gida ka canja
Kaya ka barni in yi aiki Please tun da na san yau
ma kai kam ka tashi'ba za kuma kayi aikin ba"
Ya Bata fuska.
"Uncle IB ka san ni ban gama sanin hanyoyin
garinnanba, Please ka 20 ka mai da ni
Ibrahim ya cira kai ya kallesa ya ce, "'Ka yi
hakuri Sabeer ba zan iya barin aikina in yi naka
ba, yanzu mafa marasa lafiya na dakatar ina
sauraronka.
Please har yaushe komai sai an maka kai ba Yaro
karami bane, in ba zaka iya komawa ba zan ma
(Diver) din Office magana ya mayar da kai Gida,
amma ni dai ba zan bar aikina ba".
Sabeer ya yi fishi ya fisge Key din Motar ya fita,
Ibrahim ya bisa da kallo sannan yaci
gaba da Aikinsa da niyyar in ya gama’zai je inda
suka hadu da yarinyar nan ya nemi Gidan su.
%%%%%%%%%%
Sabeer kuwa, sai da ya gama zagaye_ kafin ya
kai ga gane hanyar Gida, ga shi ba dama ya kira
Abokansa za su masa dariya.
Haka ya yi ta shan wahala kafin ya isa Gida ya
koma ya samu Momi ta dawo, wato Hajiya
Amina, sai dai bai bi ta inda ta ke ba ya wuce ya
cire kaya ya shiga Wanka. .
Ya jima kwance cikin Ruwa a (Bat Tap) yana
tunanin irin abin da zai ma yarinyar nan da inda
zai sake ganinta, sai dai hakan ya gagara,
tunaninsa bai samu maganin matsalarsa ba.
Nan tunani ya fado masa, kawai ya kira
Abokansa don su tayashi nemanta da kuma ba
shi shawarar irin rashin mutuncin da zasu ma ta.
Bayan ya fito ya ji kiran (Door Bell) na
Bangarensa, bai kula ba sai da ya sa Kaya ganin
an matsa ya fita ya bude.
Momi ce tsaye tace, "Lafiya Saber tun dazu ina
tsaye, ina ka shiga?" ’ ' Ya dan sunkuyar da kai
yace, "Momi ina Wanka ne Shigo mana,'dama ina
shirin inna fita zanje in gaishe ki. Kin dawo laflya
k0?" : "Lafiya kalau". Ta amsa masa lokacin da
ta ke zama ta ce, "Yayunka duk suna gaisheka.‘ .
- ' ' Daddynku ya fada min komai' game da_
dawowarka, sai ka dage ka koyi 'Aiki, in da hali
ma harka Karo ilimi a fannin da kafiso, duk da
Asibitin muna da Likitoci, amma akwai bukatar ka
a Asibitin. _. Ina so ka daukeni kamar
Mahaifiyarka, duk abin da ya shige ma duhu ka
20 ka sameni Bangarena na Shawara k0 wani
abu. _ Sannan ina fatan ba ka da matsala da
Ma'aikata masu kula da Bangarenka da Abincinka
suna gyara ma ka Side dinka ya kamata, yadda
kuma ka ke so?, duk abincin'da ke bukata order
kawai za ka yi..."
"Na sani Momi ba sai kin bata bakinkiba Ya
katseta. "Nan Gidanmu ne Gidan Ubana ba sai an
bani ko ance in tambaya ba. . Sannan Sister ita
ce Mamana ita ce komai na, kar ki yi qokarin
zama Mamana ki zauna a matsayin .Matar
Babana ina ga hakan zaifi mana ni dake Sannan
Uncle IB yana tare da ni, duk - bukatata shi kadai
ya isa ba sai kin sa Baki ba‘ In koyi aiki k0 kar
in. koya, wannan ba matsalarki bane Batayi
mamakin halinsa ba, ta yi wani murmushi irin ta
manyan Mata da idonsu ya bude tace To shi ke
nan tunda haka ka ke so, muje a haka-tun da kafi
son in, rikeka a matsayin dan ‘Mijina‘ Fine, ni
kam na kware wajen iya,rike ‘dangantaka tunda
rikon dan kishiya kakeson nai maka ina
maraba'da hakan. inaso ka ,sani bani da matsaia
da kai, bazan cutar da kai,ba amma fa kar ka
shiga gonata kayi kokarin tsayawa a matsayinka".
"Kema ina son ki tsaya a iyakarki".
"Da kyau".
Ta fada tare da girgiza kai ta fita. Ya bita da
wani matsiyacin kallo gami da rufe gofar Falon ya
koma ciki. ,
Wani radadi yaji ya ziyarci" hannunsa, nan ya mai
da kallonsa kan hannun, ya yi jawur har ya soma
kumbura. '
Ya ja dogon Tsaki, haushin Deeda da tsanarta ya
Kara shigarsa, don gurin da ta gantsara masa
Cizo ne.
"Amma wannan akwai 'yar rainin wayo...ni 2a ta
fadawa bafar magana? Me take nufi da na girma
amma hAlayena ba su girma ba?
Tana nufin ni yaro ne
Nan ya mike yana kallon kansa a Madubi tun
daga sama har Kasa, duk ta yamutsashi
kwana biyu kawai.
banzar yarinya yar KAU YE mummunar yarinya za
ta sani a gaba... zan mata rashin mutunci To
amma me zan ma ta?”
Waya ya dauko ya bugawa Abokansa yana musu
neman gaggawa.
Cikin minti talatin suka hallara.
"Lafiya Sabeer irin wannan neman gaggawa?"
"Ba lafiya ba
Ya fada a qule.
"Wata Aljanar Yarinya ce ta sani a gaba, ta daga
min hankali",
Salim ya kalli Nura sannan ya kalli Nura sannan
ya kalli Sabeer din ya ce, "Ba dai mutuniyarka da
ta watsa ma No... ."
Wani mugun kallo da ya masa ya sa shi gum da
Bakinsa bai Karasa ba.
Ya ce, "Na ganota".
Sabeer din ya ce,"Shawara na ke so ku bani.
wane rashin mutunci zan ma ta?"
Nura ya ce, "Me zai hana ka yiwa banza lahani,
wato ka banke banza da Mata sai 'ta Karye ta
dawo me Kafa daya?" ,
Saber ya girgiza kai.
"Not Bad Kai kuma ,fa Salim, me ka ke gani?"
Salim yace, "Hakan da ya fada dai-dai "ne" k0 ka
kadeta ko ka yi hayan wasu su saceta ta, Bace
Bat na kwana biyu a rufeta inda k0 Hannunta ba
za ta gani ba don Duhu, ta Yini kwana da
Yunwa.." ' .
Sabeer ya ce, "1 Hope shawaranku ya yi aiki,
Nura ya ce, "In dai har muka yi yadda na ce dole
ya taBata. In ta zama Gurguwa ai ta .nakasa".
Sabeer yace "Ba wannan ba, samun inda take ma
bala'i ne". "Zamu nemota a same aren da muka
hadu da ita
zamu nemota, zan mata ,abin da ba za,,,,'yan
Samari". Muryar Ibrahim ne
suka mai da hankalinsu garcshi. 'yana wannan
murmushin nasa ya ce '-'.da;abin da zaku yi a
rayuwa kuke ku ke planing tsarawa da yafi
muku".
ya yi dariya gami da fadawa jikin unless ib yace
kaida Sister ’kune rayuwata (My whole world) ya
yi, murmushi ya ce kadai fadi, amma ba Uncle IB
bane zai zauna ma. da Mata 'yar KAUYE ba. Ka
tuna
ya fada tare da murmushi ya Bata fuska.
Ya ce, "Uncle IB karka Bata min rai, kasan na
tsani 'yar Kauyen nan da aure amma nafi tsanar
yarinyar nan (I hate her the most)". .
Ibrahim ya ce, "Ni zan fita dama na leko dubaka
ne zan fita ni ina da abinyi bani ’da' lokacin
tsanar wasu k0 daukan fansa, in kuma ba'ka bar
maganar ba sai na fadawa Sister". '
Ya langaBe kai. "
’Yace Uncle IB kar ka min haka mana".
"Na dai fada ma ka ka zaba daukar fansa
.ko Bacin ran Sisiter".
Nan ya fice ya barshi. Ya maida kallonsa kanSu
Salim ya ce,‘ "Guy plan cancel"
Nura ya ce, "Wai kana nufin kana tsoron Uncle IB
da Yayarka?"
Sabeer ya ce, "Sabeer bai tsoron kowa, bai kuma
shakkar kowa just that ina son Sister da Uncle IB
(and 1' respect them a lot) ban san Batawa Sister
rai, kuma sabo da wannan Aljanar ba zan 'Batawa
Sister rai ba, sai dai duk randa na hadu da ita sai
na ma ta illa fiye da wanda ta min".
Yana magana yana kallon inda ta dankara masa
Cizo.
£££££££££££££
da tambaya da bincike a Unguwar, Ibrahim ya
gano Gidan Tabawa inda‘
Deeda ke zaune. Tana daki k0 tana shirya kaya
ranta a Bace
sabo da washe gari za ta tafi Gidan Aikinta.
Yaro ya shigo. "Wai .ana sallama da budurwar da
ke
Gidan nan".
' Inna mai F ura ta kallo Yaron.
",Waye ne
"Wani me Mota ne". Yaronn ya bata amsa a
takaice.
"Jirani". ' ‘
Nan ta shiga ciki ta dauki Hijabi 'tabi bayan
Yaron.
"Mu je
Yana zaune cikin Motarsa a Kofar Gidan ya
hango Yaro da Inna. Mamaki ya kamashi. Ya yi
saurin fitowa daga Motar lokacin da suke isowa.
Innan ta kalleshi kallon tambaya. Kallon da take
masa ya sa ya sha jinin Jikinsa. Tabbas ko k0 ba
a fada masa ba ya san ko Uwarta ko Kakarta ce.
Ya kalli Inna da kyau, ya ga irin shigar: da tayi ' ’
A ransa ya ce "Lallai wannan yarinya ta san inda
ta yi gado..." . Inna ta katse mai tunani ta ce,
"Gani; naji an ce kana sallama da Budurwar
Gidan". . Ibrahim ya kalleta da kyau ya rasa ma
me zaice mata. ‘ Tsayuwar da ta yi ta riqe
kugunta yasa yaso tuntsurewa da dariya amma
sai dake yace "Budurwa' na'ce ba tsohuwa ba
Ta kallesa da kyau ta ‘ce, "A Gidan nice budurwa
k0 kana musu ne? Me ya kawoka, me ka ke?
nema?" '
ta tsareshi da ido. Gaba daya ma ya rude ya rasa
me zai ce ma ta.
yanata.soshe-soshe da kame-kame, can dai ta
tausaya masa tace, "jikata ka ke nema me za kai
mata ya sauke numfashi ya ce, "‘Dama ta je
Asibiti ganin Likita ne to sai suka samu saBani
da kanina ta taf1 ba ta ga Likitanba na 20 in ba
ta ha'Kuri kuma in ji meye matsalar don ni Likita
ne". ‘
ta zaro Ido ta washe Baki. "Aiban sani ba.
‘ wannan ciki za ka shigo. Dama haka Likitocin-
suke na birni har Gida suke biyi marar lafiya?
Ikon Allah, ai Deedan tana Ciki shigo
‘ har ciki. A tsakar gida ta shimfida masa
Tabarma sannan ta shiga Ciki‘ ta kamo hannun
Deeda.
ke fito ga Likita har Gida ya 20 duba ki". ‘
Deeda ta kalleta cikin mamaki.
"Likita?"
"EH". Ta amsa ma ta a takaice.
"Ashe da rabon za ki ga Likita kafin ki tafi Zo mu
je". ' ' Ta ja'ta har Tsakar Gida wurinsa.
"Likita ga Jikar tawa”.
Deeda ta kallesa cikin mamaki.
"Likita har Gida?"
Ta ja Kujeran- zama na tsakar Gida ta zauna, ya
yin da Innar ta zauna a gefensa.
Deeda ta gaisheshi Sannan ta tambaya.
"Anya ni kuwa ka zo nema? K0 ka Bata ne?"
"A'a ke na 20 nema. Sunana Dr. Ibrahim, ni ne
Likitan da ki ka zo gani da safe ku ka samu
saBani da Kanina".
' Ta girgiza kai.
"0h!" Gami da dan yamutsa fuska.
"Wannan qanin na ka?"
Ya yi murmushi gami da cewa, "Ina ji dai kuna da
(Allergy) da juna, duk lokacin da aka ambaceki
sai launin fuskarsa ta canja, ‘kema haka tun
randa ku ka' hadu jininku bai zo daya
Na 20 in ga hannunki ne in ba ki haquri sannan in
ji me ye matsalarki
Kallonshi ta ke tana murmushi. A ranta ta ce,
"Akwai bambanci tsakaninsa da qaninsa.
Shi mutum .ne mai sanyin hali da kirki. Haduwar
farko na gane hakan.
Shi ko wancan haduwar farko na gane halinsa
'mara kyau.
'Jin tayi shiru ba ta amsa ba Inna ta yi carab Ta
amsa.
"Likita hannunta dai da sauqi, mu Mutan Kauye
ne muna da. dabara da namu Magun'gunan irin
wannan CiWon. -
Zan dai' yi ma ka bayanin babbar matsalar duk
da yanzu taji sauki ciwon da kansa ya baje".
Nan ta soma zayyana masa ciwon Deeda tun
tana karama har zuwa girmanta da shigowar su
Birni ya soma bajewa da kansa a hankali.
Ya dan yi shiru na tsawon lokaci 'yana kallon
Hannayenta.
Ya so ya fuskanci matsalar sai dai duk da hakan
sai ya yi bincike.
Ya ce, "Na fahimta Kaka, sai dai duk da hakan
tana buqatar zuwa Asibiti sabo da a can ne zamu
yi duk wasu gwaje—gwaje don gane ainahin
ciwon, duk da dai yanzu ya washe ba matsala,
amma 'gaba zai iya dawowa, duk da ban
tabbatar da wane ciwo bane, amma dai ba abun
damuwa bane, in ma ta sha Magani to da yardar
Allah za ta rabu da shi.
Don haka gobe in Allah Ya kaimu ta sameni a
Asibiti karfe goma."
murna ta lulluBeta. ,
:Na gode Likita."
Mun gode, duk da goben zata tafi amma" zata
ganka. kafin ta tafi".
Ya mike yana fadin allah ya kaimu goben, Inna
tana ta godiya, deeds kuws kallonSa take tana
mamakin’ kirki iron nasa
“ya mike ya kalleta ya ce, 'miss Deeda inga
hannun naki?" .ta-‘ sunkuyar dakai ta mika masa
hannun ya kalla ba tare da ya taBata ba ya ce,
"Kina da jiki 'mai kyau don bai kumbura ba, in dai
yana miki radadi ki sha (Pain Reliver)
Paracetamol da
,to"Na gode"
Nan ya yi sallama da su ya wuce.
Deeda ta bishi da kallo ya yin da Inna ta rakashi
har iofa. Ta dawo ta samu Deeda zaune ta yi-
Tagumi. '
tace, "Deeda kina tunanin tafiya ne? Karki damu
Allah na tare da ke ina tare da ke
idan kin‘ ga ana saki abin da ba dai- daiba ko ba
kya so zan dauko ki mu dawo ". Ta“ dan yi
murmushi ta ce, "Inna haka ne, ina tunanin tafiya
sai dai na‘ fi tunanin barin karatuna duk da na
koyi abu da yawa na iya abubuwa da yawa
karatu da rubutu, turanci da ma abu da yawa.
Haka na samu ilimin Addini‘ sosai a Makarantar
wanda da ban san su ba..
- Alhamdu lillahi da zaman da na yi a {Gidan
Tabawa da gatan da ta min, sai dai ilimi ba ya
qarewa, yanzu na soma dandanarshi zan so in ci
~gaba'da samunsa.
Sai dai ilimi ana samunsa ta kowacce fuska,
duniyar ~gaba dayanta Makaranta ce, kamar
yadda na koyi wani abu yanzu na fahimta, akwai
mutanen kirki akwai na tsiya.
Inna duba bambanci tsakanin wannan Likitan da
qaninsa.
Mutum mai nutsuwa mai kirki mai mutunci.
Kaninsa kuwa..." ‘
Ta ja dogon numfashi. "Bana son ma tunashi
balle maganarsa.
Inna kar ki damu ina maraba da sabuwar rayuwar
da zan shiga, a wurina wani sabon Makaranta ne
na koyon wani sabon i‘limin
rayuwa. Idan Allah Ya kaimu gobe zan je Asibitin
zan roqi Tabawa mubiya tacan» sai mu wuce.
Insha Allahu akwai‘haske a tattare data tafiyar da
zan yi". ' .Inna ta yi 'murmushi. ‘ :"Na ji dadi
Deeda yadda ki ka kwantar da hankalinki ba ki
daga hankalinki akan tafiyar ba. Allah Ya taimaka
ya sa alheri. Muna gari daya, zan dinga zuwa
dubaki, za ki dinga zuwa kema in kin samu
dama". Haka suka kusan kwana- suna hira gami
da tsara yadda tafiyar za ta kasance. . Innan ta
ci gaba da yi ma ta nasiha da bata shawara akan
zaman rayuwa da kuma sababbin
mutanen da za ta tarar ta yi mu'amala da su.
ya kuke ganin zaman deeda DA saber zai kasance
a birnin gayu anyama zasu hadu kuwa?
h shared a profile .
birnin gayu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter1
- 2 chapter donjin ci gaba
- 3 chapter2
- 4 chapter3
- 5 chapter4
- 6 chapter5
- 7 chapter6
- 8 chapter7
- 9 chapter
- 10 chapter8
- 11 chapter9
- 12 chapter10
- 13 chapter11
- 14 chapter12
- 15 chapter13
- 16 chapter14
- 17 chapter15
- 18 chapter16
- 19 chapter17
- 20 chapter18
- 21 chapter19
- 22 chapter20
- 23 chapter21
- 24 chapter. 22
- 25 chapter23⇩
- 26 chapter☜(⌒24⌒)☞
- 27 chapter 25
- 28 chapter26
- 29 chapter27
- 30 chapter28.
- 31 chapter last 29